Fitattun mutanen da 'yan uwansu suka mutu a shekarar 2020


Daga farkon shekarar 2020 zuwa yanzu da muke cikin watan Maris da shi ne na uku a jerin watanni goma sha biyun da ake samu a shekara, an samu mace-mace da kuma radadin rashin makusanta ga jerin wasu fitattu kuma shahararrun mutane masu baiwa ta musamman a cikin al'umma da suka hada da manyan marubutan Hausa, manyan jaruman fina-finai da ma mawaka.
Wannan rahoton da wakilin Mujallar ADABI Musaddam Idriss Musa ya hada, waiwaye ne ga jerin wadancan rashe-rashen da suka faru da makusantan wadannan fasihai kamar haka:


1. Marubuciya Jamila Babayo: a ranar 1 ga watan Janairun 2020 ne mijin wannan fasihiyar marubuciya Alhaji Sa'idu Ibrahim wanda ma'aikaci ne a fadar gwamnatin jihar Yobe ya kwanta dama biyo bayan wata gajeriyar jinya inda kuma mutuwar tasa ta kasance cikin makonni kadan biyo bayan samun nasarar da marubuciyar ta yi na zamowarta gwarzuwa ta uku a jerin gwarazan gasar rubutu ta mata zalla mai taken Hikayata wadda kamfanin yada labarai na BBC Hausa ke daukar nauyi a kowace shekara. Mijin marubuciyar wadda 'yar asalin jihar Yobe ne ya rasu ne a asibiti karantarwa na Maiduguri babban birnin jihar Borno inda a yanzu ya cika watanni biyu da kwanaki goma da rasuwa.

2. Jaruma Halima Atete: a ranar 6 ga watan Fabairun 2020 ne mahaifiyar wannan shahararriyar jarumar da tayi fice a masana'antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood mai suna Hajiya Maryam Yusuf ta rasu a safiyar ranar bayan doguwar jinya da ta yi fama da ita. Marigayiyar dai ta rasu ne a wani a wani asibiti dake babban birnin tarayya Abuja.

3. Marubuci Kabir Yusuf Anka: a ranar 24 ga watan Fabairu na shekarar 2020 wannan shahararren marubucin kuma kwararren mai aikin dab'in littattafan Hausa dake garin Kano da zama ya rubuta sanarwar rashin dansa Hassan da ya yi wanda ya kasance Jariri ne da bai ko cika makonni biyu ba a duniya. Marubucin wanda a mako daya kafin afkuwar lamarin ya bayyana tsananin farincikinsa bisa haifar 'yan biyun da mai dakinsa ta yi da guda ya kasance da namiji dayar kuma 'ya mace wato Hassan da Usaina saboda yadda Allah ya cusa masa sha'awa da kuma son 'yan biyu kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook ya sake bayyana komawa warin dan nasa cikin siga mai bayyana tsananin so da kuma shauki irin na da mahaifi.

4. M. Sharif: a ranar 3 ga watan Maris din nan da muke ciki ne kuma wata sanarwar ta sake fita dake bayyana rasuwar mahaifin su shahararren mawakin Hausan nan kuma dan wasan fim wato Umar M. Sharif wanda kuma kani ne ga gogaggen jarumin nan Abdul M. Sharif da kuma fitaccen mai kofar da rawan nan a masana'antar Kannywood Mustapha M. Sharif. Sanarwar wadda shi Umar din ne ya wallafa a shafinsa na Instagram cike da alhini da kuma nuna dangana da kuma soyayya ya rubuta ne kamar haka, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un, ina mai alfahari da samun mahaifi kamarka, domin kuwa ka yi mana dukkan abin da ya kamata mahaifi ya yi wa ’ya’yansa. Allah Ya jikanka da rahama Allah Ya gafarta maka. Allah Ya sanya Aljannan ta zama mazauninka. Allah Ya yafe maka dukkan kurakuranka. Ya ubangiji muna godiya a gareka.

Muna masu yi musu addu'a da kuma fatan Allah ya jikansu ya kuma gafarta musu, amin.

Rahoton Musaddam Idriss Musa


Reactions
Close Menu