Shafin Fasihiyyah: Annobar Korona Wakar Khalid Imam

Masu gaɗa suna ta shewa,
    'Yan caca da masu karta.

'Yan daudu da ma kilaki,
   Sun tsere babu kowa.

Tituna leƙa ka duba,
   Kasuwanni har mashaya.

Makarantu ga sinima,
   'Yan kwalo da masu dambe

Sun ɓace duk don Korona,
   Ko 'ina duka tsit kake ji.

Ta bi gwamna har gidansa,
   Ta shaƙi wuyan minista.

Can a Ladan ga Yarima,
   Ta bi shi cikin turaka.

A Abuja har a Villa,
   Ta shige ciki ta yi sheƙa.

Tai ƙwayaye ta yi 'ya'ya,
   Annoba ce ta gaske.

A masallatai da coci,
   Duk an koma ga Allah.

Sarki mai shirya komai,
    Wanda Shi ke share sharri.

Ba tsumi kuma ba dabara,
   Duniya yau an bi Allah.

Masu sheƙe aya su more,
   A ƙasar Italiya har Amurka.

Ƙasar Sin can a Chana,
   Ta kai da yawa kushewa.

A Farisa har Faransa,
   Babu kowa yau a titi.

Kufai ka kira yi Turai,
   Champions League an yi hutu.

Ba a yin zancen Ronaldo,
   Haka Missi ba batunsa.

Ita dai cutar Korona,
   Cuta ce ba bu shakka.

Ba ta kunya ba ta tsoro,
   Ba ta sabo ko sanayya.

Yau mutum ya gane cewa,
    Bai da karfi sai na Allah.

Bai da sauran duk dabara,
   Kariyarsa tana ga Rabbu.

Gatan kowa Ilahu,
   Mui ta bauta mai da ɗa'a.

Mu rabauta a yau da gobe,
   Don ko dai cutar Korona.

Wa'azi ce babu shakka,
   Kurciya in ta yi kuka.

Saƙo nata ban da wawa,
   Bare gaula da soko.

Hankali kura kira shi,
   Ta yin zabari na guga.

Mai rabo shi ke rabauta,
   In an wa'azi ya gane.

Zunubansa ya nemi tuba,
   Kan ya ji shi cikin kushewa.

© Khalid Imam
26/3/2020
Reactions
Close Menu