Wasa Waƙe a Bisa Faifan Nazari: Duba Daga Waƙar Sambisa ta Abdullahi Al-Hassan Liyaliya

Tare da Dakta Ahmad Salihu Bello ƙwararren malami a sashen Hausa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Zaria.

Waƙar Sambisa waƙa ce da a yanzu take kan tashe wanda hakan yasa ta mamaye lunguna da saƙo na sassan arewacin Najeriya. Saboda kaɓuwar da waƙar ta samu ne ya sanya babu babba ba yaro, ko'ina akan samu waɗanda ke hirar waƙar musamman kan kalaman cikinta da kuma salon barkwancin da waƙar ta zo da shi wanda dalili na wannan karɓuwa da waƙar ta samu ya sanya mawaƙin cigaba da sako jerin wasu waƙoƙin a matsayin cigaban waƙar ta farko.

          Tasirin da ita wannan waƙa take da shi a fanni daban-daban da suka shafi rayuwar al'umma da kuma fito da wasu muhimman al'adu na Hausawa ne yasa Dakta Ahmad Salihu Bello wanda ya kasance ƙwararren malamin Hausa ne a Kwalejin Ilimi ta Tarayya dake Zaria, ya zauna tsam tare da rubuta cikakken nazari kan ita wannan waƙa mai suna "SAMBISA" don amfanuwar al'ummar Hausa da kuma harshen Hausa.

Ga nazarin Daktan kamar haka:

Gabatarwa

Masana adabin Hausa sun yadda kalmar adabi ta sama asali daga Larabci. Gusau (2011) daga Larabci kalmar ita ce adab ko abd (tilo ko a'ab (jam'i), wasu kuma suna ganin daga adda ba (tilo) ko adab (jam'i) aka sami asali na kalmar (Gusau, 2011). Masana irin su ɗangambo, (2008) Gusau, (1991) Rufa'i (1981) sun yi ittafaƙin Adabi a lugga tana iya zama; fasaha ko ƙwarewa ko hanyar yin wani abi ko abu mai ƙayatarwa ko halaye kyawawa. Adab na Larabci ya ci gaba inda ya ƙunshi ayyuka na ɗan'Adam, musamman hikima da azancin magana. Gusau (2011): daga baya, adab na Larabci ya taƙaita ne a kan waƙa da zube, kuma kan haka aka yi masa rubuce-rubuce masu yawa tun a ƙarni na 6.

Adabi na Turawa ta wannan fuska, adabi ne wanda aka samo shi tun a tsakanin ƙarni na 5-6. Musamman bayan bunƙasar daulolin na Girkawa da Ramawa kuma adabin Ingilishi an samar da hanyar rubua shi ta yanayin rubutun Latin daga Romawa (Gusau: ix). Adabin turai ya haɗa maganganun hikima da waƙoƙin baka da kaɗe-kaɗe da sauransu.

Haɓakar ilimi da yawaitar fannoninsa a ƙasar Turai sun janyo aka sami hada-hada ta ayyukan adabi daga mutane daban-daban. Alal-misai, yaƙin noma (mutanen Scandanaria) da kafa mulki a ƙasar France da Italy da Ingila sun ƙara zuguguta ayyukan rubutaccen adabi. A ƙarni na 16, Willams Shakespeare da muƙarrabansa sun ƙarfafa rubutun wasannin kwaikwayo da zube. Zuwa yau rubutaccen adabin Turai ya bunƙasa matuƙa kuma ya sami marubuta, manya da ƙanana da sassan adabi daban-daban da kuma ƙungiyoyin adabi iri-iri (Gusau, 2011:v1).

Gusau (2011) ya ce adabi a wajen Hausawa sun bayyana shi ta hanyoyi da dama kamar yadda masana irin su Yahaya, (1973) da Umar (1978) da Yahaya da Muhammad (1976) da Sa'id, (1981) da Batura (1985) da Rufa'i (1981) da Gusau (1984) da Yahaya, I.Y suka yi ittifaƙi a kai da cewar adabin Hausa, adabi ne wanda ya shafi hikimomi da sarrafa harshe da kuma hanyoyi. Waɗanda suka shafi tafiyar da rayuwa ta yau da kullum, kuma yakan zama mai yin darasu da hannunka-mai-sanda ko mai barbaɗa gishiri a rayuwa. Gusau, 2011:3).Wasan Kwaikwayo da Kashe-Kashensa

