YOWA: An yi Taron Ƙaddamar Da Jagororin Ƙungiyar Marubutan Jihar Yobe


A jiya Asabar babbar ƙungiyar nan ta mawallafa, manazarta, marubuta waƙoƙi da marubuta masu amfani da kafafen zamani a yanar-gizo da ake kira Yobe Writers Association ko kuma 'YOWA' a taƙaice wadda ita ce ta farko kana kuma ƙungiya mafi girma a faɗin jihar ta Yobe da ma yankin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya bakiɗaya ta gudanar da taron rantsar da jagororin ƙungiyar a garin Potiskum biyo bayan babban zaɓen ƙungiyar da ya gabata.

Taron wanda ya gudana a daƙin taro na makarantar Premier Academy dake Potiskum ya samu halartar Jagorori masu muƙaman farko wanda aka rantsar da su don cigaba da tafiyar da al'amuran ƙungiyar bayan rushe jagororin riƙon ƙwarya da aka yi watanni biyu da suka gabata tare da gudanar da babban zaben.
Mahalartan dai sun baƙunci garin Potiskum ɗin ne daga dukkanin garuruwan dake shiyyoyi uku a faɗin sassa na jihar wanda suka haɗa da marubutan ƙaramar hukumar Nguru dake shiyyar arewacin jihar, marubutan shiyyar gabas da suka haɗa da Damaturu babban birnin jihar, da mahalarta da suka fito daga ƙananan hukumomin shiyyar kudancin jihar da suka haɗa da; ƙaramar hukumar Fika, ƙaramar hukumar Nangere, da kuma ƙaramar hukumar Potiskum wanda suka karbi baƙuncin takwarorin na su.
A yayin gudanar da taron dai, jagororin sun ɗauki alƙawurin yin ayyukan ofisoshin su bisa amana, riƙon gaskiya, tare kuma da tabbatar da wanzuwar haɗin kai, girmamawa gami da mutunta juna kuma kowannensu ya bayyana ƙudurrai da kuma ayyukan cigaban da zai yi ƙoƙarin samarwa a ƙarƙashin ofishinsa.

Jerin mahalartan dai sun haɗa da Malam Bukar Mustapha gwarzon gasar kainuwa kuma sabon shugaban kungiyar, Ma'ajin ƙungiyar Malam Jamil Alhassan shahararren manazarci, marubuci kuma babban mawaƙi tare da kakakin ƙungiyar kuma Editan Mujallar ADABI Malam Musaddam Idriss Musa da Malam Muhammad Maiyo Niniko jami'in hulɗa da jama'a, da Hajiya Amina Ma'aji mataimakiyar shugaba, da Saratu Tinja jami'ar sanya ido, da Hafsat Fulani jami'ar bincike, da Hussaini Muhammad Inusa magatakarda da Idriss Umar Elhaj.
Reactions
Close Menu