"Abin da yasa muke shirya gasar gajerun labarai a duk ƙarshen wata" - Ƙungiyar POWA

A jiya Litinin Mujallar ADABI ta samu damar haɗo wani rahoto na musamman kan ƙungiyar marubutan nan masu amfani da harshen Turanci da kuma Hausa da shalkwatarta ke garin Potiskum na jihar Yobe wato Potiskum Writers Association wadda ake kira 'POWA' a takaice, inda ta  tattauna da shugaban ƙungiyar kan wasu batutuwa da suka shafi ƙungiyar da kuma neman jin abin da ya ja hankalin jangororinta wajen shirya gasar ƙarshen wata-wata da ƙungiyar ta ɗauki tsawon wani lokaci tana gabatarwa.

Ga abin da shugaban ƙungiyar Musaddam Idriss Musa ya bayyanawa Mujallar ADABI kan manufarsu ta shirya waɗannan gasanni da a yanzu aka shafe aƙalla watanni tara a na gabatar da su,

To, maƙasudin shirya ita wannan gasa dake gudana na tsawon sati ɗaya ko biyu a ƙarshen kowane wata abu ne da yake da alaƙa da tushe na kafa ita wannan kungiya. Domin yana daga cikin ginshiƙan kafa wannan ƙungiya tamu ta POWA taimakawa marubuta masu tasowa da ma waɗanda sun daɗe suna rubutun amma matsalar ƙarancin kuɗin da zasu buga rubutun nasu zuwa littafi yasa ba su kai ga wallafa su ba ganin cewa mun kai su ga samun ita wannan damar da zamu wallafa littafi mai ɗauke da gajerun labarai da kowanne da ya faɗa cikin waɗancan rukunai guda biyu zai ɗaga shi cike da alfahari tare da cewa nima akwai bugaggen littafin da ƙungiyar POWA tayi dake ɗauke da labarina a ciki. 

 

Da Mujallar ADABI ta nemi jin shin ko me yasa ƙungiyar ke zaɓar labarun ta hanyar gasa a maimakon kawai a buƙaci kowane marubuci da ya tura labarinsa a buga, shugaban cewa yayi,

To ai shi komai da mutum zai yi yana buƙatar tsari bare kuma abin da aka kira shi da sunan na ƙungiya, ƙungiyar ma kuma ta marubuta, mutanen da su al'umma ke yiwa ganin ke akan gaba wajen kawowa jama'a al'amura na cigaban rayuwa, wayewa da kuma riƙe musu al'adunsu daga ɓacewa...


...babu tsari idan aka ce kowa ya aiko da rubutunsa da sunan  cewa ƙungiyar mu za ta ɗauki nauyin bugawa saboda yin hakan a ƙarshe kan iya haifar da ma rikici da kuma ƙananan maganganu idan ba a yi sa'a ba, saboda kowa da ya turo zai yi tsammanin ganin labarinsa a ciki. Mu kuwa ba burin mu kawai a buga littafin ba ne, na daga cikin manufarmu labaran da za a wallafa ɗin su zama masu inganci waɗanda za su taimaki cigaban ƙasa da kuma al'ummarmu dalilin kenan ma da muke bayar da jigo a kowace gasa. in ji shugaban.


Musaddam Idriss Musa, shugaban ƙungiyar Potiskum Writers Association (POWA)


Dangane da batun lokacin da za a wallafa littafin kuwa ga abin da ya shaidawa Mujallar ADABI

Alhamdulillahi, a yanzu mun samu wata tara muna shirya wannan gasa kuma dama tun farkon fara gasar a sanarwar da muka fitar mun bayyana wa jama'a cewa za a ɗauki tsawon shekara guda ne a na yi, inda za muna zaɓan labaran da suka zo daga kan mataki na ɗaya zuwa na uku, amma idan ya zama cewa akwai labarun da muke ga sun cancanta su shiga kundin ko da kuwa ba su faɗa a jerin waɗannan matakai ba mukan faɗawa masu shi cewa labaransu zasu samu damar shiga kuma zasu samu kyautar da ta dace da irin nasu matsayin a yayin bikin karrama gwarazan gasar da kuma ƙaddamar da littafin wanda zai faru bayan mun kammala aikin tarjamar labaran zuwa harshen Turanci wanda yanzu haka kwamitin kula da wannan aikin na kan yin hakan domin littafa biyu ne za mu wallafa masu ɗauke da labaran a cikin harsuna biyu.


A na sa ran dai cewa akwai nau'ikan kyaututtukan da ƙungiyar ke tanadi ga gwarazan gasar wadda a yanzu ta ɓoye kamar yadda shugaban ya bayyana ma cewa ba yanzu ne lokacin faɗa ba a yayin da muka nemi jin ta bakinsa kan hakan.

Reactions
Close Menu