"Kokarina a kullum rubuta abin da zai amfane ni da kuma al'umma" Jamila Rijiyar Lemo

Malama Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo fasihiyar marubuciya ce da ta daɗe a na damawa da ita a harkokin adabi inda ta ƙware a fannoni da dama da suka haɗa da rubutun littattafai, gajerun labarai da kuma rubutun fim a masana’antar shirya fina-finan Hausa wato Kannywood. It ace ta samu nasarar zamowa gwarzuwa ta biyu a gasar ƙirƙirarrun gajerun labarai na mata zalla mai taken ‘Hikayata’ wadda BBC Hausa take shiryawa a duk ƙarshen shekara. A wannan tattaunawa da ta gudana tsakaninta da Musaddam Idriss Musa zaku karanta abubuwa da dama na daga tambayoyin da wakilin namu yayi mata kama daga abubuwan da suka shafi rayuwarta da kuma yadda aka yi ta zama marubuciya har izuwa kan batutuwan da suka shafi nasarar da ta samu bara da kuma shawarwarinta ga masu sha’awar shiga gasar ta bana. Ga yadda hirar tasu ta kasance:
Malama Jamila Rijiyar Lemo 


Za mu so ki faɗawa makarantanmu tarihin rayuwarki a taƙaice


Assalamu alaikum warahmatullhi Ta’ala wa barakatuhu. To kamar dai yadda aka sani sunana Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo. An haife ni a shekarar 1980, na yi karatu tun daga firamare zuwa jami’a matakin digiri.


Ya aka yi kika zama marubuciyar littattafan Hausa?


Rubutun littattafaina ya samo asali ne tun ina makarantar firamare. Akwai wani yayana mai suna Yaya Nasir da idan mun dawo daga makaaranta yake zaunar da mu ya duba darusan da muka yi, yayi mana tambayoyi, abin da muka gane ya kara fahimtar da mu wanda babu gane ba kuma ya koya mana shi. Wasu lokutan ma yak an yi mana extra lesson na irin abubuwan da ya san za a yi mana su a gaba yadda idan an zo yi mana shi ba zai ba mu wahala ba. To a cikin haka wata rana, bayan y agama koya mana darasi saai na dauko wani littafin shi ina dubawa a ciki sai na ga wani rubutaccen labari na wa san kwaikwayo to ina gani na san rubutun shi ne kuma sai zuciyata ta ba ni cewa kirkirowa yayi sai na tambaye shi cewa yaya Nasir wannnan labarin kai ka yi, sai yace eh. To take a lokacin sai na ji cewa ai nima zan iya kirkirowa saboda daman ina karance-karance. To ban yi kasa a gwiwa ba sai nace da shi ai nima zan iya rubuta labara irin wannan, to take sai ya dauko littafi sabo don ya karfafa min gwiwa yace to ga shi je ki rubuta. To cikin ikon Allah na je nayi rubutun littafi guda yanzu haka ma yana nan a wajen shi sunan littafin idan baka ci naman kura ba za ta ci naka. Daga nan na cigaba da rubutuna har na tafi Sakandire har kuma na kai ga yin aure ina yi.Shekarar da ta gabata kin samu nasarar kaiwa zagayen ƙarshe na gasar Hikayata da BBC ke shiryawa inda kika zamo gwarzuwa ta biyu a gasar. Shin kawo yanzu ya kike kallon ita waccan nasara da kika samu?

Babu abin da zance gaskiya kawo yanzu bisa nasarar da na samu ta zamowa gwarzuwa ta biyu a gasar BBC Hikayata a shekarar da ta wuce, sai dai nace Alhamdulillah! Nagode Allah. Saboda wata nasara ce gagaruma da nake mata kallon ɗaya daga cikin abubuwan da suka zama abin alfaharina a rayuwata kuma ta zamo daga cikin abubuwan da suke sani nishaɗi da farinciki da jin daɗi a duk lokacin da na tuna. Saboda na farko duk abin da aka kira da suna gasa to duk fa wanda ya shiga ya san cewa kokawa ce da gogayya da juna, kowa yana ƙoƙarin ya kada wani ko kuma kowa yana ƙoƙarin a ce shi ne. To duk wanda ya yarda ya shiga, buƙatarsa da manufarsa ya ci nasara. To kuma ka shiga, ka samu nasarar nan…Allah ya baka, to ai ko kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Dole kuwa wannan abu ya sanya bawa farinciki da jin daɗi a rayuwarsa saboda wani abu ne wanda mutum ya shiga yana da tunanin cewa komai ƙwarewarsa da iyawarsa lalube ne a duhu saboda rashin tabbacin kai labari ko akasin hakan amma farat ɗaya sai ka ji ka kai labarin nan, Allah ya kaika. To babu abin da ya fi wannan farin ciki Alhamdulillahi...na godewa Allah a bisa wannan nasara da na samu ba zan taba mantawa da ita ba kuma na ji daɗin da har kawo yanzu ina kallonta a matsayin wani abu na alfahari a rayuwata. Alhamdulillah!


