Rubutacciyar Waka: 'Matata' - Na Musaddam Idriss
🌹MATATA🌹
1▪
Rabbi wanda yayi ni yai ƙunci
Shi yaso ya hane ni yin bacci
Zuciya raɗaɗi da ma ɗaci
Yau take na rashinki matata

5▪
Nayi-nayi a rai na manta ki
Amma a kullum ƙara ƙaunarki
Zuciya ta take da begen ki
Sake ganinki kawai nake fata.

9▪
Kullum gaban ƙabarinki sai kuka
Ya ci ƙarfi na da sheshsheƙa
Ni Musaddam babu sam shakka
Ba za ni manta dake ba matata

13▪
Mutuwa baki min ba sam gata
Ruhi na wadda na so ki kai sata
Shin hakan da kikai ya cancanta?
Roƙo nake dawon da matata.

17▪
Zullumi kwance cikin rai na
Tausayin ɗan ƙanƙanin ɗana
Da shi nake kwana, wunin rana
Sanda dake ba ni yinsa matata.

20▪
Rabbi gani gaba cikin kuka
Na zube domin na roƙe ka
Rahamarka ka kaiwa mai sonka 
Ina nufin ka jiƙanta matata.

(C) Musaddam Idriss Musa
02.Apirilu.2020
Reactions
Close Menu