"Yana dakyau a na tantance littafi kafin ya fito kasuwa" - marubuciya Rabi Garba Tela


sannan kuma yana da kyau a ce a na tantance littafi kafin ya fito kasuwa tare da kafa doka akan yawan adadin littattafan da marubuci zai rubuta a shekara.

Hajiya Rabi Garba Tela na daga jerin manyan marubutan Hausa mata na wannan zamani da aka daɗe a na damawa da su a harkar adabi inda sunanta ya karaɗe lungu da saƙo na arewacin Najeriya kai har ma da ƙasashe maƙota. Sai dai kuma an kwashi tsawon lokaci rabon da aji ɗuriyar marubuciyar wanda hakan ya janyo cecekuce a tsakanin makaranta littattafan Hausa musamman masoyanta inda wasu ke raɗe-raɗin cewa marubuciyar ta yi batan dabo ne a sakamakon daina rubutu da ta yi. A bisa wannan dalili ne wakilin Mujallar ADABI, Musaddam Idriss Musa yin tattaki musamman don zantawa da marubuciyar inda ta feɗe masa biri har wutsiya kama daga tarihin rayuwarta da yadda aka yi ta zama marubuciya izuwa amsar tambayarku ta shin har yanzu tana rubutun littafai ne ko kuwa ta daina kamar yadda ake ta yaɗa jita-jita? Ga yadda hirar tasu ta kasance:


Hajiya Rabi Garba Tela


Da farko za mu so ki faɗawa makarantanmu tarihin rayuwarki a taƙaice. Shin wace ce Hajiya Rabi Garba Tela?


RGT: Ni dai sunana Rabi Garba Tela, an haife ni a garin Potiskum shekarar 1983 cikin ƙaramar hukumar Nangere tun a lokacin da Yobe take ƙarƙashin jihar Borno. Na yi makarantar firamare ɗina a Buraima dake nan cikin garin Potiskum bayan na kammala na tafi makarantar gaba da firamare a FGGC Potiskum. A shekarar da na gama nayi aure wanda a halin yanzu ina da yara biyu maza. A shekarar 2008 na koma makaranta inda nayi diploma a bangaren Arabic.


Kina a sahun manyan marubutan Hausa mata da ake ji da su a Najeriya, shin tun yaushe kika fara rubutu kuma me ya ja hankalinki wajen zama marubuciya?

RGT: Na fara rubutu tun ina JSS 3 a shekarar 1997 sai dai ban samu damar bugawa ba saboda a lokacin karatu ne a gabana. Bayan na kammala karatun sakandire nayi aure har na haifi yarona na farko, sai sha'awar rubutun ya sake bijiromin. Nan take na ɗauki alƙalami da takarda na fara rubutu. Abin da ya janyo hankalina na ji ina sha'awar yin rubutu kuwa shi ne na kasance makaranciyar littafan Hausa tun ina aji huɗu na furamare. Na karanta littafa da dama kamar su ‘Inda So Da Ƙauna’, ‘Kukan Kurciya Jawabi Ne’, ‘So Marurun Zuciya’ da sauransu. To tun a wannan lokacin marubutan suna burge ni ta yadda suke ƙoƙari wajen isar da saƙo tare da wayar da kan jama'a ta hanyar rubutu. A sanda na samu kaina da karatun littafan Bilkisu Ahmad Funtuwa sai na gane cewa nima ya kamata na fara rubutu saboda abubuwan da na ke ji ko gani suna faruwa a zamantakewar al'umma, wanda a ganina ta hanyar rubutu ne zan iya isar da saƙon da na ke so yaje wa al'umma duba da yadda rayuwar zamantakewar aure ta lalace, rashin zaman lafiya yayi ƙaranci a tsakanin ma'aurata tare da fitintinu masu yawa a cikin auren da wanda ya kamata da wanda bai kamata ba, haƙuri yayi ƙaranci musamman a wajenmu mata da kuma jahilci da rashin abin yi wannan shi ne babban dalilina na fara yin rubutu.