Umar, (2020) ya raba wasan kwaikwayon Hausa dangane da tushensa da kuma kashe-kashensa zuwa gida biyu. Wato akwai wasanni na dauri akwai kuma na zamani. Ya ce wasannin kwaikwayo na gargajiya su ne waɗanda ake da su tun kafin zuwan baƙin al'adu cikin al'adun Hausawa waɗanda suka gada tun iyaye da kakkani. Ire-iren waɗannan wasanni sun haɗa da: wasan Gauta da wasan Dandali da wansa magi da wasan kalankuwa da wasan tashe da wasan 'yan kamanci da wasan hawa dokin kara. Duk waɗannan nau'o'in wasan gargajiya ne. Amma wannana maƙalar tana ganin shin ya dace a shigo da wasan tashe rikunin wasannin kwaikwayo na gargajiya? Domin idan ana batun wasannin gargajiyar Bahaushe ana tsammanin wasanni ne da aka yi kafin zuwan musulunci ko masu kama da bautar gargajiya, kuma idan aka dubi duka wasannin da Umar, (2020) ya lissafo a matsayin na gargajiya duk suna nuna tsatsube-tsatsube da hatsibibanci da kuma bautar gargajiya. Ana iya ware wasannin gargajiya bayan zuwan musulunci suna masu cin gashin kansu. 

Har ila yau Umar, (2020) ya yi ƙoƙarin zayyano wasannin kwaikwayo na zamani. Inda ya ce shi irin wasan kwaikwayo da za a gani ya kunno kai cikin ƙasar Hausa sakamakon cuɗanya da wasu baƙin al'adu da Hausawa suka yi da wasu al'ummomin waɗanda kuma suka yi tasiri a kan Hausawa. A wannan nau'in wasan kwaikwayon an sami yin amfani da ƙarin wasu abbubuwa da ci gaban zamani ya kawo. (Umar, 2020:282). ƙarin bayani a kan abubuwan da zamani ya kawo a cikin irin waɗannan wasannin zamani shi ne, ilimin zamani (boko) ya haifar da rubutaccen wasan kwaikwayo tare da na'u'rorin ɗaukar hoto da murya a rediyo da talabijin ko magiji ko bidiyo ko satilat. Kamar yadda aka lissafo wasannin kwaikwayo na gargajiya wannan shi ma yana da ire-irensa kamar haka; wasan Daɓe ko Dan damali da wasan kwaikwayo na littafi da wasan kwaikwayo na rediyo da wasan kwaikwayo na talabijin da beben wasan kwaikwayo da wasan-waƙe (Umar, 2020:254:285).

Taƙaitaccen Tarihin Mawaƙin Waƙar Sambisa

Sunansa Sani Abdullahi Alhassan inkiya (Liyaliya-Bura) haifaffen garin Bura da ke ƙirfi Local Goɓernment jihar Bauchi. Sana'arsa waƙa yakan rubuta ya sayar tun daga waƙoƙin siyasa da na sarauta. Yakasance mai yawan kallon fina-finai na Hausa, amma shi ba fim ɗin ne ya dame shi ba, illa ya fi mai da hankali wajen kallon da jin saƙon da waƙoƙin fina-finan Hausa suke nusar wa. Allah cikin ikonsa yau ya zama mawaƙi sama da shekara goma-sha ɗaya. Kaɗan daga cikin waƙoƙinsa akwai; Sambisa, da Kishiya da Matar Sarki da dama. Dalilin sa na yin waƙar Sambisa shi, ya ga yawancin mawaƙan yanzu sun fi raja'a wajen gina waƙoƙin soyayya in suna son nishaɗantar da mutane. Sai ya karkata wancan tunanin ta shigo da matsalar aiwatar da soyayya da kuma waƙe a cikin tasa fasahar. Ta yadda hankalin mutane zai dawo kai. Shi ya sa ya yi tunanin ƙirƙirar waƙa yana alaƙanta da Sambisa. Ga kaɗan daga kalamansa kai tsaye a wata hira da aka yi da shi ta Legit T.V 2020.

