A madadin mai girma shugaban kungiyar Rayuwarmu Ayau Ta Kasa Malam Shehu Na Amo Dange (Uban Dawaki) da shugaban kungiyar RAYAAS reshen jahar Adamawa
Da iyalan gidan Malam Adamu Baba Ahmad da na Malam Muhmuda
Suna farin cikin gayyatarku zuwa bukin daurin auren 'ya 'yansu, Muhammad Faisal Adam (Mataimakin shugaban kungiya reshen jahar Adamawa) da amaryarsa Hajiya Lubabatu Muhammad
Wanda Za'a Daura In Sha Allahu Kamar Haka:
Rana: 27 ga watan Maris, 2020.
Lokaci: Bayan saukowa daga sallar Juma'a da misalin karfe 02:30 na yamma.
Waje: Anguwan Huji gidan Alh. Adamu Yadeeya hanyar zuwa garkida da ke cikin karamar hukumar Gombi, ta jahar Adamawa.
Ka da a manta akwai gagarumar liyafa ta musamman tare da lashe-lashe da tande-tande bayan an daura aure.
Duba da yanayin da ake ciki na takaita zirga-zirga da tafiye-tafuye, jama'armu da ke nesa muna baran addu'o'i daga bakunan ku masu albarka, da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu zaman lafiya da zuri'a ta gari
Na kusa bamu daukewa kowa ba sai mai larura
Ga mai bukatar karin bayani ya tuntubemu akan wadannan lambobi kamar haka:
08036514180 ko kuma
08068265678
Allah ya bada ikon halarta...
Amiin
Sanarwa
Auwali Adamu Differences
(Sakataren Tsare-Tsare Na Kasa Baki Daya)
Turawa abokai dake