Mariya: Sabuwar Wakar Musaddam

 


Yau nai damarar fadar gaskiya,

Shi yasa na nufo ki ya Mariya

Ko za ki daken da bulaliya,

Sai na fadi me yake zuciya.Batun so ne dake jijiya,

Ba ma fa jini ba dai kin jiya,

Da a zuciya dukka yai mamaya,

Ma'ana dai sonki ya Mariya.Mata dukka dai kamar mujiya,

Nake kallon su sai ke daya,

Na ji tamkar an sakan kugiya,

Kaunarki ta cakumen zuciya.Na fada miki tun watannin jiya,

Mai kyau tamka yake gimbiya,

Ba a yi ta ba sam a Najeriya,

Kai ko da can kasar Indiya.A zamanmu idan ki kai juriya,

Kika zauna ba batun zamiya,

Zan kaiki har kasar Saudiyya,

Daga ranar kin zamo Hajjiya.


Rubutawa: Musaddam Idriss Musa

Reactions
Close Menu