Bari in ƙirƙiro wani abu wanda nishaɗantar da mutane, kuma ya ba su dariya, sai na danganta waƙa na da Sambisa, na zaɓi saurayi mai naci da nemo mace (Budurwa na haɗa su) na dai tsaya na yi tunani da lissafin yanzu a ce mutum ne ya ga mace ta burge shi bai santa ba, bai san daga ina take ba yana sonta. Ta ba shi dokoki ya ce duk ya yarda wato itin samarin nan 'yan kanzagi ya yi azarɓaɓin binta. Daga ƙarshe sai muka yi tunanin ta yaya zamu yi maganin irin waɗannan samarin a cikin waƙar ta raha da nishaɗi sai muka ce tace daga Sambisa take kuma daga baya an ga yadda ake yin tababa. Hira a Legit T.V. 08089559243. Sambisa

Sambisa dai daji ne wanda yake a yankin ƙasar Borno, a shiyar Arewa maso gabashin Nijeriya, Sannan tana shimfiɗe a ƙasa ta yamma maso kudanci ƙasar Chadi ta kuma yi iyaka da dajin yawo buɗe ido na namun daji (watoral nark) na Chadi ta ɓangaren Kudu. Tana da muraɓa'in kilomita sittin (60 kilometers) ko mil 37 a ta ɓangaren yamma maso gabashin Maiduguri. Babban birnin jihar Borno. (Sambisa Forest-Wikipedia).

     Dajin Sambisa ya zama wata mafaka ko maɓoya na Boko haram shekaru sama da goma wani Konal ɗin Soja ɗan ƙasar Kamaru Abubukar Bakari wanda yana ɗaya daga cikin manyan kwamandoji masu yaƙi da boko haram ya tabbatar da cewa; Sambisa daji ne mai mutaƙar haɗari, saboda nan ne ainihin babbar matattarar 'yan ƙungiyar Boko haram. Boko Haram dai sunan da aka fi kiran wata ƙungiya ce masu iƙirarin kafa tutar musulunci a Nijeriya da wasu jihohin yammacin Afrika irin su Nijer da Kamaru da Chadi. Ta dai samo asali daga Nijeriya ta hannun Muhammad Yusuf a shekarar (2004) a Ingilishi akan kira sunan ƙungiyar da Islamic state in west Africa. Ko kuma a harshen Larabci ana kiran su da Jama'at Ahl'assunnah Lid Da'awah Wal-Jihad. Wato ƙungiyar mutanen sunna da wa'azi da jihadi wanda aka fi sani da Boko Haram. A yanzu Abubakar Shekau ne yake jagoranta tun shekarar 2009. A bisa dalilin gumurzu da bata kashin da sojojin sukan yi da 'yan ƙungiyar har ya zama sama da mutane miliyan 2.2m suka salwanta a yankin shi ya sa babu wani mahalukin da zai faɗa dajin Sambisa siddan domin zama ko neman wani abin duniya ba, ba bisa dalilin tsaro ko kuma hukumance ba. Don haka, dajin Sambisa ya zama dodon daji wanda idan har mutum ya shiga to watakila sai dai ka zama gawa. Ganin haka ne, wannan mawaƙi wasan-waƙe yake yi amfani da tunaninsa domin tsorata samari masu nuna soyayyar yaudara da cewa Sambisa a can za a ɗaura aure ko kuma budurwar ta ce Sambisa nan ne garin su domin a gwada ƙarfin son da yake wa Zainab na gaske ne ko na ƙarya ne.

Wasan Kwaikwayo 

Daga jin sunan ana ƙoƙarin kwaikwayon wani abu ne domin a yi raha ko nishaɗi. Umar, (2020) ya ce wasan kwaikwayo harɗaɗɗen suna ne, wato wasa da kuma kwaikwayo, waɗanda suka haɗu suka tayar da wasan kwaikwayo ƙamusun Hausa na CNHN (2006:470) ya ce kalmar wasan tana nufin aiwatar da wani abu don raha ko nishaɗi; ko kuma yin wani abu wanda ba gaske ba. Sannan kwaikwayo tana nufin kwatanta yin wani abu da ya taɓa faruwa a zahiri; ko koyan wani abu da wani ya yi, ko yake yi. Don haka, idan aka haɗa kalmomin guda biyu wasa da kwaikwayo za ta shi kalma guda ɗaya wato wasan kwaikwayo, wato aikata wani abu da yake faruwa a cikin al'umma bisa kwatanta yadda wani ko wasu suke yinsa a zahiri ko kuma a siffar ƙirƙirar wasa domin a nishaɗantar ko a ilimantar ko wayar da kai da sauran jigogin makamanta soyayya da hani ga aikata mummunan halaye ko kuma yin koyi da kyakyawa. Wannan ra'ayi ne wanda ya yi dai-dai da na masana irin su ɗangambo, (1984) da Malumfashi, (1984) da Ahmed (1985) da Umar (1987) da Yahaya (1992) da Furniss (1996) da 'Yar Aduwa (2007) da Umar (2014) Bello, (2016) da kuma Umar (2020).
Zumuntar Waƙa da Wasan Kwaikwayo

