Rage yawan ƙungiyoyi ne abin da zai kawo haɗin kan marubuta - Zahra Alkali

Zahra Alkali daya ce daga matasan marubuta mata na online dake kan cin ganiyarsu wajen amfani da kafar yanar-gizo suna aika rubuce-r ubucensu. A wannan tattaunawar da ta gudana tsakanin Editan Mujallar Adabi Musaddam Idriss  Musa da marubuciyar wadda take da gogewa ta musamman wajen nazartar al'amuran da suka jibanci marubuta musamman masu amfani da kafar yanar-gizo ta bayyana matakan da take ganin za a dauka wajen samar da hadin kai a tsakanin marubutan Hausa dake rubutun online.
Zahra Alkali (Dideeylov)


Da farko makarantanmu za su so su ji cikakken sunanki da kuma takaitaccen tarihin rayuwarki

Sunana Zahra Abdallah Alkali wadda aka fi sani da Zahra A.A (Dideeylov). Ni 'yar asalin jihar Yobe ce daga karamar hukumar Potiskum. Amma an haife ni ne a nan garin Abuja inda na yi karatuna tun daga Nursery zuwa makarantar gaba da sakandire, inda na karanci fannin addini. Naso karanta fannin shari’a amma Allah bai yi cewa da hakan zan fara ba, sai dai duk da haka ina sa ran karantawa a gaba. A yanzu haka ina bautar kasa a Abuja babban birnin tarayya kuma shekaru na ashirin da hudu a duniya.


Me ya ja hankalinki wajen zama marubuciya?

Na kasance mai tsananin son bincike ta kowane fanni wanda zai kasance na karuwa a gare ni da kuma sauran 'yan'uwana Musulmai, ina iya cewa, rubutu dabi’ata ne, ya shiga cikin jikina, rubutu rayuwa ta ce, domin ba na iya zama ba tare da na yi rubutu ba, ko ya kasance ina rubuta littafi ko nasiha gare mu gaba daya. Saboda haka, babban abin da ya janyo hankalina har na fara rubutu shi ne yadda na ga mutane sun fi ba da mahimmanci ga karatun littafan labarai akan karatun littafan addini, hakan yasa na ga cewa sanya nasiha mai ratsa zuciya ta fannin rubutu babban taimako ne ga al’umma musamman ma ga mata. Saboda mata a yanzu akan su je Islamiyya sun fi ba da hankalinsu kan karatun littafi hakan yasa na ga bada wannan sakon ta fannin rubutu babban taimako ne gare mu baki daya.


Tsawon wane lokaci kika dauka da fara rubutu?

Na fara rubutu tun ina aji biyar a firamare, a duk lokacin da na ji sha’awar yin wani abin, sai in fara rubutu a kan abin da ke kusa da ni, da kuma abinda na fahimta akan wasu abubuwa na yau da kullun. Bayan da na shiga sakandire, sai na fara rubuta irin gajerun labarai masu darasi a ciki, musanman game da yadda na karanci duniyar da kuma yanayin mu'amalar mutane ta yau da kullun. Daga baya kuma sai na fara rubutun littatafi. Ba zan manta ba littafi na farko da na rubuta SAILUBA wanda na yi shi ne a kan mahinmacin uwa a rayuwar dan’adam. A wannan littafin na janyo hankalin masu wulakanta iyayensu musanman ma idan aka ce mahaifiya domin mahaifiya ita ce babban jigo a rayuwar dan’adam.


Zuwa yanzu littattafai nawa kika rubuta sannan kina bugawa ne ko a yanar-gizo kike wallafa su?

Na rubuta littafi za su kai kamar guda goma sha uku. A yanzu iyakarsa a “online” ne. Amma ina da burin wallafawa idan Allah ya yarda.


Waye ubangidanki a harkar rubutu ko?

Adamu Yusuf Indabo shi ne ubangidana a fannin rubutu.


A jerin littattafan da kika rubuta wane ne bakandamiyarki, kuma wane sako yake dauke da shi?