Kasancewar shekara ta zagayo inda kuma tuni aka buɗe ƙofar shiga gasar ta bana, me yake zuwa ranki da zaran kin tuna da gasar?

To hakika bisa zagoyarwar wannan shekara da aka bude gasar hikayata abin da yake zuwa raina na farko shi ne wato lokacin da muka yi rubutu na gasar hikayata na bara da kuma lokacin da ake ganiyar fitar da wadanda suka ci nasara a zagaye na farko. Ina cikin gwagwarmaya a makaranta muna shekarar karshe ta fita na kammala digiri a takaice ma ina zana jarabawa. To, dan fisha da na dan leka whatsapp dina a gidan marubuta sai na ga an turo labarai guda 25 da suka fito a zagayen farko. To sai na bi da sauri haka ina dubawa a na kusan karshe ko na biyun karshe ne haka sai na ga Ba Ayi Komai Ba. Nace kai ikon Allah sai nace to akwai kuma sauran rina a kaba, da sauran aiki fa yanzu kuma sai an fitar da guda 15 a ciki sannan kuma a fitar da guda 3. To sai na share na cire dai tunanin a raina na cigaba da karatuna. To bana mantawa na tafi makaranta ko washe gari ne ko yaushe ne, a dai tsakanin ne na manta dai yanzu amma dai ba zan manta da yadda abubuwan suka faru ba. Na shiga makaranta muna da jarabawa a rwnar na shiga da wuri ko karaywa ma daga gida ban samu nayi ba don naje kan lokaci tunda daga gida zuwa inda nake zuwa makaranta BUK ne a kuma newsite nake...akwai nisa. Ina zuwa na duba sai na ga ina da dan sauran lokaci akalla sai na tafi gurin cin abinci. To ina gurin cin abincin sai Al-Amin Daurawa wanda shi ma marubuci ne kuma dan uwana ne, kuma abokin aikina ne kuma ajin mu daya sai ya kira ni a waya. Sai yake cewa wallahi da zazzabi yake ba shi da lafiya amma da ya ga labarina ya fito a cikin ukun da suka yi nasara ya ji ma kamar ya warke kai yana taya ni murna. sai na ji abin kamar a mafarki…nace, ‘da gaske?’ yace wallahi, Allah ya bada nasara da sa'a. To, gaskiya wannan abin ba na mantawa da shi ina tunawa. To ina ina tashi ina zuwa aji zamu shiga jarabawa sai na ga coursemates dina suna ta kallona ana ta fadin Anti Jamila congratulations. Wannan ya rungume ni, wancan ya rikoni suna ta min fatan alheri har muka shiga jarabawa muka fito ana ta wannan maganar. Gaskiya na ji dadi course mates dina sun yi farinciki yadda ka san su ne suka ci wannan gasar haka suka nuna farinciki kamar su dauke ni su goya ni, ina tuna wannan. Sai kuma a duk cikin wannan gwagwarmaya da nake ciki, to a karshe ma dai a wannan shekara na daga abin da ke zuwa min a raina ranar da zamu tafi Abuja ma karbar awad din nan na bikin karrama mu sai dana zana jarabawa na tafi kuma a lokacin ma ban gama jarabawar ba akwai wasu kusan guda biyu zuwa uku a gabana ga shi ba interval (tazara). To wadannan duk wasu abubuwa ne da ba zan manta da su ba kuma suke zuwa raina a yanzu haka. Kuma cikin ikon Allah haka nan na tafi Abujan nan Allah yasa muka dan samu matsala ta rashin tashin jirgi, sai ya kasance bamu dawo akan kari ba kuma ga shi ban tafi da abubuwan karatun jarabawar tawa ba ga shi kuma ina shekarar karshe ne. To haka dai cikin hukuncin Allah na yita addua kuma Allah da ikonsa haka na gama karatuna lafiya ba tare da na samu matsala ba, aka ba ni satifiket dina. Alhamdulillah, to wannan abin yana dawo min a cikin raina bisa wannan shekara da ta wuce.Da BBC za su sake ba ki wata damar don tura labarinki a gasar ta bana shin za ki tura ko za ki ci girma ki bar wa sauran ƙananun marubuta mata dake ƙoƙarin jarraba tasu sa'ar?


