Nazari Da Sharhin Waƙar Talaka Bawan Allah Na Ibrahim Auwal Abubakar
Sunan Waƙa: Talaka Bawan Allah 
Nau'i: Rubutacciyar Waƙa
Jigon waƙa: ƙuncin rayuwar yau
Manazarci: Musaddam Idriss Musa
Shekarar Sharhi: 2020
Warwarar Jigo

Waƙar “Talaka Bawan Allah” waƙa ce da ta yi duba kan halin rayuwar yau da talakan Najeriya yake ciki na matsi da kuma ƙuncin rayuwa wanda saboda tsananta da al’amarin yayi har an kai ga wani mataki da miliyoyi ba ma dubbanni ba daga cikin talakawan Najeriya a yau na gagara samun ɗan abincin da za su kai zuwa bakin salati. Duk kuwa da girman ƙarfi na tattalin arziƙi da ƙasar take da shi idan aka kwatantata da sauran ƙasashen dake zagaye da ita. Ga kuma a ɓangare guda, tarin ɗaruruwan attajirai da manya-manyan ‘yan kasuwa masu arziƙi da ƙasar take da su waɗanda suka yi shuhura saboda arziƙinsu kuma sunayensu ya zaga duniya ba ma a iya fadin ƙasar kawai ba.

          A lokuta da dama an sha samun wasu na kamuwa da mamaki idan suka ji an yi furucin cewa akwai miliyoyin talakawan dake wuni yunwa, kwana yunwa a Najeriya, wanda hakan kuma ba ya rasa nasaba da rashin kusanci na zama waje ɗaya da talaka da ire-iren waɗannan mutanen suke da shi tunda ko a birane al'ada ce ta masu da shi, warewa kawunansu unguwanni irin nasu na masu hanu da shuni duk da zummar gujewa yin cuɗanya da talaka.

         Babban abin duban shi ne, ba tun yau ba ne aka mayar da rayuwar talakan Najeriya abin Allah sarki duba da yadda aka daɗe a na bautar da talaka a ƙasar musamman ma shuwagabannin dake riƙe da madafan iko na siyasa wanda har ta kai minzalin da a lokutan yawon kamfen yayin gudanar da manyan zaɓuka, akan iya sayen zuciyar talaka har ya kada kuri'a ga ɗan takarar da ba shi da yaƙini kan nagartarsa don kawai an ba shi mudu guda na masara ko shinkafa ko kuma dai don an ba shi takardar kuɗi wadda ba ta fi Naira ɗari biyar zuwa dubu ɗaya ba. Inda daga an kammala zaɓen kuma shikenan sai rayuwar talakan ta sake tsunduma cikin wata sabuwar baƙar wahala akan wadda yake ciki ta baya wanda kuma a ƙarshe hakan shi ya zamo ƙashin bayan samun matsalolin da suka ƙunshi na yawaitar mabarata manyan mata da maza dake bin tituna da gidaje suna yawon roƙon abinda za su ci, samun ƙaruwar yara ƙanana dake yawon talla, yawaitar matasa ‘yan sara-suka,  ƙaruwar matan banza dake zaman kansu da kuma mafi muni ɓullowar ‘yan ta’adda a Najeriya waɗanda ake daɗa cigaba da samu da suka haɗa da ‘yan fashin dake tare hanyoyi, masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga daɗi da masu tada ƙayar baya kamar ƙungiyoyi irinsu Boko Haram.

         Dukkan waɗannan abubuwa ne da ko shakka babu samuwarsu yana da alaƙa da halin matsin rayuwa irin na yau wanda talakan Najeriya ya samu kansa a ciki domin ga zafin talauci ga kuma rashin mai tausaya masa. Inda kuma a bisa shi wannan dalili ne mawaƙi Ibrahim Auwal Abubakar ya rubuta ita wannan waƙar mai suna ‘Talaka Bawan Allah’ don bayyana yadda rayuwar talaka a Najeriya take gudana a ƙarƙashin ƙuncin talauci da rashin madafa inda a tashin farko bayan buɗewa da ambaton Ubangiji, mawaƙin ya fara da bayyana mana irin kallo da kuma matsayin da talakan Najeriya yake da shi a wajen shugabanni, 'yan siyasa da kuma attajirai inda yake cewa;

2.

Mai kudi burin shi ya mallakeka,

Shugaba burin sa ya mulkeka,

Buri na ɗan kasuwa ya cuceka,

Duk da talaucin da ya addabeka,

Ba ka jin shi daɗi sam ko sukuni.

Waɗannan baitoci ne da ko shakka babu suka fito a fili ƙarara suka bayyana mana matsayin talakan Najeriya da cewa mutum ne marar cikakken 'yanci ko ma a ce mutum ne wanda yake rayuwar ƙangin bauta ba tare da ya samu ko da mutum guda daga na sama da shi ba da zai tausayawa halin ƙuncin talauci da kuma rashin jin daɗin rayuwar da yake ciki ba. Baitocin sun kuma hasko mana ɓoyayyar ɗabi'ar 'yan siyasar Najeriya da cewa, babban ƙudirin dake gabansu shi ne a ce sun ɗare kan madafan iko, da zaran kuma sun yi nasarar samun hakan to fa burinsu ya gama cika, ba su da wani tunani akan talaka domin manufar hawa kujerar daman ba a kansa aka ginata ba. Haka su ma masu arziƙi a nasu ɓangaren, buƙatarsu a ce sun mayar da talaka boyi-boyinsu domin sun ɗauki talaka ne a matsayin da yake kwatankwacin na motar da ake safarar kaya da ita, ba sa nemansa sai wata buƙata ta aiki mai wahala ta taso musu wadda ke buƙatar aikatuwar jiki kafin su iya ba shi kwandalar da za ga kashe masa yunwarsa ta lokaci guda. Haka kuma su ma 'yan kasuwa, ba su da mutumin da suke burin gallazawa kamar talaka, wanda hakan kuwa shi ya daɗa ƙara tsanantar mummunan yanayi na halin ni 'ya sun da talakan Najeriya yake ciki a yau na rashin ƙarfin ciyar da kansa.

