Hana maigidanki fita waje da wannan sirrin kwalliyar


Kasancewar masu sana’ar kwalliyar fuska suna zabga kudi, wannan dalilin ne yasa na ga ya dace amaren gobe su koyi yadda za dandasa kwalliyar da kan su ba tare da sun ko da kashe ko kobo ba, kuma yadda ko da bayan sun yi aure ne za ku iya yin irin wannan kwalliya domin burge angonku a kullum.
Ya kamata fitar da za a yi ta biki tafi ta koyaushe kyau. Saboda duk wadda ta kalli amarya koda sau daya ne ba sai ta tambaya wace ce amaryar ba.
Kayan kwalliya
Gazal kalar baki da mai ruwan kasa
Eye shadow
Hoda
Mascara
Jambaki (ja, shi ne ake yayi yanzu)
Fandesho (foundation)
Hodar Blush
Gashin ido na roba (faud eyelashes)
Ma’askar gira (tweezers)


Ka’idoji 
Kafin a fara komai, za ki wanke fuskarki da sabulu marar karfi .
A dauko ma’askar gira( tweezer) sai ki aske girarki.
Sannan sai a jira fuskar ta bushe. Bayan fuskar ta bushe, sai a shafa mai kadan a fuskar musamman ma in fatar mai gausti ce. In ko fatar mai maiko ce, to ba sai kin shafa mai ba.
A shafa hodar fandesho mai launin fata. Sannan a bar ta kamar minti uku. Sannan a samu hoda mai kama da launin fatar sai a shafa a fuska zuwa wuya da kunnuwa Saboda kada launin fuskarki ta bambanta da ta wuya.
A samu gazal musamman ma launi mai ruwan kasa (dark brown) sai a zana a girar da aka aske.
“Eye shadow” launin kayan da zaki sa sai a shafa kamar iri biyu a kan fatar ido.
Kwalli; a shafa a ido sai a samu maskara (mascara) launin shudi (blue) ko baki a gashin fatar ido, ana taje shi.
Hodar ‘blush’; a shafa a kumatu.
Jambaki; a shafa a lebba. Bayan an yi haka, sai a sake samun gazal mai launin kasa wato (dark brown) a bi lebban bakin da shi. Bayan an gama wadannan abubuwa, za a ga fuskar ta canja sosai.
Reactions
Close Menu