Sharhin waƙar 'Mai Dalli Mai Dala Angon Kandala' (1) Na Abubakar Ladan Alan Waƙa


▪Mawaki: Aminu Ladan Abubakar (ALAN WAKA)
▪Nau'i: Wakar Baka
▪Rukuni/Aji: Siyasa
▪Shekarar Buga Waka: 2019
▪Tsayin Waka: Mintuna 9 da sakan 45
▪Jigo: Hannunka mai sanda ga 'yan siyasa, fadakarwa, wa'azantarwa, zaburarwa dasauransu.
▪Manazarci: Musaddam Idriss Musa
▪Shekarar Sharhi: 2019/2020

《《《《《《《SHIMFIDA》》》》》》》

Wakar "Mai Dalli Mai Dala" waka ce da ta fito a daidai lokacin da kasar Najeriya take tsaka a yanayi na halin juyin juya halin fama na yaki da miyagun laifuka da suka yi tarnaki da katutu ga cigaban kasar da kuma walwalar jama'ar cikinta. Matsalolin wanda suka hada da rashin tsaro sakamakon hare-haren 'yan ta'adda, yawaitar 'yan fashin kan hanya da sace-sace, da kuma matsala ta masu garkuwa da mutane kana da matsalar cin hanci da rashawa wanda ya zamo kashin bayan hauhawar dukkan sauran matsalolin sabili da zamowarsa ruwan dare a cikin al'umma. Inda a karshe saboda nisan da matsalar rashawar ta yi har ta kai matsayin da jita-jitar da talakawan kasa suke ji na sama da fadi da dukiyarsu da ake ya fara zama bayyanannen abu. Domin an kai ga wani mataki da jiga-jigan masu fada a ji daga mahukuntan gwamnati a sassa daban-baban na matakan mukami sun tsunduma ga wannan kazamin aiki na karbar na goro wannan yasa idanuwa suka yawaita akan gwamnati mai ci don ganin irin matakin da za ta dauka musamman saboda kasancewarta wadda tayi kaurin suna wajen nuna kyama ga aikata cin hanci da rashawa tare da barazanar hukunci irin na ba sani ba sabo kan duk wanda aka samu da hanu wajen aikata wannan laifi inda kuma har ta kai ga tana yiwa kanta take ko kallon cewa dukkan masu ruwa da tsaki a tafiyarta amintattu ne kuma masu kishin kasa.

        Sai dai kuma daukacin al'ummar kasar suna da shakku kan wasu tsiraru daga jiga-jigan mukarraban gwamnatin wanda hakan yasa suka dora alamar tambaya akan su bisa sanin su a baya ko kuma zargin da suke yi musu na aikata laifukan da suka shafi almundahana da babakere da kuma aikata laifukan cin hanci da rashawa.

        A wannan tafiya da ake yi ne daidai lokacin da ake tsaka da fara yakin neman zabukan shekarar 2019 aka saki wani dan guntun bidiyo mai dauke da hoton gwamnan jihar kano mai ci wanda a ciki aka nuna hoton gwamnan yana karbar wasu kudade da ake zargin cin hanci ne kamar yadda mai alhakin fitar da bidiyon wanda ya kasance dan jarida ne a kasar ya bayyana.

        Bisa fitar wannan bidiyo ne mawaki Aminu Ladan Abubakar (ALA) wanda ya kasance haifaffen jihar kano inda gwamnan ke mulki kuma mawakin jam'iyar gwamnan wato APC ya rera wannan waka da taken, "Mai Dalli Mai Dala Angon Kandala" wadda nake shirin kawo nazarin da na yi akan ta yanzu.....
Reactions
Close Menu