Covid19: Jaruman Kannywood sun girgiza bisa mutuwar Abba Kyari

Ali Nuhu            Hafsat Idriss          Sani Danja


Biyo bayan sanarwar da ta fito a daren jiya Juma'a daga fadar shugaban kasar Najeriya wadda ke dauke da sakon mutuwar shugaban ma'aikata ta fadar gwamnatin ta tarayya wato Malam Abba Kyari a sakamakon jinyar makonni da yayi bayan ya kamu da cutar nan ta Covid-19.
Daukacin ma'abota amfani da kafafen sadarwa a wayewar garin yau Asabar musamman ma taurarin masana'antar shirya fina-finai ta Kannywood da suka hada da jarumai, mawaka, da kuma marubutan littattafai da kuma fina-finai sun wayi gari ne cikin matukar kaduwa da kuma jimamin rashin da ya faru.


Marigayi Abba Kyari 

Da suke bayyana jimami da kuma sakonnin ta'aziyyarsu jaruman wanda suka hada da Ali Nuhu, Abba El-mustapha, Ibrahim Maishinku, Hafsat Idriss, Nuhu Abdullahi, Shamsu Dan Iya, Teema Makamashi, da kuma masu bada umarni da suka hada da Aminu Saira, Abdul Amart Mai Kwashewa da sauransu na daga jerin jaruman da sakonnin su suka fara mamaye kafafen sada zumunta a safiyar yau inda suke janjantawa cikin kalamai dake bayana kaduwa da kuma girgizar da suka yi gami da yi wa marigayin addu'o'in samun dace.

Reactions
Close Menu