Rayuwarmu A Yau Youth Awareness Association (RAYAAS)Rayuwarmu A Yau Youth Awareness Association (RAYAAS)

Motto: Domin Hadin Kai Da Cigaban Al'umma.

Kungiya ce ta sada zumunci, fadakarwa da kuma taimakon juna. Wacce ta keda rijista da hukumar yiwa kungiyoyi da kamfanoni rijista ta kasa, CAC wato (Corporate Affairs Commission). Wanda hakan ya bamu damar gudanar da aiyukanmu na taimakon jinkai, wayar da kawunan matasa da kuma tarukanmu na kungiya a fadin tarayyar kasarnan bisa doka da oda.

Muna da membobi da shugabannin kungiya a daukacin jihohin Najeriya baki daya, sannan muna gudanar da taron kasa duk shekara a daya daga cikin jihohin da shugabannin su ka zaba.

Bayan haka jihohi su na gudanar da taruka a kalla sau biyu ko sau hudu a kowane wata.

Shiyyoyi su na gudanar da tarukan kungiya duk bayan wata shida, ko sau daya a tsakiyar shekara.

Yanzu haka mun gudanar da taron kasa karo na farko a karamar hukumar Zaria ta jahar Kaduna 2018.

Mun kuma gudanar da taronmu na kasa baki daya karo na biyu a babban birnin jahar Bauchi 2019.

Kuma in sha Allahu muna kan shirin gudanar da taronmu karo na uku cikin wannan shekara ta 2020 a babban birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda mu ka fada a baya, RAYAAS kungiya ce mai zaman kanta wace bata da alaka da siyasar cikin gida ko ta waje. Sannan ba ta yanki daya ko kabila daya ba ce, RAYAAS ta 'yan Najeriya ce baki dayanmu harda makwaftan kasashe irinsu Kamaru, Chadi, Niger, da makamantansu kowa zai iya shigowa da kyakkyawar manufa ayi tafiya da shi.

Don haka bata wani yanki ba ce, ta kasa ce baki daya, kuma RAYAAS ba ta addini daya ba ce, ta kowa da kowace, sannan bata jinsi daya bace, maza da mata manya da yara, Bayarabe da inyamuri, Hausa da Fulani (BARE-BARI DA MUTANE) kowa ya shigo muna maraba da shi cikin wannan kungiya mai albarka.

Bayan haka muna gudanar da aiyukan da su ka shafi taimakon jinkai ga mabukata da marasa galihu.

Ga sunayen wasu daga cikin jihohin da mu ka gudanar da aiyukan agaji da taimakon gaggawa, kadan daga cikin su a takaice sun hada da:

Jihar Adamawa, inda mu ka kai tallafin sabulai, omo, da sauran kayan bukatu yau da kullum zuwa asibitin Specialist da ke garin Jimeta-Yola, tare da gudummuwar jini.

Jihar Gombe, mun kai ziyara gidan marayu, da kangararrun yara da kuma gidan fursuna, kuma an taimaka musu da kayan bukatun yau da kullum, sannan an fitar da masu kananan laifuka. Kuma an gudanar da aikin gaiya na gyaran lambatu da cikon wata karamar gada ta cikin anguwa da ta rushe.

Jihar Kaduna, shugabar matan kungiya ta jagoranci kai ziyara gidan marayu har sau uku domin taimaka musu da kayan masarufi, kuma ta na ci gaba da yin hakan daga lokaci zuwa lokaci.

Jihar Sokoto, mun kai ziyara asibitoci tare da taimakawa marasa lafiya da abin kaiwa bakin salati.

Jihar Zamfara, mun kai ziyara asibitocin gwamnati sannan mun taimakawa marasa lafiya, bayan haka mun gudanar da aikin tsabtace wani karamin asibitin gwamnati da ya cika da ciyawa, domin kare majinyatan da ke kwance a wajen daga kamuwa cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya.

Birnin Tarayya Abuja, mun gudanar da aikin gayya na gyaran makabarta da kuma wasu taimakon jin'kai.

