ANA: Rikicin Shugabanci Na Kungiyar Marubutan Najeriya Ta Kasa Na Cigaba Da Ta'azzara


Tun bayan babban taron kungiyar marubutan Najeriya ta kasa mai lakabin ANA a takaice, wanda ya wakana a jihar Enugu inda kungiyar ta shirya gudanar da babban zabenta bayan da  wa'adin tsofin jagororin kungiyar ya cika. Rikicin da ya barke a taron ya haifar da rarrabuwar kai da kuma yamutsi inda a karshe aka tashi baram-baram a taron.

Sai dai kuma tun bayan wannan taron dan takarar neman kujerar shugabancin kungiyar wanda ya fito daga shiyyar arewacin Najeriya, Barr. Abdullahi Wada ya kama jan ragamar ayyukan kungiyar a matsayin sabon rantsattsen shugaba, abinda su kuma 'ya'yan kungiyar musamman wadanda ke bangaren kudancin kasar suka bayyana rashin amincewarsu tare da nisantar da kungiyar daga wannan ikirari na Wada da cewa ya nemi kungiyar da yake shugabanta amma ba ANA ba domin kungiyar ba ta yarda da wancan zaben da aka gudanar ba.

Al'amarin rikicin dai ya yi tsamin da har ta kai ga abin ya koma fadan yanki tsakanin marubutan sashen kudancin Najeriya da kuma marubuta mazauna yankin arewa.
Reactions
Close Menu