"Ban sani ba ko a nan gaba zan fara siyasa" - Jaruma Rahama Sadau

duk abin da na yi duk kankantarsa mutane sai sun yi magana a kai.


Rahama Sadau


Fitacciyar jarumar nan ta masana’antar Kannywood, Rahama Sadau ta ce dukda cewa a yanzu bata da ra’ayin siyasa ba ta sani ba ko hankalinta zai karkata ga hakan zuwa nan gaba.

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da ake cigaba da zaman killace kai saboda annobar cutar korona da ta mamaye duniya a wata hira ta musamman da kamfanin dillancin labarai na BBC Hausa suka fitar biyo bayan samun damar zantawa da jaruma Rahama din a shafin Instagram.

A cewar jarumar ita ba ta siyasa, ta ce ita 'yar Najeriya ce kamar kowa duk da cewa ba ta da tabbacin ko a gaba za ta yi ra’ayin tsunduma cikin harkokin siyasar kamar yadda ta bayyana, “Ban sani ba ko a nan gaba zan fara siyasa, amma a yanzu a'a,” in ji ta.

Dangane da yadda ta tsinci kanta a wannan hali da ake ciki na kulle din kuwa, jarumar cewa ta yi, “Lokacin kullen sai dai mutum ya yi ta yin kame-make. Ka yi karatu ya ishe ka, ka yi kallo ya ishe ka, ka yi chatting ya ishe ka," in ji ta.
Ta ce kullen ne ya sa ba a jin duriyarta kwana biyu. Har ila yau Rahama ta ce ta ji babu dadi a lokacin kuma ta ji kamar za ta mutu.

         Jarumar ta kuma bayyana damuwarta da cewa, sana'arsu tana bukatar tara jama'a kuma yanzu an hana yin hakan saboda wannan annoba inda a bisa wannan dalili a cewarta, korana ta fi shafar su fiye da kowa.

           Rahama dai a kwanakin baya-bayan nan ta kammala karatunta na digiri inda ta karanci fannin Kimiyyar Tattalin Kayan Albarkatun Dan Adam a kasar Syprus. Ta ce karatun ne ya sa ba ta iya ci gaba da harkokin fina-finanta ba gadan-gadan.

           Daga abubuwa na musamman da jarumar ta kwarai akai kuwa kamar yadda ta ce, tana iya magana da harshuna har guda uku Hausa, Turancin Inglishi da kuma Indiyanci.

            Da take amsa tambaya kan abin da ya shafi zamantakewar rayuwarta kuwa musamman kan abin da ya shafi alakarta da masoyanta Rahama ta ce mutane da dama suna son ta da aure, 
yawanci sai dai na yi dariya ko kuma na ce na gode,
 In ji ta. Sai dai ta ce ita ba ta da wani saurayi a Kannywood a halin yanzu.        Dangane da yadda take yawan jawo ce-ce-ku-ce, Rahama ta ce hakan yana faruwa ne saboda yadda ‘‘ duk abin da na yi duk kankantarsa mutane sai sun yi magana a kai.’’ 
Rahama ta ce hakan ba ya sa ta damuwa "saboda mafiyawanci ban cika gani ba.’’

Idan na ga mutum daya ya fara magana mara dadi, fita nake yi gaba daya. Ba na ganin sauran, sai komai ya yi sauki. Wani lokacin kuma ina gani ban zan iya sa abu ya dame ni ba, abin da bai kai ya kawo ba.
 a cewarta.
Reactions
Close Menu