A'isha: Rubutacciyar Wakar Musaddam Idriss


A'ISHA

Sunan da bai zama naki ba
Sautin da ba na muryarki ba
Kalaman da ba daga gun ki ba
Girki idan fa ba naki ba
`
Koda ruwa ne ba ni sha
In bai fito ta gun A'eesha
Koda ya zamma ina tasha
Sai kin fadi mini je ka sha
`
Karfi na sonki a zuciya
Girman da yayyi na mamaya
Wane na tekun maliya
Balle na Jan ruwan Indiya
`

Ga duniya yau na fada
Kowa ya ji ni ba yin rada
Tabarma ta so na shimfida
Gare ki hau kai A'isha

(C) Musaddam Idriss Musa
02.Apirilu.2020
Reactions
Close Menu