Dabon Kano a Gidan Sambo: Ziyarar Sarkin Kano a Hadejia

Daga Badamasi Yusuf Bodmas Abu Hammad 

Dangantaka tsakanin Masarautar Kano da Hadejia dadaddiyar dangantaka ce wadda ta fara tun zamanin Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarkin Hadejia Muhammadu Sambo, zaka yadda da abinda na fada idan ka karanta Littafin Hugh Clapperton wato (Journal of Second Expedition) inda yake cewa...

" 22/feb./1822. I afterwards went by invitation to visit the governor of Hadeja, who was here on his return from Sockatoo, and lived in the house of the wambey."

(Daga hagu) Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero tare da Mai martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Adamu Abubakar Maje


Tarihin Birnin Kano ya nuna cewa Sarkin Kano Usman Dan Dabo shi ya fara baiwa Sarkin Hadejia Buhari mafaka bayan cire shi daga sarauta kafin ya koma Takoko (Shafowa) da zama, sannan wannan Dangantaka ta ci gaba da wanzuwa har zamanin Basasar Kano ta 1894, lokacin da Galadiman Kano Yusufa ya nemi taimakon Sarkin Hadejia Muhammadu da Sarkin Gumel Habu, da Sarkin Jafun Modibbo da su taimake shi ya shiga gidan Dabo. Wannan Dalili ya dan raunata waccan Dangantaka wadda har ta kai ga Zaman Dako a iyakokin Hadejia da Kano, amma daga baya dangantakar ta gyaru zamanin Sarkin Kano Alu.

Zamanin Sarkin Kano Muhammadu Sunusi 1954-1963, ya kawowa Sarkin Hadejia Haruna Ziyara sau da dama wadda har ake kiran Masaukin sa da suna "Gidan Sarkin Kano" yana nan a cikin fadar Hadejia daga Arewa. Haka kuma Sarkin Kano Ado Bayero ya kawowa Sarki Haruna ziyara ba sau daya ba, sannan zamanin Sarkin Hadejia Abubakar Maje ya kawo irin wannan ziyara sau da yawa har zuwa wajejen 1996/97, inda ya zo bayan Sallar Isha'i kuma ya kwana. In ka dauke zuwa bikin Bada Sanda ko zuwa Sutura Sarkin Kano Ado yayi zuwa na musamman sau uku da wayon mu.Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya kawo irin wannan ziyara Hadejia a shekarar 2015/2016, akan hanyar sa ta zuwa Machina sai dai lokacin Sarkin Hadejia yana Kasar Waje.

Ziyarar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ta zo dai dai da lokacin da Sarkin Hadejia Adamu ya cika shekara goma sha takwas (18) a gadon Sarauta 2002-2020, wannan ziyara itace ziyara ta farko da Sarkin Kano Aminu Ado Bayero yayi zuwa Hadejia. Muna Addu'ah da fatan Alkairi Allah ya bada ladan ziyara. 

Daga wakilinmu na jihar Jigawa, Badamasi Yusuf Bodmas Abu Hammad

Reactions
Close Menu