An Sanar Da Sakamakon Gasar Marubutan Hausa Ta Cibiyar Nazari Na Aliyu Mohammed Zagaye Na FarkoDaga Musaddam Idriss Musa


Wata sanarwa da ta fito a makon da ya gabata biyo bayan shiga gasar marubutan Hausa na shekarar 2020 wanda cibiyar Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute, Kaduna ke shiryawa duk shekara ta bayyana sakamakon zagayen  farko na tantance labaran da aka shigar da su a gasar ta banana.

Da yake bada kiyasi kan adadin labaran da aka shiga gasar da su a bana, jami'in kula da gasar Malam Muhammed Isah Suleiman ya bayyana cewa, "gabaki daya, mun sami jimullar labarai guda talatin da takwas (38) ne wadanda marubuta mabanbanta suka turo domin shiga gasar."

Dangane ga sha'anin alkalin gasar kuma jami'in ya dora da cewa, "Alkalan gasar sun yi nazari mai tsawo da daukan lokaci wajen dubawa da karanta tsakuren shafi goma na labaran da kuka turo. Bisa ga sakamakon da alkalan gasar suka fitar, mun fidda labarai guda goma sha biyar (15)".
"Su wadannan labarai sune suka cancanta dasu tura mana da cikakkun labaran su kafin karfe 12 na daren ranar 15 ga watan Augusta, 2020 domin Alkalan gasar su samu daman fidda zakarun gasar na shekarar 2020 a karshen watan Satumba, 2020". In ji jami'in
Labaran dai da suka haye zagaye na farkon sun hada da:
1. YINI SITTIN DA ƊAYA
2. GUDUNMAWARMU
3. DAMA SUN FADA
4. SANADIYYA
5. DAN WAYE
6. AIKA AIKA
7. KADDARAR ZAWARCI
8. YAN ZAMANI
9. A DALILIN KWARONA VIRUS
10. KA KI NAKA
11. HALIMATU
12. ILLAR ALMAJIRANCI
13. KANA TAKA ALLAH NA TASA
14. BURGAMI A HAMNUN BERAYE
15. WAYE MAKASHINTA

A karshe jami'in ya mika sakon godiyar sa da kuma fatan alheri ga daukacin marubutan da suka samu damar shiga gasar ta bana, "Mun gode da kokarin ku na shiga gasar marubutan Hausa ta Aliyu Mohammed Research Library, Gusau Institute, Kaduna. Kuma muna fatan zaku bada himma wajen shiga gasar a shekara mai zuwa, idan Allah ya kaimu, domin neman samun nasara. Muna muku fatan Alkhairi wajen shiga gasan a nan gaba, idan Allah ya bada ikon hakan".
Reactions
Close Menu