Na shigo Kannywood ne domin na bada tawa gudunmawar - jaruma Khadija Yobe


KHADIJA Alhaji Shehu da ake yiwa lakabi da Khadija Yobe na daga sabbin jarumai matan da ake yiwa kallon sun shigo masana'antar Kannywood da kafar dama saboda duba da aka yi kan farin jini da kuma karbuwar da ta samu har ma ta kai ga samun damar fitowa a a wasu daidaikun manyan fina-finai.
Jarumar wadda ta kasance cikakkiyar bafulatar jihar Yobe ce dake a yankin arewa maso gabashin Najeriya kuma tsohuwar dalibar Jami'ar jihar Yobe wato (YOSU) inda ta karanci digirinta na farko a fannin jagorancin jama'a wato Public Administration ta bayyana irin nata hangen da kuma duban da take yiwa masana'antar ta Kannywood. Ga yadda hirar ta kasance
M.A: Shin ya aka yi kika samu kan ki a Kano kasancewarki mazauniyar jihar Yobe har ma kuma kika samu damar shiga masana'antar finafinan Hausa ta Kannywood?
Amsa: To gaskiya garin a Kano ni ba baƙuwa ba ce, domin lokacin da rikicin Boko Haram ya yi tsanani sai baban mu ya taso, mu ka dawo Kano. Sai da mu ka yi shekara huɗu, mu ka koma gida.
To kuma da man mu na da 'yan'uwa da yawa a nan, don haka ko da na gama karatu na, na ji ina son na shiga harkar fim, sai na dawo na zauna a wajen 'yan'uwan mu. Don haka yanzu ina garin Kano da zama.

 Na zo masana'antar Kannywood ne domin ni ma na bada tawa gudunmawar, domin tun ina yarinya na ke so na yi fim, sai dai a lokacin ban samu dama ba."

M.A: Ko a wane fim ta fara fitowa, kuma zuwa yanzu finafinan da Khadija ta yi za su kai kamar nawa?

Amsa: To da ya ke ban daɗe da shigowa ba, don a cikin wannan shekarar ta 2020 ma aka fara sa ni a fim, amma dai fim ɗin da na yi wanda aka gan ni a ciki shi ne 'Wutar Kara', sai kuma 'Hikima' wanda a yanzu mu na aikin sa, ba a kammala ba. Sai dai na fito a wasu finafinan da yawa, ban riƙe sunan su ba, da kuma waƙoƙi, waɗanda sai nan gaba za su fito.


M.A: Kowanne jarumi yana da burin da ya ke shigowa harkar fim da shi. To ita Khadija Yobe menene nata burin?

Amsa: Ni dai babban buri na shi ne faɗakarwa ga al'umma kamar yadda sauran jarumai su ke yi, domin na san harkar fim akwai faɗakarwa a cikin ta, don haka na zo na bayar da tawa gudunmawar.

M.A: Kin fuskanci wani cikas ko matsala a yayin da kika nemi shigowa masana'antar fim?

Amsa: Gaskiya babu wata matsala da na fuskanta, domin baban mu ya na da fahimtar al'amura, don haka da na yi masa bayani, ya gamsu. Don haka da amincewar sa na shigo cikin harkar.

M.A: kin taba yin aure ne a baya kafin shigowarki masana'antar a yanzu?

Amsa: A'a ban taba yin aure ba gaskiya.


M.A: Shin ya ya kike ganin al'amura su na gudana a cikin Kannywood?

Amsa: Babu wata matsala, domin ni ban ga wani abu  ba kamar yadda ake ta faɗa. Sai dai mutane su gane, kowa da irin yadda ya ke gudanar da rayuwar sa - ko ɗan fim ko ba ɗan fim ba. Don haka bai kamata a rinƙa yi wa 'yan fim kuɗin goro a kan abin da aka ga wani ya yi ba.

 M.A: Wace shawara ko sako kike da shi ga sauran wadanda suke wannan harka ta fim?

Amsa: Ni dai ina kira ga 'yan fim da su haɗa kai domin sai da haɗin kai ne za a cimma nasara a kan abin da aka sa a gaba. Ina yi wa kowa fatan alheri. Allah ya ƙara haɗa kan mu.

 M.A: To amin Khadija.
Reactions
Close Menu