A daren jiya Alhamis alkalan gasar kungiyar marubutan nan mai suna Potiskum Writers Association (POWA) suka fitar da sakamakon gasar kungiyar mai jigo akan 'Nadama'.
Sanarwar sakamakon wadda aka bayyana a shafin yanar gizo na kungiyar na dauke da jerin sunayen marubutan da labaransu suka yi zarra a kakar gasar.
Ga jerin sunayen marubutan da suka lashe gasar kamar yadda aka wallafa a shafin kungiyar;
Bangaren gajerun labarai:
1. Zulaiha Haruna Rano a mataki na daya.
2. Sumayya Babayo Abdullahi tare da Rabi Garba Tela a mataki na biyu.
3. Muntasir Shehu a mataki na uku.
4. Nabila Rabi'u Zango a mataki na hudu.
Labarai masu alaka
● Kwamitin alÆ™alai sun bayyana marubuta shiga da suka yi nasara a gasar gajerun labaran powa
Bangaren Rubutattun wakoki:
1. Isah Muhammad Machina na daya
2. Ibrahim Auwal Abubakar na biyu
3. Mahmudul Kalam na uku
Za a iya ganin sakamakon a shafin kungiyar ta hanyar wannan mahada; sakamakon-gasar-gajerun-labaran-powa
0 Comments