Kurunkus: Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano da Arewa24 sun daidaitaBiyo bayan dannowar kai na wasikar da Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano dake Najeriya ta yi wadda ke dauke da sakon hani da cigaba da nuna wsu shirye shiryen gidan talabijin din Arewa24 da suka hada da Gidan Badamasi da kuma shirin Kwana Casa'in, a makon da ya gabata aka kai ga samun daidaito a tsakanin gidan talbijin din da kuma hukumar inda suka sulhunta game da ita wannan takaddama.


Sanarwan sulhun wadda ta fito ta bakin Isma'ila Na'abba Afakalla shugaban hukumar, ta bayyana cewa, "Bayan zama da aka yi tsakanin hukumar tace fina-finan Kano da jami'an gidan talbijin na Arewa24 jiya Alhamis da yau Juma'a, an kai ga matsaya inda aka amince za a cire bangarorin da suke dauke da abubuwan da al'umma ke korafi a kai."


Afakallahu din dai ya kuma kara da cewa a halin yanzu gidan talbijin na Arewa24 din ya amince cewa nan gaba ba zai sake nuna wani fim din Hausa ba sai "ya kasance wanda yake da shaidar tantancewa da ta fito daga hukumar tace fina-finai".


Ko mene ne ra'ayoyinku dangane da matsayar da aka samun? Za ku iya aika mana sakonni kai tsaye ta dukkan shafukan mu na yanar gizo ko kuma ta hanyar sakon kai-da-kai ta lambar mu kamar haka +2349026249597.

Reactions
Close Menu