Fasihiyyah: Wakar Juyin Zamani Na Nasiru G. Ahmad

JUYIN ZAMANI1. Allah ban hikima basira,
    In yo waka har in rera,
    Kan hali na kasarmu Zara,
    Wadda ake kauna a duba.

2. Ba wata ce Nijeriya ce,
    Wadda diyanta sun yi dace,
    Hadin kayi a zamantakance,
    Ba kyashin wani babu gaba.

3. Ba bambanci na kabila,
    Ko hanyar duba ga kibla,
    Kowa na yin tasa salla,
    Albarkarmu ba tai ragi ba.

4. Shumagabanni na ta kwazo,
    Kowanne a fagensa gwarzo,
    Ba zancen dan wane ya zo,
    Dan talaka ba zai tsaya ba.

5. Kan haka ne aka san kasarmu,
    Kowa na sha'awar zamanmu,
    Yai bunkasa arzikinmu,
    Baki na ta zuwa a tarba.

6. Yau mun wayi gari a tasku,
    Ga mu kukumce babu fakku,
    Ba falala mun rasa hakku,
    Ba kauna sai yada gaba.

7. Yawan sakacin shumagabanni,
    Da son kayi hakki a danni,
    Kabilanci bamban na dini,
    Sun yadu ba domin kure ba.

8, Su ne dalilin hargitsewa,
    Yawan fitina har kangarewa,
    Gwamnati ta kasa iyawa,
    Hakkoki ba ta zam tsare ba.

9. Sai kungiyoyin 'yan ta'adda,
    'Yan sunkuru sunka tad da,
    Muradinsu an kasa mai da,
    Bakin nufinsu na kulla gaba.

10. Bango an ce in ya tsage,
      Jangwala za ya shiga ya toge,
      In ba tsaga ba shi hange,
      Wurin shiga ba zai tsaya ba.

11. Dole mu zam tuhuma ga kanmu,
      Son duniya ne kwadayinmu,
      Ba kishi na kasa jiharmu,
      Ai makiyanmu ba sa wuce ba.

12. Mun sau koyarwa ta dini,
      Kowa na ta fadin kawai ni,
      Sam ba kaunar ikhwani,
      Sai muka zamto babu haiba!

13. Dalili ke nan a'ada'u,
      Sunka nufo mu da dukka da'u,
      Gida da waje mun kasa daf'u.
      Daukar ranmu ba mun tsare ba.

14. Kullum sai fa kisan kiyashi,
      Ga 'yan Arewa muna ta nishi,
      Masu fada a ji sunka bar shi,
      Don ba diyansu ake kashe ba.

15. An bi gidaje an ta kone,
      An taushe dukiyar mutane,
      Duk wani laifi dan Shimal ne,
      Mun ki batun ga muna da raiba.

16. Kawai bayan guzuma ka rabe,
      Don kashe karsana ko a karbe,
      Duk lamura yau ga su kirbe,
      Yau talaka bai san na yi ba.

17. Lallai ne damara mu ja ta,
      Mu dau mataki ya wajabta,
      Don mu kawar da shiri na keta,
      Da an nufo mu ba ma sake ba.

18. Tun farko dai kuri'armu,
      Kar mu saka wa makiyanmu,
      A nan Arewa har kudunmu,
      Mu tabbatar na kwarai muke ba.

19. Sai addu'a saifu gare mu,
      Mu gyara mugayen halinmu,
      Allahu sarki za ya ji mu,
      Duk matsalarmu ba ta tsaya ba.

20. Nasiru G. Ahmad ya tsara,
      Na 'Yan awaki Kano ya rera,
      Don mu kula hali mu gyara,
      Ya Allah ka tsare mu gaba.

Alhamdu lillahi.


Reactions
Close Menu