“Karance-Karance Ya Zamo Linzamin Tafiyar Da Ragamar Rayuwata” Kawu Sule

Kawu Sule

Daga Dandalin POWA

Assalamu'alaikum warahmatullahi ta'ala wa barkatuhum. Barkanmu da warhaka, sannunmu da arziƙin sake saduwa a wannan lokaci na maraicen Lahadi daren litinin a cikin wannan gida na Potiskum Writers Association (POWA) mai tarin albarka domin gabatar da shirinmu na baƙon POWA. Shirin da yake kawo muku jajirtattun mutane daga cikin duniyar marubuta/manazarta masu sadaukar da tunaninsu, dukiyarsu da ma lokacinsu wajen ganin sun ɗabbaka adabin Hausa.


Garin Potiskum yau muka yiwa tsinke tare da yada zango domin lalubo baƙon namu na POWA a yau inda kuma muka samu nasarar ƙwaƙulo muku Sulaiman Abubakar (Kawu Sule) wanda ya kasance tsohon manazarci ne fasihi mai bibiyar adabin Hausa sau da ƙafa. Cike da ɗoki tare da nishaɗi muke gabatar muku da baƙon namu na yau. Ku kasance tare da ni mai jan ragamar shirin Amina Ma'aji (Maman Khairat) da abokan aikina; Aisha Muhammed Sani (Xayyeesherth) da kuma Hassan Bello (Salihi)  don karanta yadda tattaunawar tamu da baƙon namu ta kasance. Ga dai hirar tamu kamar haka;


Mai Gabatarwa: Barkanmu da sake kasancewa a cikin shirinmu mai farin jini na Baƙon POWA. Muna yi wa baƙon barka da zuwa, fatan ka iso lafiya?

Baƙo: Wa’alaikumussalam wa Rahmatullah. Barkanmu da wannan lokaci.
Mai Gabatarwa: Da farko zamu so mu ji cikakken sunan Baƙon namu tare da tarihin rayuwarsa a taƙaice.

Baƙo: Bayan Gaisuwa da girmamawa ga dukkannin ilahirin jama’ar wannan dandali mai tarin Albarka…Da farko dai kamar yadda ya gabata sunana Suleiman Abubakar (Kawu Sule). Ni haifaffen cikin garin Potiskum ne, an haife ni a shekarar 1989. Na fara karatu a makarantar Central Primary School sannan na halarci makarantar babbar Sakandire Ta Jeka-ka-dawo cikin garin Potiskum. Daga nan a 2009 na shiga karatu a makarantar koyon aikin malunta dake cikin garin Potiskum wato FCE Potiskum inda na karanci Ilimin koyan Aikin Noma wato Agricultural science Education. Sannan kuma bayan na kammala karatuna na shaidar zama cikakken malami na fara aiki da makaranta mai zaman kanta a matsayin malamin aji a Alfurqan Learner's Academy Potiskum inda na shafe shekaru uku cur ina koyarwa. A shekakar 2016 Allah ya sahale mana muka bude tamu makarantar mai suna Premier Academy duk dai a cikin garin Potiskum din inda na samu matsayin Headmaster. Daga nan kuma na koma Jami’ar Maiduguri don ƙaro karatu inda na chanja sheƙa daga ɓangaren ilmi zuwa fannin ƙere-ƙere, na koma karatu a tsangayar Kimiyya da Fasahar Noma wato Agricultural and Environmental Resources Engineering.

Mai Gabatarwa: Dakyau Allah ya ƙara basira. Shin baƙon  namu ya na da aure ne ko kuwa dai yana kan niyyar yi ne?

Baƙo: Masha Allah. Maganar aure kam gaskiya babu…sai dai kyakkyawar niyya kuma mai ƙarfi ma kuwa. Ina buƙatar addu’a da shawarwari daga gareku mutane masu daraja.

Mai Gabatarwa: kamar yadda muka sa ni dai baƙon namu makaranci ne, ko za mu iya sanin me ya ja  ra'ayinka wajen fara karance-karance?

Baƙo: Batun karance karance zan iya cewa gado na yi don na tashi na ga kakata, mahaifiyar mahaifiyata tana yi kuma haka zalika mahaifiyata ma… kawai tashi nayi na tsinci kaina a wannan lamari kuma Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu don kuwa an ci ribar karance-karance.

