Sai an kawar da waɗannan matsaloli idan a na son cigaba a Kannywood - Momo

Fitaccen dan wasan Kannywood kuma mai gabatar da shirye-shirye a tashar Arewa24 da ke Najeriya, Aminu Shariff Momo ya bayyana mana matsalolin da suka fi addabar Kannywood.

Aminu Shariff (Momo)

Momo ya bayyana rashin iya sarrafa sakonni masu inganci a matsayain ɗaya daga cikin matsalolin Kannywood.

A cewarsa, "isar da sakonni masu kyau a cikin fina-finai ga al'umma abu ne mai muhimmanci amma a yanzu ana fuskantar matsalar sarrafa sakonnin masu inganci."

Dama dai masa'antar ta jima tana shan suka kan abin da mutane sukan kira yin fina-finai masu bata tarbiya.

Momo ya ce "akwai bukatar a koya wa masu rubutu da kuma masu gabatarwa yadda za su fitar da sakonni a fim dinsu ta yadda mutane za su fahimta, domin kaucewa masu cewa fim na bata tarbiya."

"Muhimmancin sako na bacewa ne a tsakanin siradin mai rubutawa da kuma mai bayar da umarni," in ji jarumin.

Wata matsala ta daban da ya tabo a yayin hirar ita ce rashin kudi. Jarumi Aminu ya bayyana cewa yadda ake satar fasaha a masana'antar ke sa mutane basu cin moriyar kudaden da suka Zuba domin yin fim.

"Lamarin da ke sa ake rasa masu zuba hannun Jari a yanzu."

Amma a daya bangaren ya nuna farin cikinsa kan yadda ake haska fina-finai a gidajen kallo na Cinema, a cewarsa yin hakan zai kare fina-finan Kannywood kuma zai hana mutane su Iya satarsu.

Momo ya kuma jaddada muhimmancin kare al'adu da kuma harshen Hausa ta hanyar fito da su a cikin fina-finai yadda ya kamata.

"Akwai dumbin labarai a kasar Hausa, idan ana sarrafa su a cikin fina-finai ta yadda za su burge wasu al'adun, hakan zai janyo mutanen waje su ji sha'awar zuwa arewa domin samun labarai."

Jarumin ya taimaka sosai wajen gina masana'antar tun da aka kafa ta duk da dai ya rage fitowa a cikin fina-finai saboda rashin lokaci kamar yadda ya sheda mana.

A yanzu ya fi mayar da hankali ne kan shirinsa na Kundin Kannywood wanda ake nunawa a tashar Arewa24.

Shirin kan karbi bakuncin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finai a Kannywood.

Reactions
Close Menu