Kaddamar Da Littafin Rubutun Fim ya Budewa Marubutan Hausa Ido


An dade ana kokarin wayar da kan marubuta masu amfani da harshen gida musamman ma Hausa kan dacewar tafiyar da ayyukan su da zamani duba da yadda ake ta dada samun cigaba a al'amuran sana'o'i da zamantakewar duniya amma abin ya ci tura.

A na cikin wannan hali ne kwatsam sai ga shahararren marubucin littattafai da kuma fina-finan Hausan nan, Malam Bala Anas Babinlata ya kawowa duniyar rubutu wani gagarumin cigaba inda ya shirya taron kaddamar da littafinsa na RUBUTUN FIM a kafar sadarwa na Facebook. 

Taron wanda faruwarsa a yanar-gizo ya kasance biyo bayan dokar hana taro da gwamnatin Najeriya ta sa saboda gujewa yanuwar annobar korona, ya zamo wani tsani da zai haifar da gagarumar cigaba a harkokin rubutun Hausa a fadin Najeriya. 
Reactions
Close Menu