Coronavirus ta mayar da 'yan fim abin tausayi - Adam A. Zango

Adam A. Zango

Tauraron fina-finan Kannywood, Adam A. Zango, ya ce coronavirus ta mayar da 'yan fim abin tausayi saboda ta tilasta musu zaman gida.
Sai dai tauraron ya ce hakan ya fi domin kuwa samun lafiya ya fi neman kudi.
A cewarsa, annobar coronavirus ta shafi sana'arsu sosai kasance ta hana mutane cakuduwa da juna.
Ya ce a matsayinsa na tauraro da mawaki, babban aikinsa ya shafi zuwa taron jama'a don haka bai wa mutane umarni su zauna a gidajensu ba tare da zirga-zirga ba tamkar tsayar da sana'arsa ce.
Reactions
Close Menu