Zan kawo haɗin gwiwa tsakanin Kannywood da Nollywood - Paul Sambo


WANI fitaccen jarumi a masana'antar finafinai ta kudancin Nijeriya, wato Nollywood, mai suna Paul Sambo ya bayyana cewa zai dage wajen kawo kyakkyawar alaƙa tsakanin Nollywood da Kannywood.Jarumin ya kuma bayyana matuƙar farin cikin sa dangane da yadda ya samu karɓuwa a Kannywood a lokacin da ya shigo masana'antar domin yin aiki.Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar sa da mujallar Fim a Kano a wajen ɗaukar wani fim ɗin Hausa Hikima Movie. Hafizu Bello shi ne daraktan fim ɗin, yayin da Alhaji Sheshe ya zamo mashiryin fim ɗin.An gudanar da aikin shirya fim ɗin a ƙarshen watan Janairu na 2020.Shi dai Paul Sambo, ya kasance ɗaya daga cikin jaruman Nollywood tsawon shekaru 20 a yanzu, domin kuwa ya fara fim ne a shekara ta 2000, inda ya fito a Oduduwa."Tun daga sannan na ke cikin harkar fim zuwa yanzu. Kuma na yi finafinai masu yawan gaske tunda ba zan iya kawo su ba a yanzu. Amma dai na san wanda aka fi sani na da shi a duniya shi ne 'The Sons of the Caliphate'."To amma dai Paul ɗan Arewa ne, domin ɗan salin Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ne a Jihar Bauchi."Sai dai duk finafinai na na Nollywood ne kuma sai ga shi a yanzu na samu kai na a fim ɗin Kannywood. To ka ga kowa ya bar gida, gida ya bar shi," inji shi."Yanzu da na zo gida sai gidan ya karɓe ni. Amma dai ni abin da na sani, idan ka na yin fim mutane ne su ke gani su ke faɗar ka, don haka idan Allah ya yi cewa za ka ɗagu zai biyo ta mutane ne, don haka duk abu ne mai sauƙi a wajen Allah."Mujallar Fim ta tambayi Paul Sambo yadda aka yi har ya shiga cikin fim ɗin Hausa. Sai ya amsa: "To idan ka kula, shi harkar fim ne, kuma kamar yadda shi Hafizu Bello ya kira ni, na fahimci ita babbar masana'anta ce, domin gaskiya girman ta babba ne don ta yi fice a duniya."To da shi Hafizu Bello ya kira ni, ina jin a farkon watan Janairu mu ka yi magana da shi, mu ka yi magana ta hanyar Balala, mu ka yi magana da shi kan wannan fim ɗin Hikima Movie, to da su ka faɗa mini tsarin fim ɗin, sai na ga wannan fim ne wanda ya kamata na yi, domin ko babu komai ina da ɗimbin masoya a cikin wannan masana'anta ta Kannywood tun daga 'Son Of Caliphate' da na fito a Sarki sai ya zama na samu masoya masu yawa a Kannywood."To kawo ni da su Hafizu Bello su ka yi ina ganin wani farko ne na samun haɗin kai domin a bunƙasa masana'antar, domin ka san babu abin da aka fi samu da sauƙi sai idan an haɗa kai, domin an ce sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi."To abin da ya faru kenan. Kuma da na zo, na gamsu da yadda abin ya ke tafiya. Don haka ina godiya ga Allah da kuma mutanen da su ka ba ni wannan damar domin da Kannywood da Nollywood duk abu daya ne."Mun tambaye shi kan cewar da ya ke wannan shi ne karo na farko da ya shigo Kannywood domin gudanar da aiki, ko yaya mu'amalar su ta kasance da 'yan Kannywood?"Haba, ai gaskiya na ji daɗi ɗari bisa ɗari. Mun yi mu'amala; kowa ya yi murna da gani na, don a baya su na gani na a nesa, yanzu na matso kusa, don haka sun yi murna sun ji daɗi kamar yadda na ji ni ma."Don haka duk wata ƙwarewa da na samu a Nollywood, duk gaba ɗaya ina shirin kawo ta cikin Kannywood. Kuma duk wani abu da na gani ana son gyara, to zan gyara. Sannan akwai ƙanana masu tasowa, su ma a tayar da su."Wannan shi ne girman, don idan ka girma, to sai ka tashi na ƙasa shi ma ya ɗaga. To abin da na ke shirin yi kenan."Don haka zan ci gaba da zama da 'yan Kannywood mu rinƙa mu'amala domin mu na son a wannan shekarar ta 2020 ta zama shekarar kawo canji a harkar fim a Kannywood."Domin haka ma a yanzu akwai wasu finafinai a ƙasa wanda za mu shirya. Don haka ina fatan za a  samu canjin da mu ke so mu kawo."Daga ƙarshe, Paul Sambo ya yi fatan ɗorewar haɗin kai a tsakanin Kannywood da Nollywood.
Reactions
Close Menu