Sabi kuma manyan litattafan Hausa guda 5 da zaku so karantawa a yayin da suke shirin shiga kasuwa

Daga Musaddam Idriss Musa 

1. Wukar Fawa: littafi ne na gawurtacciyar marubuciyar Hausan nan Hajiya Hassana Abdullahi  Hunkuyi wadda aka dade ana damawa da ita tsawon shekaru a duniyar rubutu. Salon dake dauke da zubin labarin da kuma yadda marubuciyar ta kulla zarensa gami da warware shi cikin gwanintar iya sarrafa alkalami kadai ya isa sanya makaranta fantsama izuwa shagunan sayar littafai don yiwa kansu tanadin kasaitaccen littafin nata wato Wukar Fawa wanda ya samu kyakkyawan aiki daga kamfanin Maizar Publishers  kama daga dab'i da kuma tsarin bangon littafin.

2. Matafiyi (The Traveller): Kayataccen littafi ne da yazo da sabon tsari da kuma zubin labari da yake mai kama hankali da kuma caja kwakwalwa bisa yadda marubucin yayi amfani da basira da kuma kwararewar iya sarrafa alkalami ta hanyar hado rayuwar jiya da kuma yau ya dinke su a waje guda. Littafin wanda marubuci Musaddam Idriss Musa ya rubuta shi, yana dauke da yarukan kabilun arewacin Najeriya har guda 30 a cikinsa wanda hakan yana daga cikin abubuwan da suka mayar da littafin ya kasance na musamman kuma gagarabadau a jerin littafan Hausa. Shi dai wannan kasungumin littafin wanda kamfanin dab'i na Ndaláá-Dookun Publishers suka yi aikinsa na dauke da zubi da kuma tsari mai matukar kama zuciya r masu karatu gami da sanya musu shauki, alhini da kuma jefa zukatan a cikin rudani da kuma fargabar abinda kan iya faruwa a gaba har sai sun kai ga karshen littafin. Wannan dalili yasa dumbin makaranta suka  zamo cikin kaguwar jiran shigar shi kasuwa.


3. Tallafi: littafi ne da hazikar marubuciyar nan wato Malama Zainab Abubakar Kangama ta wallafa bayan wallafa littattafanta da suka hada da Garkuwata, Nima 'Ya Ce kashi na 1, 2, 3 da kuma na 4. Inda kuma a yanzu shi wannan littafi nata mai suna Tallafi wanda ya samu kwarewar aiki daga shahararen kamfanin dab'in da ba shi da tsara wato AGF Graphics Fagge dab yake da shiga kasuwa. 

4. Bikon So: kayataccen labari ne da marubuci Aminullahi Lawan (Elder) ya rubuta cikin nuna gwanintarsa da kuma kwarewar da yake da ita a fannin so. Litttafin wanda ya ginu akan jigon soyayya na dauke da tarin muhimman darusa na zamantakewar masoya. Shakka babu idan akwai wadanda ke neman karawa soyayyarsu karfi ko kuma neman yaye wata matsala tasu dake da alaka da soyayya, littafin Bikon So na dauke da dukkan warakar matsalolinsu.Reactions
Close Menu