Kawo yanzu da kika shafe waɗannan shekaru kina rubutu, aƙalla littafa nawa kika rubuta kuma ya sunayensu suke?


RGT: Aƙalla na rubuta littattafai bakwai. Littafina na farko shi ne Duniyar So, sai kuma Zama Da Surukai, Rashin Dace Da Miji, Kishiyata Ce, Nayi Nadama, Uwar Goyo da kuma kudurar Allah.


A na iya cewa an daɗe rabon da aji ɗuriyarki ko wani sabon littafi naki ba wanda hakan yasa wasu ke tunanin ko kin daina rubutu ne, shin ya abin yake?


RGT: Haƙiƙa na daɗe ban yi rubutu ba sakamakon komawa makaranta da nayi, amma ba wai na bar rubutu ba ne yanzu ne ma nake jin nishaɗin yin rubutun don akwai tarin littattafan dana ke son rubutawa a yanzun, don haka ina nan daram riƙe da alkalamina har gobe bi izinillahi ta'ala.


Da zaran an ambaci sunanki aƙasarin mutane musamman masu karanta littattafanki na yi miki kallon cewa 'yar garin Kaduna ce ke ko kuma jihar Kano. Me za kice kan hakan?


RGT: To ni dai haifaffiyar garin Potiskum ce wanda a yanzu take ƙarƙashin jihar Yobe kuma ban taɓa fita zuwa wani gari da niyyar zama ba sai dai naje don ziyara. A garin Potiskum aka haife ni anan nayi makaranta anan nayi aure, kai na takaice maka labari har yanzu ina zaune ne a garin Potiskum kuma wannan jita-jita da ake cewa ni 'yar Kaduna ce ko Kano ba gaskiya ba ne ban san ma yaya aka yi aka yaɗa ta ba.
Duba da daɗewar da kika yi ana damawa dake a harkokin rubutu, shin waɗanne irin ƙalubale kika fuskanta a yayin da kike ƙoƙarin zama marubuciya da kuma bayan nasarar da kika samu bayan kaiwa ga wannan mataki da kike a yanzu?


RGT: Rayuwa tana da ƙalubale masu yawa musamman ma idan a kace Allah ya ɗaukaka mutum. Na fuskanci ƙalubale a harkar rubutu a wajen mutane masu yawa harda makusantana, A farkon fara rubutuna mahaifina baya so don a ganinsa na ɓullo da wata hanya ce wacce za ta hana ni karatu, an kira ni da maƙaryaciya wai ina rubuta labarin ƙarya, wasu mutanen suna min kallon mai ɓata tarbiya ta Islama da kuma ta zamantakewa, abubuwa da dama sun faru kafin daga baya Allah ya kawomin sauƙinsu tare da ɗaukaka ni a idon jama'a. Da ma kuma Allah yana cewa, ‘duk wanda ya dogara da Allah, to Allah ya isar masa’.


Me yake ci miki tuwo a ƙwarya, dangane da harkokin rubutu?


RGT: Abin da yake cimin tuwo a kwarya kuma yake damuna a zuciya a game da harkar rubutu shi ne rashin ci gaba. Har yanzu akwai naƙasu a harkar rubutu duba da yadda ƙasashen ƙetare suka cigaba, mu ma a nan Najeriya muna da manya manyan marubuta masu baiwar rubutu amma har yanzu rubutun bai cigaba ba wanda hatta harkar fim ma tafi shi cigaba.


Ko kin gamsu da tsarin da ake tafiyar da harkokin rubutun Hausa a yanzu musamman ma yadda ake gudanar da kasuwancin littattafai?


RGT: A gaskiya ban gamsu ba domin wannan tsarin ya kawo mana koma baya a harkar rubutu tare da samun naƙasu mai girma acikin harkar ta yadda kasuwar littattafai ta fadi ƙasa warwas, littafi ya koma ba shi da daraja kamar na da.


Wasu kan yiwa marubutan Hausa kallon mutanen da kansu ba a haɗe yake ba, shin me za kice kan wannan?