A baya an yi bayani a kan nau'o'i da ire-iren wasan kwaikwayo tun daga na gargajiya zuwa na zamani. Haka ma ita waƙa ta kasu kashi biyu akwai waƙoƙin gargajiya akwai na zamani wanda, kuma kowanne nau'i. Yana da siffofin da yanaye-yanayensa da kuma yadda ake aiwatar da shi tare fasahohinsa. A nan ana so a nuna cewar akan samu wasu nau'o'in wasan kwaikwayo wanda akan aiwatar da su tare da raƙ------ waƙa. Don haka za mu iya kafa hujja idan muka kalla maƙalar Umar (2020) inda ya ce daga cikin nau'o'in wasan kwaikwayo na zamani akwai wasan Rere.

Wasan-Waƙe

Shi wannan wasa yana zuwa cikin salon waƙa, mawaƙi ko mawaƙa ne za su tsara waƙe amma idan aka lura za a fahimci cewa wasan kwaikwayo ne kawai. A wannan wasa akwai wani salon aiwatarwa mai karsashi cikin gwanintar iya sarrafa murya ta hanyar wargantawa, Umar, (2020:285). Wato dai, idan mawaƙi ɗaya ne zai riƙe kwaikwayon muryoyi a waƙe a matsayin taɗi yayin da idan mawaƙa biyu ne - namiji da mace - za su riƙa bayeyeniyar baitoci a matsayin taɗi. Sannan suna amfani da sassa na gaɓoɓin jikin suna aiwatar da abinda suke rarara a aikace, ta yadda mai saurare zai iya kallon su a zahirin Bidiyo ko talabijin ko faya-fayen C.D. kaɗan daga cikin misalai na irin waɗannan wasarare ko waƙaƙƙen wasu su ne; funmi Adams cikin waƙarta Ina Gizo yake da ɗanmaraya Jon cikin waƙar Karuwa ta zuwa gun Boko, wato sukan yi calikanci ko 'yan kamanci a cikin irin wannan wasa kuma yawanci za a ga dama daga cikin jigogin ire-iren wannan wasa na wasa-rare yakan ba da fifiko a kan illar yin ƙarya ko cin amana ko kuma faɗin gaskiya ko zalunci tare da hani da munanan ayyuka misali; waƙar funmi Adam ta inda Gizo yake: jigonta hana ƙarya, haka nan ita ma ta ɗan Maraya Jos, kaɗaita Allah a daina zuwa gidan Boka da hani da karuwanci ko illarta. Da wannan ne maƙalar take ganin wasan-Rare ya faɗo cikin rukunin wasan kwaikwayo na zamani. Dalili shi ne shi akan aiwatar da shi bayan a rubuta labarin tare da yadda ake son a tsara waƙar. Sannan bayan an rera waƙar ne za a zo yi daddatsa labarin yadda za yi shirin wasan kwaikwayon waƙar wato (script).

Rubutun Fim

Shi ya ƙunshi ginin labari ne da hoton murya takan shigo ne kaɗai a inda ake da buƙata a faɗaɗa ko a fito da hotunan sarari don mai kallo ya kara fahimta. Me yasa? saboda shi fim ana yin sa ne ga duniya baki ɗaya, babu maganar bambancin harshe, ana sa ran idan aka yi fim kowacce al'umma ta iya kallonsa ta gane ko da babu fassara, ba kamar littafi ba, shi fim ba a yinsa da yawan zance da hoto ake yinsa. Duk fim ɗin da za rufe sautinsa a ƙura wa hotunan ido ba a gane me ya ƙunsa ba to wannan fim bai yi ba. Babinlata, (2020:15) da wannan nake cewa wannan maƙala ta tsamo wata waƙa mai ɗauke da siffar wasa-waƙe. Wanda Sani Abdullahi Liya-Liya ya rubuta, shi kuma Yamu Baba (Angon Sambisa) da Zainab Usman Aliyu (Amaryar Sambisa) suka aiwatar da shi cikin siffar wasan kwaikwayo a shekarar 2019 zuwa 2020 daga kashi na ɗaya zuwa kashi na huɗu. Wanda Kamfanin IBSP International, Jos suka ɗauki nauyi wanda kuma Abubakar S. Shehu ya ba da umarni.

Ra'in Wasan Tir-Madalla

Wannan maƙalar ta ɗora kanta a kan ra'in tir-madalla, Sulaiman (2019) ya ce wasan tir-madalla shi ne gwama siffofin wasan ban tausayi da na raha ko barkwanci a cikin wasa guda. 

