Fasihiyyah: Mai abin fada ai ba shi fada

Daga Nasir Usman Babaye 

Nasir Usman BabayeMAI ABIN FADA AI BA SHI FADA.  XXXX

1 Bisimillah sarkina Ahadun,
Wanda yai yi wake yai yi gyada. 

2. Kai yo salati sarkina, 
Da sallamarsa gun Dahe ka dada. 

3.  Zan yo batu kan 'yanci ne, 
Magana rubutu kar ka kwada. 

4.  Zo ka fadi ni ma na fadi, 
Babu tsegumi kuma babu rada. 


5.  Shi ra'ayi ai riga ne, 
Kowa ya sa yai ta rangwada. 


6.  Cece -kuce ne dole a yi shi, 
Babu zunguri babu tankada. 

7.  Kun san fahimta fuska ce, 
Babu mai guri babu shimfida. 


8.  Wane ya zo saurare shi, 
Ko da da ganga Kar Ka kada. 


9.  Raddi za kai ka iya yi, 
Ba rigima kuma babu fada. 


10.  Abinda na ce shi za ka fadi, 
Kar ka rage kuma kar ka dada. 


11.  Ita ce amanar yin raddi, 
Ba sauye-sauye ba rikida. 


12.  In na gama tsaf to mike, 
Sa ainiya kai ta markada. 


13.  Ware aya ware tsakuwa, 
Kar Ka bar mutane su kwankwada. 


14.  In ka ga ba dai-dai ba fitar, 
Lungu da sako ka sakada. 


15.  Yanci ya sa nai wakar nan, 
Wataran ku ji ta har da kida. 


 16.  Ni ne Nasir dan Usmanu, 
Babaye zan dan kishingida.             16/03/2020.
Nasir Usman Babaye.
Reactions
Close Menu