Kannywood: Sharhin Fim Ɗin 'Abbana' Na Kamfanin Abnur EntertainmentSUNAN FIM:                 ABBA NA
KAMFANI:                     Abnur Entertainment, Kano
LABARI/TSARAWA:     Yakubu Kumo
UMARNI:                     Sadiq N. Mafia
TAURARI:                    Ali Nuhu, Aisha Aliyu, Sadiq Sani Sadiq, Tijjani AsaseFIM din ya na magana ne a kan wani mutum (Ali Nuhu) da ’yar sa Nabila (A’isha Aliyu) wadda sakamakon kamuwa da ya yi da hawan jini har ya kasance ba ya iya yi wa kan sa komai sai ita ’yar ta yi masa. Hakan ya sa ta kwadayin son ta aure shi. Daga baya aka nuna ba shi ya haife ta ba, rike ta ya yi. Ciwon sa ya tashi bayan aure, ya kwanta jinya kafin ya rasu, ta koma wa tsohon saurayin ta, Umar (Sadiq Sani Sadiq).

ABUBUWAN BURGEWA

ü    Labarin ya na da kyau.

ü    Hoto da sauti sun fito.

ü    Guraren da aka dauki fim din sun dace.

ü    Taurarin labarin sun hau matsayin su yadda ya kamata, musamman Nabila karama.

KURAKURAI

1. Bai kamata Alhaji ya ce, “Addu’ar da na yi wa Allah” ba, sai dai ya ce, “Addu’ar da na yi wa Nabila.”

2. Mafi akasari an san gidan biki da jama’a, musamman dangin uwa ko makota wadanda ba a rasa aminai makusanta ba, amma har aka kai mahaifiyar Nabila asibiti ba a nuno mana wata alama da za ta shaida mana ana biki a gidan ba. Haka babu rakiyar wani zuwa asibitin sai amarya.

3. Ba a nuno mana alamar Nabila ta turo wa Umar sako a wayar sa ba, illa ya kira har ta katse ba ta dauka ba, a karshen maganar zucin sa sai mu ka ji ya na sallallami, sannan mu ka gan shi a asibiti. Ta wace hanya sakon ya samar da kan sa?

4. Da mamaki uwar amarya ta rasu ana gobe daurin aure, amma a ce iyayen ango ba su sani ba, har sai washegari da rana su ji labarin a bakin ango, bayan a ranar ake daura aure.

5. Yadda Umar ya ke ba wa mahaifiyar sa labarin asalin su Nabila, kamar ba a yi bincike ba kafin a fara maganar lokacin ne za a fara binciken.

6. Umar ya koma gida, amma da aka sake nuno shi a asibiti sai mu ka ga hular sa tun ta farko ce. Ko da an canza shadda amma kalar sai ta saje da waccan, don haka ba kowa zai lura Umar ya sauya kaya ba. Sannan a cikin maganganun Nabila sai ya kasance kamar sun yi kwanaki a asibitin, “…yau wannan, gobe wannan…”

7. Tunda akwai maigadi a gidan, me ya hana Alhaji ya dauko wanda zai kula da shi maimakon ’yar sa?

8. A rayuwar zahiri babu waka, amma kawai sai mu ka ga Nabila da Umar tare da abban ta su na waka ba tare da an nuna tunani ko mafarki ba ne wakar.

9. Abubuwan da su Lawal (Tanimu Akawu) su ka yi ya wuce gona da iri yayin jin rasuwar dan’uwan su.

10. Da ma a ce ba Nabila ce ta bada labarin rayuwar baya ba, da fim din ya fi armashi.

11. Duk da so so ne, amma yadda Nabila ta zabi wani ba Umar ba, zai yi wahala ya karbi uzurin ta a gaggauce.

12. Duk lokacin da za a nuno Abba a asibiti jallabiya daya ce ake nuno shi da ita.

13. Ya kamata mu ga karshen su Habu (Tijjani Asase) kafin a kammala fim din.

Reactions
Close Menu