Waɗannan siffofi kan iya kasancewa na zubin wasan ban tausayi amma sai a ƙarshe wasan ya ƙare da farin ciki ko sulhu. "A zamanin wayewar kai nau'in wasan tir-madalla ya ɗauki wani salo na ɗaukar duk wani wasa wanda gwarzon ya kusa hallaka a matsayin tir-madalla, ko kuma wasan da aka sami kaucewa mutuwa ko haɗarurruka ko kuma sauyi daga halin ƙunci da ake fuskanta zuwa ga ƙarewar wasa cikin farin ciki, waɗannan na daga cikin siffofin wasan tir-madalla. (Sulaiman 2019:49).

Manazarcin ya nuna cewa a ƙarni na sha tara, ana danganta wasannin Ibsen masu suna Ghost (1881) da The Wild Duck (1884) da Uncle ɓanya (1900) da The Cherry Orchard (1903) a matsayin wasanni masu ɗauke da siffar tir-madalla. Manazarta da dama sun yi amfani da wannan ra'in wajen nazartar wasannin kwaikwayo, kaɗan daga cikinsu sun haɗa da Bond (1999) (Plautus Amphu trypn as Trage Comedy) da Seɓerin, (1989) (tragi comedy and Noɓelistic Discurse in Celestine) da Sulaiman (2016 da 2019). Wannan maƙalar ta yi amfani da wannan ra'in wajen nazartar wasan kwaikwayo na wasan-waƙa. Saboda shi wasa-waƙe yakan assasa ne da siffar waƙa a matsayin wasan kwaikwayo kamar yadda su Willians Slakespare suke yi da su Aristole da Cuddon kafin ya rikiɗe zuwa aiwatattcen tare rakiyar kiɗa da waƙa a lokaci guda.

Hanyoyin Nazarin Wasan Kwaikwayo Na Fim

Kamar yadda sauran sassan adabin zamani suke da dabaru ko hanyoyin da ake ɗaura su domin nazarin su ko yin turke kamar waƙoƙi da zube, haka nan shi ma a fim ɗin Hausa yana da nasa mazubin da a akan auna shi da shi domin a tantance tare da tsattafe aya daga cikin tsakuwa fim baya tabbata sai da su. Wadatar waɗannan sanadarai a cikin fim shi ne tushe ko dirkoki wanɗanda suke madogara na yin nazarin fim ɗin Hausa.

Haruna, (2012) da Bello (2018:53-54) sun yi ittifaƙi a kan wasu dabaru da za a iya baje kowanne irin fim ɗin Hausa a kan su domin a gano cancantarsa da kuma matsayinsa ko darajarsa a fagen nazari. Wanda rashinsu a cikin fim ka iya rusa fim ko kuma dusashe armashinsa gaba ɗaya. Waɗannan dirkoki na nazarin fim su ne; jihon fim da tsarin fim da 'yan fim ɗin ('yan wasa) da harshen fim da tufafin fim da kayayyakin fim (properties) kwalliya a fim da sautin fim da mahallin fim da labarin fim da kuma uwa uba masu ɗaukar nayuinsa tare da bayar da umarni da ma'aikatan bayan fage.

Waɗannan su ne ginshiƙai, waɗanda suke dole a ga matsayinsu da bayyanarsu a cikin kowanne irin fim. Bari mu ɗauke su ɗaya bayan ɗaya a yi musu sharhi ɗaya bayan ɗaya a taƙaice domin a haskakawa mai karatu fitilar nazarin fim a Hausa.

Muhallin fim: kalmar muhalli an aro ta ne daga harshen Larabci wa Al'muhallun. A lugga yadda Hausawa suka aro ta daga Larabci ba su sanya mata siga ko tsari ba. Ta fuskar ma'ana kalmar muhallu a Larabci tana nufin bigre ko wuri da ake amfani da shi a fagen ilimi. Salad (1981) ya ce Hausawa na kallon muhalli a matsayin tsare-tsaren da magina ke yi a ƙasar Hausa da kuma irin ƙyale-ƙyalen na nuna ƙwarewa a wajen fagen samun muhalli da kuma hanyoyin nuna gwaninta ta wajen ƙirƙira da amfani da magani da wasu al'adu don hana ɓacin muhalli haka kuma da amfani da sihiri, don kare martaba da samar da wurin zama (muhalli) a ƙasar Hausa. (Soba, 2015:1-3). Idan muka yi la'akari da ma'anonin muhalli mabambanta za a iya cewa, muhalli mazaunin da ke kewaye da mutum da dukkan abubuwan da suke taimakawa rayuwarsa na yau da gobe. A tsarin nazarin fim ɗin Hausa, muhalli babban ginshiƙi ne wanda a kan sa akan gina kowanne irin wasan kwaikwayo. Muhalli a wasan kwaikwayo yakan iya kasance dandamali wanda za a yi masa ƙawa da kayan wasa daban-daban, ko kuma gida ko fadar sarki ko tashar mota wato abinda dai aka fi so a nazari muhallin ya amsa sunansa na muhallun da aka tsara za a yi amfani da shi a wasa dai-dai da yadda labarin fim ko wasan kwaikwayo ya zo da shi.

