Siyasa Ce Ta Sa Gwamnatin Ganduje Rufe Gidan Hotona – Sani Danja


Fitaccen jarumin Kannywood kuma mawaki, Sani Musa Danja, ya ce banbancin siyasa ne kawai ya sa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano rufe gidan daukar hotonsa.

Hukumar ta ce ba a yiwa kamfanin rijista da ita ba kamar yadda dokokin jihar da suka shafi gidajen kallo da daukar hoto da fina-finai suka tanada.

Sai dai jarumin, wanda ya yi fice a jerin ‘yan Kannywood din da ke goyon jam’iyyar adawa ta PDP da kuma Kwankwasiyya, ya ce ya cika dukkan ka’idojin da dokar Najeriya ta tanada wurin kafa kamfani.

“Babu wata maganar yin rijista, akwai da ma mutanen da ake hakonsu saboda dalilai na siyasa kawai,” kamar yadda ya shaida wa BBC.

A nata bangaren, hukumar tace fina-finan ta hannun shugabanta Malam Isma’ila Na’abba Afakallah, ta ce babu siyasa a cikin lamarin ko kadan.

“Kamfanoni da dama irin wadannan da suka sabawa dokokinmu na yin rijista muna daukar mataki a kansu kamar yadda dokata ta tanada”.

Sai dai ba wannan ne karon farko da ake samun takun-saka tsakanin ‘yan Kannywood magoya bayan Kwankwasiyya da kuma hukumar ba.

Kuma jama’a da dama na ganin hakan na da nasaba da banbancin siyasa duk da cewa akodayaushe hukumomin da abin ya shafa na musanta hakan.
Reactions
Close Menu