"Ina da ra'ayin fara fitowa a fim din Larabawa" - Priyanka Chopra


Daga Musaddam Idriss Musa 

Shahararriyar jarumar nan kuma mai shirya fina-finai Priyanka Chopra Jonas wadda ta yi fice a babbar masana'antar shirya fina-finan kasar Indiya da ake kira Bollywood ta bayyana kudurinta na son fara taka rawa a matsayin jaruma cikin fina-finan daular Larabawa da ake yinsu da harshen Larabci.

(HOTO) Priyanka Chopra Jonas, jaruma kuma mai shirya fim a kasar Indiya


Jaruma Priyanka ta bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da kamfanin jarida na Africa News kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito inda ta bayyana cewa, tana matukar kaunar aikinta kuma tana sha'awar ganin ta yi aiki a masana'antun shirya fina-finan dake yankin daular larabawa duk kuwa da kalubalen da take da shi na rashin iya Larabci amma ta bayyana cewa wannan ba matsala ba ce, za ta iya koyon Larabcin duk kaiwa ga cika wannan kuduri nata.

Yawar kawai ban iya yaren ba, sai dai ina da muradin ganin an dama da ni a dukkan masana'antun shirya fina-finai a fadin duniya. Ina matukar son aikina kuma zan iya koyon sabon yare idan da bukatar hakan.
Jaruma Priyanka Jonas dai ta shafe shekaru ashirin a Bollywood kuma tana daga cikin manyan mata jarumai da fuskokinsu suka kasance ababen muradi da son gani a akwatunan talabijin din 'yan kallo. 

A shekarar 2000 ita ce ta lashe gasar sarauniyar kyau ta duniya kuma a shekarun baya kadan da suka wuce ne ta auri fitaccen mawakin nan mamallakin Jonas and Brothers wato Nick Jonas.
Reactions
Close Menu