Nazarin Wasa-Waƙen Kwaikwayon Waƙar Sambisa

Ƙamusun Hausa (2007) ya ce nazari yana nufin duba abu ko tsokaci ta hanyar karatu a zuci ko kuma bincike game da wani abu. Shi kuma wasa-waƙe nau'o'in wasan kwaikwayo ne mai ɗauke da siffofi guda biyu zuwa uku a haɗe lokaci guda wajen aiwatarwa. Wata waƙa da kwaikwayon abinda mawaƙar yake furtawa haɗe da barkwanci kamar 'yan kama. Wato yana wasa wanda aka fara tsara shi a bisa waƙem daga baya aka ɗaura waƙe bisa faifan kwaikwayon waƙe tare da raƙiyar kiɗa da kuma aiwatar a cikin tsarin ɓedio ko C.D. ko kuma magiji. Kamar yadda ya gabata a farkon wannan maƙala waƙar Sambisa an sanya mata siffa da nau'i zuwa wasa-waƙe a matakin wani sahon salo don ilimantar da al'umma da faɗakarwa da nishaɗantarwa. Bari mu ɗauki siffofin nazarin wasan kwaikwayo mu ɗaura waƙar a kai domin nazarinta.

Jigo: kamar yadda sunan ya nuna jigo shi ne manufa ko ginshiƙi. To jigon wannan wasa-waƙe na Sambisa shi ne soyayya da faɗakarwa, ƙaramin jigon kuma barkwanci ta hanyar aiwatarwa don nishaɗantar da masu kallo.
Soyayya: kalma ce wadda take nuna ƙauna daga ɓangarori biyu na masu ƙaunar juna (ƙamusun Hausa 2007:398). A cikin wannan wasa-waƙa mai taken Sambisa an ji inda saurayin Zainab wato Liya-liya yake kawo wasu jerin kalaman soyayya na jan hankali wato na gani ina sonki, kuma ba zai g------

Liya-liya: 'yan mata don Allah ɗan dakata, takunki ya wuce harda ni ga tozalinki mai kyalkali, wankanki ya yi rufa dani.

Zaibab: malam dan Allah ka sanni ne, kake ƙoƙarin misalai da ni.

Liyaliya: A'a wallahi ban saki ba, kawai dai kama kike yi da ni dama ina da cuta a rai, yau jalla ya ɓiɗan magani.

Zainab: kai ni da baƙuwace a nan garin, kate neman sabo.

Liyaliya: batun bakuwa koko 'yar gari ni wannan ba zaya dame ni ba.


A cikin wasan kwaikwayo an nuna, Liyaliya shi da abokansa suna zaune ƙofar gida, yana ganin wata budurwa tayi fakin da mota, ta ɗauko jakarta ta rufe but ɗin motarta sai ya yi zumbur ya miƙawa sauran abokan nasa lemon kwalbar fanta da ƙaton burodin da yake hannunsa ya bi ta da kallo yana mai faɗin kalamai na gani ina so, ita kuma Zainab tana ba shi amsa gwargwadon yadda yake kawo mata harin son da yake mata don neman ta amince masa na aure. A nan za mu iya cewa aure ba ya tabbata sai da soyayya kuma sai namiji ya gani sannan yake cewa yana so. Wato wannan wasa yana jaddada cewa a bisa al'adar Bahaushe namiji ne yakan nemi mace da aure, ba kamar yanzu ba zamani ya juyar da tadar sama ya dawo ƙasa bari muji:

Liyaliya: to! mu je ma gidan ku in gaida su, a shirya rana a yi,

Zainab: to! ni garinmu ba nan ba ne, hanyar zuwa ɓata za a yi,

Liyaliya: garin naku ko a rami yake, nace da ke zu za na yi kin san garin masoyi ba ya nisa ga wanda ya yi ra'ayi.

Zainab: to! in kana buƙata zuwa komai nisa za ka yi?

