Jarumin Telugu, Jayaprakash Reddy ya mutu sanadiyyar bugun zuciya

 Jarumin wanda mazaunin Allagadda ne ya mutu ne a sakamakon bugawar zuciya kamar yadda jaridun kasar India din suka wallafa. Ya bar duniya yana da shekaru 74.


Jayaprakash Reddy

A ranar talatar makon da ya gabata aka wayi gari da sanarwar rashin Jayaprakash Reddy wanda ya kasance shahararren jarumin fim ne dake taka rawa a matsayin dan wasan barkwanci a masana'antar fim ta Tollywood dake kudancin kasar India.


Jarumin wanda mazaunin Allagadda ne ya mutu ne a sakamakon bugawar zuciya kamar yadda jaridun kasar India din suka wallafa. Ya bar duniya yana da shekaru 74.


Jarumi Sudheer Babu na daga cikin jaruman farko-farko da suka fara bada sanarwar mutuwar marigayin ta hanyar dorawa a shafinsa na Tweeter, "Na farka da samun labarin da ya matukar girgizani. Fatan salama a gareka maigida". in ji jarumin.

Jarumi Jayaprakash Reddy


Ofishin gwamnatin Babban minista na Andhra Pradesh (CMO) ita ma ta fitar da sakon ta'aziyyarta kan mutuwar jarumin. Hakanan shugaban kungiyar nan da ake kira da suna Telugu Desam Party (TDP), wato N Chandrababu Naidu shi ma ya bada na shi sakon ta'aziyyar a madadin 'yan kungiyar bisa wannan rashi na babban jarumi.


Reactions
Close Menu