(Dariya) gaskiya dai wannan tambaya ta dan ba ni dariya. To gaskiya ne abin da kuka ce, to shi hali na taimakawa da cin girma ba za a rasa yin shi ba za a rasa yin shi ba ana yin shi kuma ana yin shi ne a inda ya dace inda ya kamata amma sai nake ganin kasan kowa da ra'ayin shi da kuma akidarsa ta rubutu. To gaskiya akidata ta rubutu ina rubu ne bisa fadakarwa kuma kokarina kullum Allah ya ba ni ikon rubuta abin da zai amfane ni da kuma al'umma duniya da lahira. To harka ce ta bada gudummawa, abu ne wanda daman ance wanda ya kirkiri mummuna yana da zunubinsa da zunubin wanda ya bi shi haka wanda ya kirkiri kyakkyawa yana da ladansa da ladan wanda ya bi shi. To wannan aiki ne na lada ba zaka gaza ba, ba zaka fasa ba saboda duk abin da ka yi ka fadakar da mutane na ilimi to ai kana da ladansa. To wannan dalilin shi ne zai iya sawa nace da kamar wuya gurguwa da auren nesa, to wannan ra'ayin nawa da akidar tawa shi ne nake ganin ba lalle na iya cin girma ba musamman ma da nake ganin wannan gasa mataki ne guda uku; akwai na farko, akwai na biyu, akwai na uku. To sai nake ganin ta wani bangaren ma idan fa har mutum bai kure mataki ba ai yana da damar ya sake shiga gasar (dariya) Allah ya bawa gwaraza hakuri wadanda suka ciri tuta na farko gwarzayen shekara wadanda su ne masu lamba ta daya...to sai nace ai su ya kamata su ci girma tunda sun riga sun kure matsayi (dariya)  Allah ya huci zuciyarsu suma dai ban sani ba ko suna da ra'ayi irin nawa. To amma wanda yayi na uku da na biyu sai nake ganin akalla ai kamar yana da sauran dama, kamar zai iya kara shiga idan ya kure lambar shikenan sai a bari sai a iya hakurin. To amma dai kamar yadda na fada maka nifa wannan akidar tawa da ra'ayin nawa ba lalle na iya bari ba saboda tunanina idan na kai ga ci to rubutana inda ba na tsammani ma zai iya zuwa saboda BBC Hausan nan harka ce ta duk duniya bakidaya to shi kuma irin wannan abu ne da kake domin ka wayar da kan al'umma ka fadakar da su babu maganar gudu kuma babu ja da baya.


Jamila Rijiyar Lemo suna ne a yanzu da ya zama sananne a Najeriya, shin ko kin taɓa haɗuwa da wasu da suka bayyana miki cewa sun san ki ne bayan lashe gasar da kika yi ta Hikayata kuma ya kika ji?

Ko shakka babu, ko ba su da yawa akwai su gaskiyar magana. Saboda akwai wasu da idan na hadu da su musamman ma a makaranta saboda lokacin da abin ya faru idan baka manta ba na fada maka ina tsaka da rubuta jarabawa, to ko da muka dawo na cigaba da zuwa makaranta ina zana jarabawa. To, duk inda na shiga za a ce ga ni ai nice na ci gasar BBC a matsayin gwarzuwa ta biyu ana ta min fatan alheri da jin dadi. Musamman ma da yake library and information science na karanta, to laburarin makaranta gidana ne kullum ina nan ina ciki don kusan babu wani ma'aikacin laburaren da bai sanni ba kuma duba da cewa a cikin ma'aikatan wajen wadanda 'yan uwana ne tare muka yi karatu da su ko dayaushe muna tare a duk lokacin da wasu daliban suka shigo idan suka ji ana hirar za su jiyo su sa baki. Sannan kuma ta bangaren soshiyal midiya din nan za ka ga wasu sun turo cewa da suna jin sunana amma ba su taba karanta littafina ba amma duba da wannan gasar ta BBC din da aka fada ni ce gwarzuwa ta biyu daman suna jin sunan amma basu taba cin karo da rubutuna ko labari nawa ba suna so su karanta da sauransu. To kuma da yake gaskiya ni yanzu babu littafina a kasuwa saboda na kwana biyu ban rubuta littafi ba bisa yanayin karatu da abubuwa amma insha Allahu yanzu ma zan dora zan sake buga littattafaina na shigar da su kasuwa wadanda zan gyara ma zan sake rubutawa a sake bugawa insha Allah. Amma maganar sani tun lokacin da na rubuta kanya ta nuna kafin ma shan koko littafina na farko da na fara wallafawa gaskiya daga kasashen ketare ma da dama sun sha zuwa domin ganawa da marubuta kuma ina daya daga cikin wadanda ake turo su waje na don tattaunawa da ni, musamman ciyaman Ado Ahmad Gidan Dabino ya kan turo su su zo har gida. Akwai wani farfesa da zan iya kama sunansa Grand Parnes wanda ya zo Najeriya tun daga Ingila muka hadu a can gidan Dan Hausa yayi Interview da ni akwai wata Baturiya ita ma da ta taba zuwa har gida ta yi interview da ni to wannan ba wani bakon abu ne a waje na domin ina kyautata zaton hatta a laburaren Oxford dake Ingila ba za a rasa littafina na Kanya ta nuna ba.


