Sharhin labarin 'Mutuwata' Na Musaddam Idriss Musa


Sunan Labari: Mutuwata
Marubuci: Musaddam Idriss Musa
Shekarar Rubutu: 2020
Nau'i/Rukuni: Gajeren labari
Yawan Kalmomi: 445
Masu Sharhi: Muttaka A. Hassan, Hussaini Mohammed Inusa, Ali Dahiru, Kamal Bala.

Zubi Da Tsari
     Tare da cewa an zubo labarin ba tare da amfani da kanun labarai ko babi ba (wataƙila saboda gajere ne), labarin ya samu kyakkyawan tsari ta yadda aka yi amfani da sakin layi a wuraren da suka dace, sannan an saka ayoyi da waƙafi da sauran alamomin rubutu a inda suka dace.

Salo Da Sarrafa Harshe
     Marubucin ya yi amfani da sassauƙan salo wurin isar da saƙonsa. A ɓangaren sarrafa harshe marubucin ya yi ƙoƙari wurin yin amfani da hikima da azanci tare da kalmomi masu sauƙi wurin isar da saƙonsa, ta yadda hatta ɗaliban ƙaramar sakandire za su iya fahimtar saƙon.

Jigo
     Wannan labarin ya ginu ne akan jigon: “shuka alkairi" wato ƙoƙarin nusar da mu cewa idan muka aikata ba daidai ba a karshe za mu kare ne a cikin damuwa da nadamar rashin tabbaci na makoma mai kyau.

Warwarar Jigo
     A fakaice marubucin wannan labarin ya tsoratar da mu a kan rashin amfani da ƙuruciyarmu yadda ta dace; kamar yadda muka ga Baba Adamu wanda har tsufa ya riske shi ya kare rayuwarsa ne a hanyar sabon Ubangiji a karshe ya girbi gubar da ya shuka. Hakanan kuma labarin ya nusar da mu muhimmancin ilmi, kamar yadda muka ga Malam Muhammadu (liman) ya yi amfani da ilimi ya tunatar da Baba Adamu abin da bai sani ba ko ya sani ya manta a daidai lokacin da shi Baba Adamun yake kan gangarar barin duniya.

     Labarin dauke yake da muhimman darusan dake da matukar muhimmanci musamman a wannan zamani da muke ciki wanda za ka ga mutane suna holewarsu kawai wato aikata sabon Ubangiji kai ka ce ma sun manta da cewar za su mutu kuma za ayi musu hisabi.

    A cikin wannan dan gajeren labarin an yi kokarin bayyana mana wani babban ilimi wato sanin cewa dukkan mummunan aikin da bawa ya aikata matukar zai tuba, tuba na kwarai to tabbas Allah zai gafarta masa zunubansa. Akwai izina sosai a cikin labarin dake tsoratarwa kan kada mutum ya aikata manya-manyan laifuka irin wadanda tauraron labarin ya aikata domin ba dole ba ne ka aikata kuma ka samu lokacin tuba kafin mutuwarka. Ta iya yuwuwa ka mutu kana cikin aikata laifin wanda hakan zai zama babbar masifa gareka a lahira.

    Bugu da kari kuma marubucin labarin ya yi matukar kokari musamman kasancewar labarin dan gajere sosai amman yana dauke da abubuwa masu muhimmanci da suka hada da:
1. Tunatarwa
2. Fadakarwa
3. Wa'azantarwa
4. Nuni akan aikata aiyukan kwarai da dai sauransu.

Kurakurai (Ƙa'idojin Rubutu)
- Ya so ba yaso ba.
- Da ƙyar ba daƙyar ba.
- Da ke ba dake ba.
- Na ce ba nace ba.
- Kawo wa kaina ba kawowa kaina ba (jakada *wa* ce).
- A kan ba akan ba.
- Mahalicci ba mahalicci ba.

 Gyara Ko Tambayoyi
1-Marubucin ya rubuta a cikin labarin, "Ban san ya ake yi ko ya al'amarin yake faruwa ba, illa kawai daga ƙarshe na kan tsinci kaina tsamo-tsamo a cikin hali na aikata laifi ko alfasha". Ya za'ayi mutumin da yake aikata laifi da alfasha ace bai san ya ake hakan take faruwa ba? bayan labarin bai nuna sihiri a kai masa ba?

2- An nuna Baba Adamu tsoho ne ɗan shekara 80, amma an lafta masa cututtuka masu haɗari rututu kamar; daji, hawan jini, ciwon ƙoda, sida da ciwon sukari. Anya kuwa waɗannan cutukan ba su yi wa dattijo mai shekaru 80 yawa ba?

3- Anya dattijo ɗan shekara 80 zai iya rayuwa da waɗannan cututtuka har ma ya samu tattaunawa da mutane?

Shawarwari
Maimakon a tara wa Baba Adamu cutuka masu yawa da haɗari har kusan biyar, zai fi kyau a ce an rage su an liƙa masa cutukan da a ɗabi'ance sukan riski tsoho mai irin shekarunsa (musamman wanda bai yi ƙuruciya mai nagarta ba) wato kamar; makanta, ciwon ƙafa, ciwon baya da sauransu.
Reactions
Close Menu