Kannywood: Shin da gaske Ali Nuhu ya ƙara aure a ɓoye?

An shafe aƙalla kwanaki huɗu da fara yaɗa jita-jitar cewa shahararren jarumin wasan Hausan nan mamallakin kamfanin shirya fina-finan da ake kira fa suna FKD productions wato jarumi Ali Nuhu da ake wa laƙabi da sarki ya sake aure na biyu wanda hakan ya janyo hankulan mutane da dama musammman masoyansa duba da cewa lamarin ya zo ne kwatsam, a bazata.Jita-jitar wadda musabbabin samuwarta ya kasance biyo bayan bayyanar wasu hotuna da jarumin ya ɗauka tare da wata da ba a san ko wacece ba inda kuma hakan yasa masu wancan batu suka yi zargin cewa akwai yiwuwar wadda yake shirin aura ne matsayin mata ta biyu duba da rubutun da ya yi inda yake cewa "save the date" ma'ana kada a manta ranar, shi ne abin da ya kawo hauhawar batun har ma ta kai ga janyowar cecekucen da ake yi da kuma samuwar tashoshin labarai na YouTube dake yaɗa cewar jarumin ya ƙara aure ne.

Sai dai kuma Ali Nuhu ɗin ya ƙaryata wannan batu tare da yin ƙarin haske dangane da hotunan wanda a baya ya yi ta ɗora su a shafinsa na sada zumunta ba tare da cikakken bayani ba wanda kuma yayi hakan ne daman don ya ja hankalin jama'a kan hotunan da zummar ganin abin da mutane kan iya cewa akan su.

 Ga dai abin da jarumin ya fito ya bayyana "Bayani akan hotunan Aure da ke yawo a shafukan sada zumunta, wadannan hotuna ne na shirin GIDAN BIKI na @mlmibrahimsharukhan da muka ɗauka ba hotunan aure na ba ne. Da fatan za ku zo booking din bukukuwanku a IZEEMA EVENT Centre da ke Titin Magajin Rumfa a Kano. muna godiya."
Reactions
Close Menu