Juyin Lamari domin littafi ne da ya kunshi abubuwa da yawa na zamantakewar rayuwa. Musamman akan rayuwar zamani, da ya kasance mai cike da ababe na son zuciya da kin gaskiya da cin amana ga juna. Sakon da littafin yake aikawa shi ne "matukar mutun bai shuka arziki ba ba zai girbi arzikin ba, shi kuma sharri dan aike ne, duk inda yaje zai dawo, duk wanda ya yi dogaro ga Allah ba zai taba tabewa ba.


A wane irin yanayi ki ka fi jin dadin rubutu?

Yanayi na fushi domin na fi jin dadin fito da abin da yake raina.


Iyaye da dama yanzu na yiwa littafan Hausa kallon cewa hanya ce ta lalata tarbiyar yaran su, mene ne ra’ayinki kan haka?

A gaskiya iyaye da suka dauki littafin hausa a matsayin hakan sun san abin da suka gani shiyasa suka yanke wannan hukunci, sai dai kuma bai kamata a yi mana kud'in goro ba, dan a komai na duniya akwai 6angare mai kyau da mara kyau, matsalar shine wani lokacin bangare mara kyau yana danne mai kyau din dan haka su rinka yi mana kyakyawan zato saboda a samu gyaruwar lamarin.
Abin da zance ga masu rubuta abin da bai dace ba acikin littatafansu shine "Allah ya shirye su, ya kuma ganar dasu, kuma su sani cewa duk abin da muka yi wanda yake dai-dai da akasinsa zamu tsaya a gaban Allah ranar gobe kiyama kuma Allah zai mana hisabi a kai, dan haka tun kafin a kai ga hakan gwara mu fara yi wa kan mu hisabi mu gyara tun Allah yana ara mana lokaci" domin abin ya zama ruwan dare kuma makaranta su suke taimakawa gurin ha6aka irin wannan mumunar abin, domin da basu karantawa kuma basu goyan baya da an samu maslaha a cikin lamarin. 


Wane buri kike son cinma wa a harkar rubutu?

Babban burina na ga rubutuna ya taimaka wajen ilimantarwa a kodayaushe.Ta wace hanya kike ga marubuta musamman mata za su yi amfani da kafar yanar-gizo wajen samun kudi?

Farko dai sai an samu hadin kan marubuta za a samu cigaba yadda ya kamata. Domin rashin goyan bayan wasu a wannan fannin yana taka rawa wajen datse wa wasu samunsu, musanman yanda wasu sukan yi forwarding din rubutun da ya kasance na kudi ba tare da sunyi la'akari da turawan zai iya sa wasu suki saye ba.


Akwai marubuta bugaggun littattafai dake yiwa ku da kuke rubutun yanar-gizo kallon kuna kawo musu koma baya, shin ta ya za ki gamsar da su cewa rubutun yanar-gizo cigaba ne da su ma ya kamata su karba?

A gaskiya rubutu a yanar-gizo ma ya fi saukin kawo kudi, saboda shi rubutu na wallafawa ana bukatan a sanya kudi kafin a wallafa shi, amma online baya bukatar haka. Idan da zasu gwada online process tabbas zasu ji dadinsa. 


Ana yin rubutun yanar-gizo ne kara zube. Ta wace hanya kike ganin za a iya samar da wani tsari da zai sa marubutan kaucewa irin abinda ya faru da marubuta bugaggun littattafai?

Idan marubutan suka cire girman kai da jiji da kai suka zama abu daya haka shi zai saukaka komai, musaman idan shuwagabannin kungiyoyi suka had'a kai gurin ganin sun kawo sauyi ta fannin cigaban marubuta gurin samar da abu daya wanda zai taimaka wa marubuta baki daya. Sannan kuma idan aka rage yawan kungiyoyi aka hade ina ga za a samu maslaha.


Me kika dauki rubutu, sana'a, sa kai, sha'awa, ra'ayi ko kuma abu na nishadi?

Dabi'a wanda ya zamo abin sha'awa ga Dan Adam.
Reactions
Close Menu