Mutuwata (Gajeren labari)


   
 
Daga Musaddam Idriss Musa

Na gama fidda rai da tsammani ga samun rabo, na kuma sallamar cewa ba na daga jerin mutanen da zasu yi gamo da katari na samun dace. Ban san ya ake yi ko kuma ya al'amarin yake faruwa ba illa dai kawai a karshe na kan tsinci kaina tsamo-tsamo a hali na aikata laifi ko alfasha.

Kawo yanzu da na ba wa shekaru tamanin baya, ni Baba Adamu ban san yawan laifukan da na aikata ba daga zamanin da nake tashen samarta zuwa yanzu da nake kwance bisa gado na jinyar ajali bayan da komai da na mallaka ya kare a wajen neman maganin cututtukan da suka yi sanadin kwanciyata har na kasance a cikin wannan hali na jinya tun daga kan cutar dajin da na hadu da ita a dalilin yawan shan sigari, hawan jini bisa rasa dukiyata, cuta mai karya garkuwar jiki da na kwaso a yawon sharholiyata da karuwai, ga ciwon koda da yoyon fitsari ban da ciwon siga da shi ma likitoci su kace ina dauke da shi.

Ina cikin wannan hali ne kwatsam sai ga Malam Muhammadu liman ya shigo duba lafiyata shi ne kuma kadai ya waiwaye ni tun bayan da na kwanta wannan jinya. Ya kuwa tarar da ni ina ta sharbar kuka.

"Ka kwantar da hankalinka Baba Adamu, ita cuta ai ba mutuwa ba ce, bugu da kari duk wanda ka ga ya kwanta jinya to Allah ne yaso shi da rahama saboda ita jinya tana kankare zunuban da mutum ya aikata ne a baya" inji liman.

Baki na na motsa dakyar cikin radadin zafin jin ciwon dake ratsa ni nace, "Gafarta Malam ni da na shafe tsawon rayuwata wajen aikata manyan laifuka a Ubangiji ta ya ma zan kawowa kaina zaton samun rahama da har zan dauki wannan ciwo a irin matsayin da ka ambata...ai kawai azabata ce aka fara yi mani tun daga nan duniya".

"Sam kada ka furta haka, kuskure ne fidda rai ga samun rahamar Ubangiji. Domin kuwa Allah da kansa yana son masu tuba bisa kuskuren da suka aikata masa. Babu wani shamaki a tsakanin MUTUM DA MAHALICCINSA kamar yadda babu hijabi ga addu'ar wanda ya tuba bisa kuskurensa. Muddin ka yi nadama akan laifukanka to ka nemi yafiyar Ubangiji shi kuma zai gafarta maka".

Da wannan jawabi na Malam Muhammadu na samu karfin gwiwa a zuciyata saboda fahimtar girman alakar dake tsakanin MUTUM DA MAHALICCINSA. Istigifari na cigaba da yi tare da zuba idon ganin ta ina mutuwa za ta sauko gare ni.

Musaddam Idriss Musa
Reactions
Close Menu