"Burina shi ne na auri Jamila Nagudu" - in ji Mubaraq Dakta

Hoton Jaruma Jamila Nagudu


Mubaraq Idris ɗaya ne daga jerin fasihan matasan marubutan zube da kuma fina-finan Hausa. A tattaunarsu da wakilin mu Musaddam Idriss Musa, marubucin ya bayyana masa yadda aka yi ya kamu da son fitacciyar 'yar fim ɗin nan ta Kannywood wato oyayyar Jamila Umar Nagudu wadda har ta kai ga a yanzu babban muradinsa shi ne ya ga ya aure ta. Ga yadda tattaunawar ta su ta kasance;

Mujallar ADABI: Za mu so mu ji tarihin rayuwarka a takaitacce?
Mubaraq: To Jama,a Assalamu alaikum da farko dai suna na Mubaraq Idris Abubakar Wanda aka fi sani da Dr mubaraq, an haifeni a jahar kano karamar hukumar Dala, nayi karatun firamare da sakandire zuwa makarantar gaba da sakandire duk anan garin kano inda a yanzu haka na koma makarantar koyon aikin lafiya dake karamar hukumar kankian jihar Katsina inda naci gaba da karatu na.

Mujallar ADABI: Tsawon wane lokaci ka dauka a harkar rubutu kuma me ya ja hankalinka wajen zama marubuci?
Mubaraq: Gaskiya zan iya cewa na dauki kusan shekaru tara a harkar rubutu. Don tun kan na kammala sakandire na tsinci kaina a cikin harkar kuma ba zan ce ga abinda yaja hankalina na zama marubuci ba saboda shi rubutu kamar yadda ka sani baiwa ce wadda duk yadda kaso ka zamo marubucin in Allah bai kaddara maka ba ba zaka iya ba. Sai dai nace abinda yaja hankalina na fara rubutu bayan na gano cewa zan iya rubutun ko nace da lokaci ya aramin damar rubutun shi ne na dauki rubutu a matsayin wata hanya ta isar da muhimman sako ga al'umma wanda ta hanyar rubutu zaka iya sauya rayuwar wani ko wata da wasu munanan ayyukan ko halayen da suka gagara daukar saiti. To duba da yanayin da muke ciki wasu sun fi daukar darasi da da gane rayuwa ta hanyar nishadantar wa, to hakan ya kara min kaimin zage damtse domin bada gudummawata ta hanyar tura sako na a rubuce da fatan Allah yasa ya isa inda duk zan tura shi, kuma Alhamdulillah zan iya cewa kwalliya na biyan kudin sabulu.

Mujallar ADABI: kai tsaye, a wane rukuni na marubuta za a ajiyeka yanargizo ko marubutan bugaggun littafi?
Mubaraq: Kamar yadda na fada maka a baya cewa fata na shi ne duk ta hanyar da na bi nayi rubutu bukatata sakon ya isa inda na turashi, to don haka bani da bangaren daya da na ware, kawai dai  duk sanda naso aika sakona  na kan zauna na yi nazarin wannan matsala ta ina zan tunkare ta? Shin ta ina sakon zai yi saurin isa ga al'umma.

Mujallar ADABI: Wane littafi ka fara rubutawa shin kana rubutun fina-finai?
Mubaraq: Littafina na farko dana fara tsintar kaina Ina rubutawa shi ne NI NAGA RAYUWA. Ina rubutun Fina finai don zan iya cewa a wannan lokacin ma rubutun film din ke neman kwace ni, don na fi karkata can bangaren a yanzu gaskiya.

Mujallar ADABI: mece ce alakarka da jarumar fim din nan Jamila Nagudu?
Mubaraq: Hmm...... Kyakykyawar alaka ce wadda ta samo asali daga indallahi.

Mujallar ADABI: ana ganin kana jingina kalaman soyayya a shafukanka na sada zumunta ga jarumar shin me ya janyo haka?
Mubaraq: Jingina kalaman soyayya ga jarumar wani sirri ne da zan iya cewa nima ban san dalili ba duk da nafi yarda da cewa hakan baya rasa nasaba da tsintar kaina da nayi ne a kogin Kaunar Jarumar da hakan ya zama silar rufewar idanuwana da ban iya kallon wata mace da kima irin ta so da kauna face ita.
Ina sonta fiye da yadda baka tunani Wanda son da nake mata bana fatan nayiwa ko  matar da zan aura Shi saboda so zai iya sawa na zuba Mata ido taci karen ta babu babbaka ba bari bare kwaba.
Batun soyayya Kuma na lura Kamar hankalin ka yafi karkata kan sanin meke tsakani na da Jarumar, to wannan magana ce ta lokaci Ni dakai da sauran mutane mu jira muga abinda Allah zaiyi.

Mujallar ADABI: mene ne babban burinka a yanzu?
Mubaraq: Burina shi ne na auri Jamila nagudu sannan ko ban yi suna a duniyar rubutu ba sako na ya dinga zuwa inda nake so.


Hoton Mubaraq Idris


Mujallar ADABI: wane kira kake da shi ga 'yan uwanka marubuta da ma masoyanka?
Mubaraq: Yan uwana marubata har kullum kirana shi ne mu hada kawunan mu, mu hada kawunan mu, mu hada kawunan mu, Rayuwar da wuya sai an jure tare da ture duk wasu kalubale a gefe Komai na rayuwa ya gaji haka.
Masoya na ina godiya sosai Allah ya bar kauna  a duk inda suke a fadin Duniya, ina sonku sosai domin duk wanda yace yana sonka ya gama maka komai.
Reactions
Close Menu