Abdul-Yasir Garba: Dan Arewa Da Ya Ci Gasar Duniya

 Abdulyasir ya zama daya daga cikin mutane 6 da aka tantance,...

Daga Yahaya S. Kaya


Abdulyasir Garba matashi ne dake zaune a Birnin Kano dake arewacin Nigeria, shi ne matashin da yazo na uku a cikin masu yin taimako a duniya ( 3rd World Youngest Humanitarian ). Sannan shi ne matashin da ya fara cin gasar a gabadaya fadin Najeriya da tahirinta, bugu da kari wannan kungiyar "World Peace International" tayi matukar jinjinawa da yabawa wannan matashin bisa ganin karancin shekarun shi da ba su haure shekaru 18 ba, amma ya zama jijirtacce wajen ganin ba shi da wani tunani da ya wuce ya taimakawa al'ummar da suke neman taimako. 


Akalla matasa sama da 238 daga kasashe 39 ke neman aikin Babbar kungiyar  Matasa ta Duniya, Abdulyasir ya zama daya daga cikin mutane 6 da aka tantance, sannan cikin ikon Allah ya zama na 3 a cikin mutane 3 da sukaci Interview. Na farko wata matashiya ce daga kasar Indonisiya mai suna  Desi Yunsari, sai na biyu matashi daga kasar Afghanista Sohrab Samin.

Reactions
Close Menu