Jarumar ta bayyana kudurin na ta na taimakawa al’umma a shafinta na Twitter, inda ta ce:
“Zan bayar da buhun shinkafa guda dari (100), kwalin magi ajinomoto guda dari (100), da kuma jarkar mai guda hamsin (50), ga marasa karfi, idan kun san wani wurin ‘yan gudun hijira ku sanar dani dan Allah ta hanyar sanya adireshin a bangaren sharhi, mutane na za su kai musu dauki.“
Sai dai kuma mutane basu nuna goyon bayasu ba akan ta bayar da taimakon ga ‘yan gudun hijira, inda da yawa suka nuna cewa akwai mutane da yawa da suke bukatar wannan taimako na ta ba wai iya ‘yan gudun hijira ba, wasu ma cewa suka yi akwai mutanen gari da sun fi ‘yan gudun hijira shan wahala a wannan lokacin.
Mutane da yawa dai suna ta iya bakin kokarinsu wajen ganin sun bayar da tallafi a wannan lokaci da annobar ta Coronavirus ta addabi duniya, wacce har yanzu ba a samo maganinta ba.
0 Comments