SHAFIN FASIHIYYAH: WAKAR SA'ADATU


Rubutuwa: Musaddam Idriss Musa

1▪️
Ubangijin da yayo Sa'a
      Zan fara roka ban sa'a
2▪️
Na wake mai suna Sa'a 
    Da kai wa baiwar yin sa'a
3▪️
A mata idan ka jiyo Sa'a 
    Ka garzaya don kai sa'a
4▪️
Mace ta musamman ce Sa'a 
     Samun ta sai matukar sa'a
5▪️
Halin kwarai na gun Sa'a 
     Yawan biyayya sai Sa'a
6▪️
Iya kula da 'ya'ya sai Sa'a 
     Tausayi yana a gurin Sa'a
7▪️
Taimakon miji duk sai Sa'a 
     Yawan karatu sai Sa'a 
8▪️
Saki na fuska sai Sa'a 
     Iya kwalliya na gun Sa'a
9▪️
Taku na girma sai Sa'a 
     Sarrafa abinci samo Sa'a 
10▪️
Iya magana na gun Sa'a 
     Taushin kalami sai Sa'a
11▪️
Rashin rawar kai sai Sa'a 
     Rashin riko duk sai Sa'a
12▪️
Yawan uzuri ma sai Sa'a 
     Ba ta son hayaniya sam Sa'a 
13▪️
Idan gida naka ba Sa'a 
     Ka yo ta babba rashin sa'a 
14▪️
Karo mata da sunan Sa'a 
     Ko a 'yar ka sa sunan Sa'a 
15▪️
Da za ka shaida ka yo sa'a 
     Duk a sanadi na samun Sa'a 

(C) Musaddam Idriss Musa
Reactions
Close Menu