Nazarin Waƙar Fim Ɗin "Ƴan Talla 2020" Na Kamfanin Teenstars Studio


Sunan waƙa: 'Yar Talla Daina Kuka
Rubutawa: Sagir Aljazari da Dakta Mubarak
Rerawa: Hafsat Rijiyar Lemo
Kiɗa: Mujahid Duma Studio
Tsayin waƙa: Mintuna 3:40
Jigon waƙa: Illar Talla
Sharhi: Musaddam Idriss Musa
Shekarar sharhi: 2020


WARWARAR JIGO
Waƙar ‘yan talla waƙa ce da ko shakka babu ta zo a daidai lokacin da ake buƙatarta domin waƙar anyi ta ne a lokacin da kusan kowane lungu da saƙo na Najeriya, a cike yake da zarya da kuma zirga-zirgar yara ƙanana masu talla da ma waɗanda shekarunsu suka tasa, musamman ma yara mata waɗanda su ne aka fi gani suna zaga gidaje ko a gefen tituna suna yawon talla. Yayin da waɗanda suka fara zama ‘yan mata kuma wato budurwai ake samun su suna kafa sansani a bakin layuka na unguwanni, tashar hawa motoci, kasuwanni kai wani sa’in ma har da makarantu da kuma asibitoci inda suke sayar da kayan tallan da aka ɗora musu kama daga na dafawa, soyawa, ɗanyen kaya dasauransu. A taƙaice duk wani wajen da ba a rasa samun shi da gungu ko taron mutane na gabatar da al’amuran rayuwa na yau da kullum, to yana da matuƙar wuya a rasa ganin ‘yan talla rakuɓe a wannan waje.

Wannan dalili ne yasa lamarin yawaitar talla na ‘ya‘ya musamman ma mata a Najeriya ya zamo abin jajantawa da kuma tayar da hankulan mutanen da ke da zurfin tunani kan illar hakan da kuma wadanda suka san irin matsalolin dake tattare da tallan, walau ga rayuwar yarinyar da aka ɗora wa tallan ko kuma ga al’ummar ƙasar ma bakiɗaya.

Ba tun yau ne ake samun mutanen da suke nuna hatsarin da ke tattare da ɗorawa ‘ya’ya mata talla ba wanda suka haɗa da matsalolin taɓarɓarewar tarbiyar yara masu tallan, rashin samun ingantacciyar kulawar iyaye, rashin nagartaccen ilimi da ake wa kirari da gishirin rayuwa, yiwuwar fadawar 'yar tallan hanun miyagu wanda sanadiyyar hakan ke samar da matsalolin da suka haɗa da matsalar yi wa 'yan tallan fyaɗe, gurɓata musu tarbiya izuwa aikata munanan dabi’u kamar shaye-shaye, sata dasauransu ga kuma ƙari akan hakan, koyon ƙaryace-ƙaryace da kuma rashin ganin girman na gaba.

Dukkan waɗannan matsaloli idan aka tattaro su aka yi duba za a ga cewa a mataki na farko iyaye ne ke da laifi da suke tura ‘ya‘yayensu ga wannan hanya mai cike da haɗari. Sai dai kuma su ma iyayen hakan na faruwa ne ba tare da son zukatansu ba domin babu iyayen da za su so ganin 'yar su tana gararamba a cikin gari cikin rashin gata in ba don dole ba saboda zafin talauci da ya addabi rayuwarsu ba. Domin wasu iyayen tsofin ma’aikata ne masu karamin muƙami da tsufa ya kamasu kuma babu hanyar samu, wasu leburori ne masu ƙaramar sana’a kama daga faskare, dako da kuma turin ruwa. Ga kuma dubban ɗaruruwa da su kuma ma mabarata ne saboda fama da nakasa da suke wanda hakan ke tilasta musu ɗorawa yaran nasu talla saboda babu wani tallafi na musamman ko tsari da gwamnati da samar wanda zai sauƙaƙa hanyar samuwar abinci ga nakasassu ko marasa ƙarfi dake cikin kasar don gujewa samuwar yara 'yan talla.

