An haramta rawa a fina-finan Bollywood


A kasar Indiya gwamnati ta hana yin rawa a masana'antun shirya fina-finan kasar ciki kuwa har da babbar masana'antar shiyar fina-finan nan ta Bollywood wadda ita ce ta biyu a duniya.

Hukuncin hana rawar ya zo ne biyo bayan ba wa jarumai damar komawa bakin fage don cigaba da yin shirin fim tun bayan dakatarwan da aka musu bayan bullowa da kuma yaduwar cutar annobar korona bairos.

Hakan na nufin a fina-finan Bollywood da sauran masana'antun shirya fina-finan kasar India din masu fitowa nan gaba, ba za ana ga wakokin dake bayyana taurari da kuma zugar mutane 'yan rawa a bayansu ba kamar yadda aka saba. Wanda hakan ko shakka babu zai haifar da rashin jin dadi a zukatan masoya fina-finai na kasar.
Reactions
Close Menu