'Korona a Kano' Wakar Khalid ImamA Kano yau ga Korona
Ya Ilahu muna gare ka
Kariya duka ba ya taka 
Ba tsumi yau ba dabara
Sai miƙa wuya wajen ka

A gida kowa ya zauna
 'Ya'ya mata da dangi
Ba fita kuma babu yawo
Ko zuwa zance da karta
Kasuwanni duk a kulle

Cunkuso duk a dai na
Ba a so jama'a su taru
Gida na biki da kallo
Gwamna ya ce mu gane
Lafiyar mu a yau mu kare.

Fuska baki mu kare
Domin ƙwayar Korana
Ta nan ke kama Bawa
Numfashi duk ta shaƙe
Nan take ta kai kushewa.

Ba a son duk mai Korona
Yai mu'amulla da kowa
Yin hakan kan sa ta haihu
Jama'a da yawa ta danne
Da wuƙa wai don ta yanka

Killace kai har iyali
Masu yi suke da riba
Ba asara ko ta ahu
Kai rahoton mai Korona
Shi riga kafi wajibi ne

Magana a yi nesa-nesa
Tazara sosai a bayar
Sha ruwa sosai a kullum
Domin cutar Korona
Shan ruwa na daƙile ta

A Kano yau ga Korona
Lafiya rayuka mu lura
Hannaye duk a wanke
Sabulu sanya ka cuɗa
Don tsafta na da kyawu

Ita annobar Korona
Ta fi hantsi kewaya wa
Zazzaɓinta yana da ƙarfi
Tarinta yana da na ci
Taurin kai ta fi jaki.

Wannan cuta mu duba
Yaro tsoho da babba
Mai kuɗi talaka da sarki
Soja liman da gyartai
In ta samu sai ta danne.

Ta kar da yawa a China
In kana Lagos ka zauna
Umarni na Manzo
Annoba in ta ɓulla
Kar ka je ko ko a zo ma.

Allah sarkin sarauta
Jiƙan mu dare da rana
Sauƙi duka na wajen Ka
Rana da wata da sammai
Lafiyar su tana gare Ka.

© Khalid Imam
15/3/2020
Reactions
Close Menu