Dalilin sallamar Aishwarya daga asibiti tare da riƙe Amitabh da matarsa

Jarumar fina-finan na Indiya, kuma wacce ta taba samun lambar yabo a sarauniyar kyau ta duniya, sun bar asibitin Nanavati ne tare da 'yarta a safiyar ranar Litinin.


Aishwarya Rai Bachchan

An sallami Aishwarya Rai Bachchan da 'yarta Aaradhya daga asibiti bayan an yi musu gwajin korona an tabbatar sun warke.

Mijinta Abhishek Bachchan, ya wallafa sakon godiya a shafinsa na tuwita inda yake gode wa 'yan uwa da abokan arziki saboda addu'ar da aka yi musu shi da iyalansa da ma mahaifinsa a kan samun sauki daga cutar korona da suka kamu da ita.
Abishekh Bachchan da matarsa Aishwarya Rai Bachchan da kuma 'yarsu AaradhyaSai dai Abishekh da mahaifinsa Amitabh Bachchan har yanzu suna asibitin inda suke karbar magani.

Amitabh Bachchan: Shahararren ɗan Bollywood ya kamu da koronaCoronavirus a India: Indiyawa na yi wa Amitabh addu'ar samun sauki

A farkon watan da muke ciki ne aka kwantar da su a asibiti bayan an yi musu gwaji an ga suna dauke da cutar korona.

Aishwarya da 'yarta sun godewa jama'a saboda addu'oin da aka yi musu, kuma tuni suka koma gida.

Jaya Bachchan (daga hagu), Amitabh Bachchan, tare da ɗansu Abisheik Bachchan da kuma jikarsu Aaradhya tare da surukarsu Aishwarya Rai Bachchan
Masoyan Amitabh da dansa a ciki da wajen Indiya na ci gaba da yi musu addu'a a kan samun sauki.

Amitabh mai shekara 77, fitaccen jarumi ne a Bollywood, kuma ya yi suna a duniya baki daya.

A ranar 12 ga watan Yuli ne ya wallafa a shafinsa na tuwita cewa, ya kamu da cutar korona.

Jaya Bachchan, matar Amitabh wadda ita ma jaruma ce ba ta kamu da cutar ba bayan da gwaji ya nuna hakan.

Indiya dai ita ce kasa ta uku a yawan wadanda ke da cutar korona a duniya.

A ranar Litinin, an samu sabbin mutum 50,000 da suka kamu da cutar korona a cikin sa'a 24 a Indiya, abin da ya kai adadin wadanda suka kamu da cutar miliyan daya da dubu dari hudu.
Reactions
Close Menu