RGT: Ba ni da ta cewa kan wannan batu domin ban san komai a game da haɗin kan marubuta ko kuma akasin hakan ba.


Shin kin taɓa shiga wata ƙungiya ta marubuta ko halartar wani taro da aka yi na masu harkar rubutu?


RGT: Eh na taɓa shiga ƙungiya wadda ake yi mata laƙabi da Potiskum Writers Association (POWA), ƙungiya ce ta marubutan garin Potiskum, inda a yanzu kuma muka haɗa ƙarfi da ƙarfe muka sake buɗe wata ƙungiyar mai suna Yobe Writers Association (YOWA). Na taɓa halartar taron marubuta na cikin gida da na waje, ma'ana namu na Potiskum da kuma na sauran jihohi.


Babbar marubuciya kamarki wadda ta haɗu da ƙalubale a harkar rubutu, ba za kuma a rasata da tarin wasu nasarorin ba, kawo yanzu waɗanne abubuwa ne kike kallo a matsayin nasarorin da kika samu a harkar rubutu?


RGT: Alhamdulillahi! Na samu nasarori masu tarin yawa a ɓangaren harkar rubutu; duniya ta san da ni suna na ya shiga cikin jerin marubutan Najeriya, ina daga sahun farko a cikin manyan marubutan da suke jihata, na samu tarin kyaututtuka daga gwamnatin jihata da kuma wajen mutanan da suke karanta littattafaina. Karramawar da na samu tare da lambar yabo daga ofishin kwamishinan ilimi na jihar Yobe ita ce nasara mafi girma da na samu a harkar rubutu, sannan kuma na cimma burina wato saƙon da nake so ya isa zuwa ga mutane ya isa.


Wane kira kike da shi ga daukacin makaranta littattafan Hausa da sauran jama’ar da harkar rubutu ta shafa?


RGT: Ina mai jawo hankalin masu karatu akan su dinga yiwa marubuci uzuri dangane da yadda suka riski rubutunsa domin shi Ɗan Adam ajizi ne yakan iya yin kuskure ko tuntuɓen harshe, sannan kuma a ɓangarenmu marubuta yana da kyau mu dinga dogon tunani tare da nazari mai zurfi dangane da abin da zamu dinga rubutawa a mutane, marubuta malamai ne waɗanda jama'a suke ilmantuwa ta hanyar alƙalumansu tare da yin koyi da abin da suka karanta. Ta hanyar rubutu al'umma zasu gyaru haka nan ta hanyar rubutu al'umma zasu iya lalacewa domin kuwa alƙalami ya fi takobi. Lura da hakan shi ne nake so nayi amfani da wannan damar wajen jawo hankulanmu akan mu dinga takatsantsan a game da abin da zamu rubuta, mu tuna cewa Allah zai tambaye mu a game da abin da muke rubutawa, sannan kuma yana da kyau a ce ana tantance littafi kafin ya fito kasuwa tare da kafa doka akan yawan adadin littafin da marubuci zai rubuta ashekara.


Ko akwai wani albishir da kike da shi ga masoya da makaranta litattafan ki?

RGT: Ina yiwa masoyana albishir da cewa insha Allahu nan ba da daɗewa ba zan fitar da sabbin littattafaina, ina kuma miƙa ɗumbin godiyata ga ɗaukacin masoyana waɗanda na sani da wanda ban sansu ba, nagode sosai a bisa ƙaunar da suke nuna min.


A ƙarshe, wane kira kike da shi ga sauran ‘yan uwanki masu rubutun Hausa?

RGT: Ina kira ga marubuta 'yan uwana da mu yi riƙo da gaskiya tare da amana kuma mu zamanto tsintsiya maɗaurinki ɗaya, tare da yiwa manyanmu biyayya, Allah ya taimakemu ya kuma buɗe mana ƙwa ƙwalenmu ta yadda za mu samu damar isar da saƙonninmu zuwa ga mutane nagode sosai.
Reactions
Close Menu