Liyaliya: mu wuce tasha muzarce ta can garin in bai wuce Ghana ba.


A nan Liyaliya ya nuna zaƙewarsa, ta son zuwa gidan su Zainab ya gaida iyayenta, duk da nuna masa garinsu da nisa amma shauƙin so ya kwashe shi, dole sai ya je ya gaida manyanta, kamar yadda aka saba a bisa al'ada, kuma ya ce ko garin su rami ne ba Ghana ba shi kam a shirye yake, kuma wani salon da ya birge shi ne shigo da karin magana cikin waƙar wato "garin masoyi ba ya nisa". To ƙarshe da wannan fitowarta kare da gardama domin amsar da Zainab ta ba wa saurayin nata, wato sunan garin su yasa shi cikin tashin hankali da jimami yadda zai gudu. Wato karambanin Akuya . . . . .  Ga yadda ta kaya; 

Liyaliya: to! faɗamin garin in dire ba ya tambaye ni in zayyana, wa za ya auri mata a nan wanda sai an yi sati guda.

Zainab: to! ni garin mu Sambisa ne ka shirya muje a ɗaura can.

Liyaliya: Allah ya kai ki lafiya 'yar garin ni kamba za ni Sambisa ba.

Turƙashi, to ka ji mutumin da yake barazana cewa, ko da ramo ne garin su budurwar tasa a shirye yake a je a ɗaura auren an ba ma Ghana ba, amma daga jin an ce Sambisa nan ya yanke jiki ya faɗi, ya kuma miƙe ya zura a guje. A fitowar ta biyu, yana cikin gudu ta tare shi tace to ai ita kuma atafau! babu wanda take so sai shi. Nan ya kaɗa baki yace ai yamanta ya faɗa cewa matansa uku, kuma in ya je guta babansa ba zai bar shi ya ƙara auran ba. Sai ta ce ya ƙara da ita ta rufe ƙofar, sai ya ce matsalar gidan haya ne suke babu wuri. Ana cikin haka sai ya tambayeta sunanta, dabararsa ya kubce" sai ta ce:

Zainab: "bilkisu mai gidan zinare, amma ana cemn Asiya".

Liyaliya: "Shubhana kaji ai wai tarko ya shaƙure wuyan mujiya".

Liyaliya garin neman gira, ya nemi ya rasa ido, wato dabararsa ba ta kai ga gaci ba domin so yake ya zulle, amma ta gano sho. Sai ya ce to ai shekarar da maman shi ta yi layya mai kitse, sai anka samu wata mai suna Asiya ta sace kafaɗar Tunkiya, kuma tun daga wannan shekarar maman shi yasa take fushi ba ta son mai suna Asiya. Don haka, ba za ta yarda ya aure mai suna Aisya ba, kuma in ya dage sai ya auri Asiya ba za ta yafe shi ba. Nan da nan sai Zainab ta ce da:

Zainab: A'a ina nufin suna na Mariya.

Liyaliya: ai ni ma ina nufin mariya, 'yan mata ki barni in kina ma Allah ba zan fahimce ki ba.

Zainab: kai da wasa nake ni 'yar Bauchi ce ziyace na zo ni nan ka ji,

Liyaliya: ƙarya kike yi min ja'ira, ba za dai ki kai ni Sambisa ba.

A bin burguwar a nan, yadda ake ta dargar kiki ƙaƙa tsakanin Liya-liya da Zainab, a kan tafiya ɗaurin aurensu Sambisa. Sauyin suna tun daga Bilkisu zuwa Asiya daga nan zuwa Mariya. Babban abin dubawa yadda Zainab ta kaɗa hajin, saurayin cewa wasa take yi ita 'yar Bauchi, ta dai kawo ziyara ne. 