Me yafi burge ki a taron karramaku da aka yi a waccan shekarar kuma yaya kike hasashen taron na bana zai kasance?

To gaskiya abin da ya burge ni game da bikin karrama mu na waccan shekarar bai wuce yadda suka canza salo ba musamman na rashin fadar wanda yake a matakin farko da na biyu da na uku har sai da ta kai aka kira sunan mu muka tafi muka zauna akan dandamalin taron kowa yana kallon mu muna kallon kowa duk ana saurare inda suka mamaye mu kowa bai san matsayinsa ba bai san matakin da labarinsa ya kai ba har sai lokacin da aka kira sunan shi aka fada mishi sannan zai san matakin da ya taka. To wannan ma wata burgewa ce tunda sun yi yawo da hankalinmu sun sa mu a tunani tare da masu kallon mu da masu sauraren mu kowa ya zaku yana son ya ga waye ta daya, waye ta biyu waye ta uku to wannan ma wata burgewa ce da suka fito da shi daban. To sai dai kuma taron bana ba zan iya cewa komai ba saboda ban san abin da zai zo ya zo ba sai abin da muka gani. To amma ina kyautata zaton babu mamaki wannan karon ma su zo musu da sabon salo, musamman yadda na ga tun daga kan kalar logo na Hikayata da aka sauya a wannan shekarar da muke ciki to babu mamaki wasu abubuwan ma kan iya canjawa kamar yadda muma a baya suka mamaye mu, amma sai dai abin da muka gani kuma muna musu fatan alheri kuma muna kasa kunne, Allah sa ayi lafiya a gama lafiya.


Wane kira kike da shi ga mata musamman gajiyayyu da waɗanda ke rubutu game da wannan gasa?

Kiran da zan yiwa mata gajiyayyu nasiha ce na suyi hakuri bisa duk halin da suka tsinci kansu domin a rayuwa kaddara iri-iri ce; akwai ta Allah akwai ta mutum. To na farko yanzu dai ina magana ne akan wadanda kaddararsu daga Allah ne kamar yadda muka sani cewa zafin nema ba ya kawo samu ba duk kowa gajiyayye ne za dube shi a matsayin rago ba ko wanda bai tashi ya nema ba. Kamar yadda ake cewa babu nakasasshe sai kasasshe. To gaskiya dai wadanda ya zamana cewa irin wannan ne sai su cigaba da hakuri da tawakkali, bakin da Allah ya tsaga ba ya hana shi abinci amma kalubalen guda daya ne su tabbatar da cewa masu nema ne su kuma dukkan mai nema yana tare da samu. Don haka ba za a zauna a  rashe ba dole su ci gaba da fafutuka har watarana a cimma rabo kuma da wahala da dadi babu abin da yake dorewa a ciki, inda rayuwa dole akwai ranar mutuwa. To duk halin da bawa yake ciki sai yayi hakuri musamman idan yayiwa kansa hisabi na cewar yayi imani Allah ne ya jarabce shi, to wannan shi ne nahihar da zan yi akan wannan bangare....sai kuma gajiyayyun mata da ya zamana cewa irin wadanda suke tsayawa ne bara, maula da kuma yawon bin gidaje don yin bara da sauransu suna kaskantar da kansu suna cewa a taimaka musu wannan ba daidai ba ne ba kuma dabi'a ce ta musulunci ba saboda ita maula da roke-roke ba shi da amfani a cikin musulunci Allah ya hana. Saboda haka ya kamata su yiwa kansu fada, hanyar nema tana dayawa domin ita sana'a yadda ta halatta akan namiji ta halatta akan mace matukar za ta kare mutunci da addininta don haka su tashi su nema babu maraya sai rago su kama 'yar sana'arsu wataran idan ba a samu ba wataran za a samu domin bara babu abin da ya kai shi wulakanci da kaskanci saboda haka sai a kiyaye.

Reactions
Close Menu