JISWA: Kungiyar Marubutan Jigawa Za Ta Gudanar Da Babban Taro A Birniwa


Gamayyar kungiyar marubutan jihar Jigawa da ake kira Jigawa State Writers Association wato 'JISWA' a takaice ta shirya gudanar da gagarumin taronta na bada kyautuka da kuma karramawa a karo na biyar wanda zai gudana a ranar Asabar mai zuwa 2020.


          Fasalin taron dai wanda zai gudana a garin Birniwa na jihar Jigawa ya kunshi karrama jerin  wasu manyan mutane daga garin Birniwan wadanda suka ba wa ilimi gudummawa da kuma wasu kungiyoyin dake aikin ciyar da al'umma gaba. 


        A bangare guda kuma kungiyar za ta karrama wasu jerin kuma na 'yan asalin garin na Birniwa wadanda suka bada gugudumma a harkokin rubuce-rubuce, adabi da kuma nishadi.

        

          Daga cikin wadanda za a karrama din akwai Ibrahim Birniwa (Marubucin Labarina na Arewa24), jarumi Hashim Yarima (IB na shirin fim din Dadin Kowa) da kuma mawaki El-Mu'az Birniwa. Za kuma a bayar da kyaututtuka ga zakarun gasar rubutun labarai da kungiyar ta saka a kan cutar corona.


        Har wayau a taron dai za a gudanar da baje kolin littattafai na 'yar kungiyar kana kuma za a bada damar sayar da fom din kungiyar JISWA


         A na sa ran taron zai kunshi manyan baki daga ciki da kuma wajen jihar wadanda suka hada da manyan malaman jami'o'i, manyan marubuta da kuma farfesoshi daga fannoni daban daban.

Reactions
Close Menu