To, koma dai ya zance yake jigon barkwanci ya fito a wasan sosai tare tausayi yadda Liya-liya ya kiɗime da ya ji ance Sambisa za a tafi a ɗaura aurensu da Zainab.Hoton Dakta Ahmad Salihu Bello (Hakkin mallaka, Mujallar ADABI)Tsari: tsari yana daga cikin siffofin da kan kula da su wajen nazarin wasan kwaikwayo. Wato yadda aka tsara fim ɗin tun daga fitowa-fitowa zuwa kashi-kashi tare da rarraba lokacin da kuma tsarin 'yan wasan. An tsara wasan Sambisa zuwa kashi huɗu, kashi na farko yana ɗauke da minti 6: da sakan 34. Sannan akwai 'yan wasa jangwarzo guda biyu wato Liyaliya da Zainab da kuma 'yan rakiyar rawa matasa gudu uku. Kashi na biyu yana ɗauke da minti 4: da sakan 54 da hudu shi ma an tsara da 'yan wasa guda biyu gwaraza da 'yan rakiyar matasa maza guda uku, sannan akwai 'yan amshin shata waɗanda ake kira da (eɗtr) suna zaune daga gefe kamar masu talla da masu sayar da rake a matsayin 'yan karo (backup). Kashi na uku yana ɗauke da minti 5: da sakan 49, kuma kashi ne da aka tsara tafiyar su dajin Sambisa tare da nuna tashar mota da dajin Sambisa da wasu ƙorata na musamman da aka ware domin ɗaukar Liyaliya da ƙarfin cin tuwo zuwa Sambisa. Anga inda Liya-liya ya arce da gudu, kuma aka ƙarafa su ka kama shi, har ita Zainab take neman agajin mutune don Allah a taimake a kamo mata mijinta.

Zainab: jama'a ku taimake ni, don Allah wannan mijina ne in ya gudu ba ya dawo wa, ba shi da ishasshen lafiya.................... shi kuma cikin tsoro da ƙoƙarin gudu sai ya ce:

Liya-liya: wallahi ƙarya take Sambisa za ta kai ni na rantse, wallahi ƙarya take.................. 

Haka kuma kafin kace kwabo, mutane da suke tashar motar nan, suka yi a tare a tare aka kamo shi sai cikin mota. Shi kuma ya kama addo'o'i kamar haka:

Liya-liya: Allahuma ajirni min musibati 
      Ja'ahum munkarun wanakirin 
       fi ƙabari, lakad ja'ahum, lailaha illallah....................

A kashi na huɗu, an nuna cewar an yi aure kuma, har Liya-liya yana jiran zai ƙara aure, wannan kashi an tsara shi bisa minti 3: dda sakan 58. An nuna tsantsan kishi a wannan kaso, domin an ga mijin Zainab, ya ce zai auro wata shirgegiya kuma ta fito fili an ganta. Inda ka yi ta bata kashi tsakaminta da maigidanta. Ga kaɗan daga cikin kalamansu:

Zainab: maigida ai kuwa ya batun aurenka ne,

Liya-liya: au babu fashi kinga ma gobe kayan aure za a kai.

Ganin haka, da jin haka ta tafi ta ɗaura tafasasshen ruwa ta watsa ma maigidan a kai sannan ta ce ita bata son jin batun kishiya domin ɗaga mata hankali yake yi.

Zainab: Maigida ka tuna fa, aure amma muka yi ƙiran sunan kishiya yakan sa min laulayi yanzu ma ji nake cikin mugun yanayi. Ni da a yi min kishita, ga ra a yimin ƙugiya ko in yi kwana arba'in ina yasan rijiya.

A nan an nuna kishin kumallon mata a cikin wasan ƙarara. Inda har ta bishi inda yake taɗi da shirgegiyar amarya da taɓarya a hannunta, ta kafa masa. Ita kuma amaryar shirgegiya ko kishiya ta kama ta tare da angon nata har ta kai a kama ko kowa a buga Zainab da ƙasa, har baki ya kumbura.

A jumlace wasan an tsari shi a bisa minti 19 da sakan 95, kuma kowane ɗan wasa ya taka rawarsa dangane matsayin da yahau a bisa harshensa da komai aiwatarwa.

Shawara

Da dama daga cikin mawaƙan Hausa na wannan ƙarni ba su mayar da hankali wajen gina waƙoƙin da za a iya mayar da su wasa ba. Yawanci sun fi mai da hankali a kan gina waƙoƙin neman kuɗi da jigon yabo da siyasa da kuma na fina-finai. Sannan ko da ma an gida waƙar a wani matani na daban akwai buƙatar a dinga mai da waƙoƙin zuwa yanayi na wasa-waƙe ta yadda za a ci moriyar gangar, wato riba biyu kenan. Waƙa da kuma wasan kwaikwayo musamman na barkwanci. 

Fasilai suna da damar sanya akalar mana'antar wasan kwaikwayo na Hausa ta yadda za su ƙirƙiri sabon salon wasan kwaikwayo domin karkata tunani da hankulan al'ummar Hausa a fagen wasa-waƙe ta yadda za a sake samun ƙarin wata kafa ta nishaɗantar da al'umma da ilimantar da faɗakarwa ta wasa-waƙe.

Kammalawa 

Reactions
Close Menu