A jihar Niger, ma membobinmu sun taba kai ziyara gidan marayu da taimakon mabukata.

Jahar Bauchi membobinmu sun koyar da mata da matasa sana'o'in hannu wadda matar gwamnan jahar Bauchi, Hajiya Aisha Lami Bala Muhammad (Kauran Bauchi) ta kaddamar da bukin yaye kashi na farko a wajen taronmu na kasa.

Jahar katsina, daya daga cikin membobin wannan kungiya tare da hadin guiwar shugabannin jahar ta katsina sun dauki nauyin koyar da wasu yara marayu sana'ar hannu kuma sun dauki nauyin karatunsu da kudin zirga-zirgarsu ta zuwa makaranta da wajen aiki, domin su tashi cikin gata da kwanciyar hankali.

Bayan haka muna gudanar da aiyuka masu yawa da su ka shafi fadakarwa game da illar shaye-shaye da zaman kashe wando a tsakanin matasan Najeriya, da alfanun zaman lafiya a jahohi daban-daban, da wasu al'amura na hadin kai da cigaban al'umma da a yanzu lokaci bazai bani damar zayyano sunayensu nan ba.

Kuma in sha Allah zamu ci gaba da wannan aiki, kamar yadda mu ka fara.

Sannan yanzu haka muna kan shirye-shiryen taimakawa yara ta fannin ilimi a jahar Adamawa.

Kafin na kammala wannan jawabi kamar yadda muka saba yi a kullum daga lokaci zuwa lokaci a social media, mukan tunatar da kawunan mu sharudda ka'idojin da aka gina wannan tafiya a kan su, domin mu cigaba da kiyayewa da kuma nusar da juna musamman bakin fuska da su ke shigowa  tafiyar tamu a baya bayan nan. Yau ma dai gamu dauke da waɗannan Ka'idoji kamar haka:

Kungiyar #RAYAAS tana maraba da duk wani rubutun zube (Essay) ko muqala (Article) da dukkan wani rubutu (Write-ups) mai ɗauke da wa'azantarwa, Ilmantarwa, tunatarwa da ma nishaɗantarwa (musamman me ɗauke da wani darasi)

Kungiyar #RAYAAS bata bukatar duk wani rubutu daya danganci musu ko jayayya gameda harkokin da suka shafi siyasa, addini, wasanni, Fina finai ko ma Tallace tallace. Sannan babu cin mutuncin wani ko wasu ko taba shaksiyyar (Personality)  wani malami ko shugaban da wasu ke girmamawa.

Shafin Kungiyar #RAYAAS baya bukatar yada duk wani hoto ko bidiyo daya danganci batsa ko nuna tsiraici, hakanan bama maraba da kowanne irin sako dake ɗauke da habaici, shaguɓe, gugar zana ko wasu kalamai da zasu iya haifar da rashin jin daɗin wani/wata ko wadansun mu.

Wajibine fassara dukkanin wani rubutun da aka yi shi da wani yare, zuwa harshen Hausa kafin shigowa da shi cikin zaure, domin amfanuwar daukacin jama'ar da muke tare da su musamman Hausa/Fulani baki daya.

Wajibine a dakatar da kowane irin posting a duk lokacin da ake kan tsakiyar gabatar da wani shiri musamman a zaurukan Kungiya ta WhatsApp, sai dai ga wanda ya nemi izini aka bashi dama, a cikin shirye-shiryen da suke da alaka da tambayoyi da amsa

A karshe wajibine, yin biyayya ga dukkanin wadannan dokoki da umarnin shugabannin kungiya kuma tilas, domin kaucewa duk wani sabanin fahimta dan tabbatar hadin kai da kuma karfafa zumuncin da yake tsakaninmu baki daya.

Da fatan Allah madaukakin sarki ya kara bamu ikon cigaba da kiyayewa.

Muna godiya!

Na ku Auwali Adamu Differences
(Danmasanin RAYAAS)
Sakataren Tsare-Tsare Na Kasa Baki Daya)
Reactions
Close Menu