Mai Gabatarwa: ka yi karance-karance da dama ko nace ma kana kan yi, shin me ka ɗauki littafan Hausa ko nace wane kallo kake yi musu, mene ne kuma ra’ayinka kan masu batun cewa littafan Hausa na ɓata tarbiyar yara mata?

Baƙo: Masha Allah. To ni kam da na tsinci abu tun daga gida kin ga kuwa ai zan ce karance-karance ya zamo limzami na ragamar tafiyar da rayuwata. Haƙaƙa akwai littafan da suke ɓata tarbiya amman ba su da yawa kamar yadda ake tunani kuma gaskiya ban taɓa ganin inda karance-karance ya zama aikin banza ba, ko ba komai yana taimakawa wajen haɓɓaka ilimi da kuma zurfin tunani.

Mai Gabatarwa: Da kyau. me za ka ce game da marubutan batsa kuma wane irin jan hankali zaka yi garesu?

Baƙo: “Dukkan abin da ka aikata zaka ga sakamakonsa” Haƙiƙa dukkan wanda ya yi rubutun batsa wallahi sai ya yi da na sani a rayuwarsa, tarihi ai ya nuna dukkan masu aikata irin waɗannan abubuwa sukan kasance cikin da na sani. Ina ga ba shi da amfani mutum ya aikata abin da zai yi nadama wanda daga baya idan ka tuna hankalinka zai tashi kuma fa yana bin zuri’a. Allah ya ba mu ikon aikata alheri.

Mai Gabatarwa: Ameen ya Allah. Shin kana da ra'ayin fara rubutu kamar yadda kake karanta na wasu ko kuma dai sha’awarka ta taƙaita ne ga karatun kawai?

Baƙo: Gaskiya ina da muradin farawa amman kuma ai harkar tana buƙatar ƙwarewa da kuma sanin ka’idojin rubutu. Insha Allah kasancewa tare da ku zai taimaka min wajen ganin na cimma burina.

Mai Gabatarwa: Wane abu ne ka yi tun na yarinta wanda idan ka tuna ko kuma a ka tuna maka yake ba ka dariya?

Baƙo: Don Allah kar ku yi min dariya…Abubuwa biyu ne suka kasance da ni wanda kullum idan na tuna sai na murmusa ko kuma idan mun haɗu da ita wacce abin ya faru da ita. Na farko, akwai wacce nake so lokacin ina College kullum idan na mata abin alheri sai ta fara min addu’a da cewa, ‘‘Allah ya baka mata ta gari’’ na ɗauka tana nufin ita ashe ban sani ba an bayar da ita. Na biyu, muna hira a zaurensu wanda zai aureta ya zo ya wuce mu da ya fito harda ba mu kuɗi mu raba ashe sadakinta ya kai. Waɗannan abubuwan kullum ya kan ba ni dariya da mamaki.

Mai Gabatarwa: (Dariya) To ni dai ban yi dariya ba. A ƙarshe, me zaka ce game da wannan ƙungiyar ta POWA? Sannan wace shawara kake da ita gare mu dake cikinta da ma marubuta baki ɗaya?

Baƙo: Alhamdulillah. Gaskiya wannan dandalin shi ne zakaran gwajin dafi a dukkannin dandalin da nake dasu saboda na samu ƙaruwa sosai a wannan zaure kuma cikin ikon Allah na samu haɗuwa da gogaggun marubuta da kuma tsoffin class mates ɗina. Batun Shawara kuwa sai dai nace  a cigaba da gashi kawai don kuwa komai yana tafiya bisa tsari da kwarewa.

Mai Gabatarwa: Alhamdulillah. A nan mu ka kawo ƙarshen wannan shiri na mu mai farin jini wato Baƙon POWA. Mu na ƙara mika godiya gareka yallaɓai Kawu Sule, Allah ya saka da alheri. Ka huta gajiya. A madadin ni kaina Aisha Mohammed Sani wadda na tattara wannan shiri tare da abokan aikina Amina Ma'aji da kuma Hassan Bello Salihi nake ce muku sai allah ya kai mu wani satin, wassalam alaikum.
Reactions
Close Menu