Waɗannan da ma wasu da dama su ne irin abubuwan da ita wannan waƙar mai suna ‘Yar Talla Daina Kuka wadda ke cikin shirin fim ɗin "Yan Talla 2020" ta yi nuni akai. Inda a tashin farko waƙar ta fara da suna mana yadda wata ‘yar talla ke bayyana mana takaicinta kan irin tashin da ta yi cikin tsananin duhun jahilci da rashin ilimi a sakamakon rashin sa ta a makaranta da iyayenta suka yi sabili da yadda rayuwarta ta kasance cewa a kullum wuni take a yawon yin talla. Kamar yadda take cewa ;

1. Na tashi ban da gata talla ce dare da rana,
2. Ban san "Alu" ba wannan na sanya rai na kuna,
3. Yin talla ne cikakken ‘yanci gidan ubana,
4. Yau ga shi yadda zan bautawa Rabbi ban sani ba.


'Yar tallan ta cigaba da bayyana mana damuwarta kan yadda makomarta ta kasance mai muni a sakamakon yawon talla da take da kuma yadda ya kasance cewa a gidansu, sam ba a martaba ilimi gami da ba shi muhimmanci ba. Sannan a matsayinta na 'ya, ba ta samu kulawar da ta dace daga iyayenta ba don ingantuwar tarbiyyarta inda take cewa;

5. A gidan mu rayuwa ce ta ba ruwan uba da ‘ya‘ya,
6. Ni ke fita na nemo me mai haɗi da gaya,
7. Ni nayi fice a talle, ilimi ko na yi sanya,
8. Yau ba kuɗi bare ilimin, ba uwa da riba.

A nan za mu ga cewa baitin ƙarshe na yi mana nuni da cewa duk wannan zafin neman na iyayen dake mayar da yaransu ‘yan talla, a ƙarshe ba sa tsinana komai illa kawai bautar da yaran da kuma gurguntar musu da rayuwa. Saboda dalilin daman shi ne samar da abin da gida zai ci na wunin ranar, ba wata ajiya ko ragowar kuɗi da hakan ke samarwa, kamar dai yadda muka gani ta bayyana cewa ita ke da alhakin samar da abincin da ake dafawa a gidan ta hanyar wannan tallen na ta.

9. Dama a ce ayau baba ya kai ni makaranta,
10. Buri na rayuwa na zamo likita ta mata,
11. Zan taimakawa dangi, jama’ar cikin ƙasata,
12. In amfanar da ‘ya‘ya ba jahilar uwa ba.

Har wa yau, waɗannan baituka dake sama sun yi mana nuni kan yadda ita wannan ‘yar tallan take da muradi da kuma mafarkin ganin ita ma ta zamo a jerin yara mata ‘yan uwanta da iyayensu suka sa su a makaranta. A ɓangare guda kuma, ta bayyana mana sha’awarta ko burin da take da shi idan wannan mafarkinta zai tabbata da cewa tana son ganin ta zama cikakkiyar likitar mata ne don taimakawa al’ummar ƙasarta da kuma fahimtar cewa samun ilimin ba a iya nan zai tsaya ba, zai taimaka mata ne har ga wajen tarbiyar yaran da za ta haifa bayan ta yi aure.
       Shakka babu akwai haɗari babba na rashin ceto rayukan yaran dake talla domin gaba su ne waɗanda za su zamo iyaye masu bada tarbiyya ga shugabannin gobe. Wadda ba ta samu tarbiyya da ilimi ba kuma me ake tsammanin za ta koyar wa ɗan da ta haifa?

A baitukan gaba, ga abin da waƙar take cewa;

13. Iyaye ku ƙara himma domin ku sauke nauyi,
14. Haƙƙinmu na wuyanku komai zafi da sanyi,
15. Har gwamnatinmu na yi kira sai ku san abin yi,
16. Masana ku wa’azantar domin samun sawaba.

A nan kuma baitukan waƙar na yi mana nuni ne ga cewa kasancewar mu a matsayi na iyaye wajibinmu ne duk zafin talauci ko mayuwacin halin da muke ciki da mu kwatanta inganta rayuwar ‘ya‘yan da muka haifa ta hanyar ilimantar da su domin hakan haƙƙi ne da ya rataya a kan mu. A ɓangaren gwamnati kuma nan ma akwai kira na musamman gare ta don ta ɗau matakin sauƙaƙawa talakawanta kuma su ma malamai ba ta bar su a baya ba, domin ta nuna buƙatar da su yunƙuro su tunatar da gwamnati haƙƙoƙin jama’arta da suka rataya akanta da kuma iyaye don su fahimci girman haƙƙin tarbiyyar yaransu da ke kan su.


Mai Sharhi: Musaddam Idriss Musa
+2349063064582
Reactions
Close Menu