A baitoci na gaba kuma, ga abinda mawaƙin yake cewa;

3.

Kowa ma kai yake cin moriya,

Ko doka ma kai taka bibiya,

Inko kaƙi ka zam mai biyayya,

Hukunci ka ka sha ba ƙyaliya,

Kan shi laifi ko ɗan ƙanƙani.

Sanannen abu ne cewa a Najeriya, babu wanda ake zartarwa doka nan take kamar talakan dake faman neman na cin yau da gobe. Kotuna da gidajen yari dake faɗin ƙasar kaf cike suke da talakawa masu manya da kananan laifi. Wasun ma an kai su an kulle ne saboda sun saci mudu na hatsin da za su kai gida ga iyalansu don su samu abinda za a ci, wasun kuma matasa ne da aka same su da laifin shan kayan maye, amma yana da matuƙar wuya a tarar da wani gawurtaccen ɗan siyasar da yayi sama da faɗi da kuɗin al'ummarsa ko kuma ɗan kasuwan dake shigo da haramtattun ƙwayoyi ko wani babban attajirin da aka gano yana aiwatar da wata mummunar halayya kamar fyaɗe ga ƙananan yara da makamantansu da cewa kotu tasa a ɗaure su a irin waɗannan gidaje. Talakan dai shi ne wanda doka ke bi ta kansa kamar yadda mawaƙin ya ambata.

A gaba ga abinda waƙar ta cigaba da bayyanawa a cikin dango na 4 da na 6;

4.

Ɗan abincin ma fa da za ka ci,

Wataran sai ya zamto rikkici,

Daman wasu ba sa so ka ci,

So suke kai bara kafin ka ci,

Tausaya maka sai dai mumini.6.

Tallafin da kake so ba hali,

Ko abincin ka sai mara fassali,

Ba ka samun koda dankali,

Bar batun ma kayan kyalkyali,

Kaicon talakan ga na zamani.Waɗannan wasu jerin baitukan ne dake ƙara nuni kan bayanin dake can a sama cewa talakan Najeriya na cikin matsanancin halin da komai ƙanƙantar darajar abinci bar ma irin nau'ikan abincin da ake samu a gidajen masu wadata gagararsa yake. Kuma waɗanda suke da ikon tallafa masa ɗin, sun ja gefe tare da kawar da kai saboda fatansu kawai shi ne a ce ga talaka nan na shan wahala. Ƙalilan ne masu matuƙar ƙarfin imanin dake iya taimakawa talakan a lokacin da yake mayuwacin hali na tsananin buƙata kamar yadda baitin ƙarshe ya nuna.

7.

Kalli min talakawan nan iyaye,

Rayuwar su kan sa har nai hawaye,

Sanadiyyar rashin yin waiwaye,

Ga muhallai na su da kewaye,

Wanda aiki ne na shuwagabanni.A baitin dake sama mawaƙin ya bayyana alhaninsa da kuma yadda yake matukar tausayawa talakawan da suka mallaki iyali saboda sanin irin halin matsin da rayuwarsu take ciki tare kuma da jajanta yadda shugabanni suka wofintar da al'amuran sauƙaƙa rayuwar  talakawan da suke jagoranta.8.

Shi ai talauci ba bauta ba ne,

Yau idan kai aka kira da kira wane,

Gobe za ka mace haka za'a bisne,

Ba musulmi sam kuma babu arne,

Ayyukan da ka yo can ka fa gani.A nan mawakin ya yi ƙoƙarin nusar da shugabanni cewa dukkan abinda suka shuka walau na alheri ne ko kuma sharri, za su tarar da shi tun a ƙabarinsu tunda duniya ba waje ne da ake dauwama ba wanda kuma hakan zai faru ne ba tare da la'akari da koma wane irin addini shugaban nan ke bi ba. Har wayau ya gargaɗi waɗanda giyar mulki da kuma dukiya ke zuga da cewa su tuna ita duniyar juyi-juyi ce, idan yau kai ake ambato gobe waninka ne.

     Da wannan nake sake nusar da manyan jagorori da attajiran ƙasa da ma gwamnati da cewa a duk lokacin da suka yunƙuro don magance ire-iren matsalolin da Najeriya take ciki a yau, to ka da suna mantawa da cewa bada himmarsu wajen ƙoƙarin ganin an daƙile kaso mai yawa na talaucin da yayi ƙatutu a tsakanin al’ummar ƙasar na daga jerin manyan abubuwan da za su kai ga nasarar samun wanzuwar zaman lafiya da kuma al'umma nagartacciya irin wadda ake buƙata.Mai Sharhi: Musaddam Idriss Musa

Lambar waya: +2349063064582Imel: realmusaddam@gmail.com 
Reactions
Close Menu