Nazari kan shirin Gidan Badamasi na tashar Arewa24

Tare da Auwal G. Danborno


Fim din Hausa wani abu ne da tarihin rayuwata ba zai cika ba sai an sanyo shi.

Bayan kasancewa ta marubuci, na kasance dan wasan Hausa na dabe. Wannan ta sanya a duk lokacin da nake kallon fim din Hausa, ina kallonsa da fuska biyu.

Fuskar farko a matsayina na marubuci. Ina kallon yadda marubucin fim din ke kulla zaren labari da yadda yake hawa da sauka. Fuska ta biyu kuma yadda 'yan wasan ke taka rawa a fim din.

Shekaru da dama da suka shude tun ina kallo ina uzuri, har ya zama na fara kiran marubutan ina korafi, daga karshe dai na hakura da kallon fim kwata-kwata.

Salon Gidan Badamasi

Shi ne wasan Hausar da ya dawo da ruhina daga dogon suman da ya yi.

Gidan Badamasi labari ne na wani Alhajin Birni da ya yi yawon duniya, wanda cire hula ya fi masa wahala a kan sauya mata.

Ko da yake a gwanancewa da kwarewa ta marubucin bai hasko yawan aure auren da ya yi ba, amma yawan yaransa da kuma dan furucin da 'yan wasan kan furta shi ya nuna yawan auri sakin da ya yi duk da ba a fadi adadi ba.

Alhaji Badamasi ya tara kudin da har yanzu a zaren tafiyar labarin ba a san adadinsu ba.

Sannan ya tara yara marasa tarbiyyar da fatansu da burinsu shi ne ya rasu domin su mallaki dukiyar da ya tara.

Shirin kunshe yake da kwararru kuma gogaggun 'yan wasan da suka hada da

Nura Dandolo, Magaji Mijinyawa, Hadiza Gabon Mustapha Naburaska, Sani DanGwari, Umma Shehu, Falalu A. Dorayi, Hadiza Kabara, Tijjani Asase da sauran su.

Tarbiyyar da ba su samu ba ya sa suka shiga kulle-kullen yadda za su sami dukiyar mahaifinsu ta kowace hanya.

Babu jin kai irin wanda ake samu tsakanin 'Da da Mahaifi ko tausayawar da Soyayya da ake samu Tsakanin Mahaifi da 'Da.

Ana tsaka da kulle-kullen yadda za a sami dukiyar Alhaji sai ga wata sabuwar fuska ta Ado Gwanja wanda ya fito da sunan ''Na Allah'' ta bayyana.

Ƙarin wasu maƙalolin daga baƙinmu na mako na baya da za ku so ku karantaNa Allah ya fito ne a matsayin Dan sanda wanda ya juya akalar shirin da sabon salon kama karya irin na wasu gurbatattun 'yan sanda.

Bayan ma su kallo sun tafi a kan tunanin an sami wanda zai kawo cikas wajen neman yadda za a sami dukiya, sai marubucin ya kara dawo da mu karatun baya.

Na Allah shi ma ya bi sahun 'yan uwansa wajen hada kai da su a neman dukiyar.

Wani abu da yanzu muka zuba ido wanda ke neman jefa mu wasuwasi shi ne yadda aka fara sansano cewa Na Allah ba Dan sandan Gaskiya ba ne.

Tambayoyin da ke zukatanmu yanzu wadanda marubucin ne kadai ya san yadda zai warware su shi ne yadda Na Allah ya sami bindiga ta 'yan sanda a matsayinsa na dan sandan gona.

Bayyanar Na Allah ta kara armasa shirin ta yadda marubucin ya sami damar kara jan zaren labarin da kuma sauya akalar tafiyar, maimakon a baya ana abu guda na neman dukiyar kawai.

Abubuwan da ya dinga aikatawa kuma wani nuni ne cikin nishadi da hannunka mai sanda kan irin yadda gurbatattun 'yan sanda ke amfani da dama da kuma khaki wajen aikata wani abu wanda bai dace ba a cikin al.'umma.

Ko ba komai hakan zai zama wani haske ga masu biye da shirin.

Akwai ilimintarwa bayan nishadi

Auwal G. Darborno


Da dama suna kallon shirin Gidan Badamasi a matsayin shiri na nishadantarwa, amma ga dukkan mai hange da nazari ya san fim din kunshe yake da ilimantarwa da fadakarwa da nusarwa bisa mummunar rayuwar rashin zabarwa 'ya'ya uwa tagari da kuma illar rashin tarbiyyantar da 'ya'yan.

Duk wanda ya ga tarkacen 'ya'yan Alhaji Badamasi zai tabbatar ba wanda ya sami karatu a cikin su, karatun arabi da boko.

Ban da illar yawan aure-auren mataye marasa tarbiyya da kuma illar rashin yi wa 'ya'ya Tarbiyya da ilmi, Marubucin ya nuna yadda illar Maqe kudi da rashin amfani da su ta hanyar da ta dace.

Ga dai kudi sun samu amma kasancewar Alhaji bai tarbiyyantar da 'ya'yansa ba, kudaden na neman zamar masa tashin hankali da rashin tabbas.

Shirin ya yi tasiri kwarai da gaske a cikin al.'umma ta yadda hatta sunayen 'yan wasan na cikin shirin, mutanen gari sun fara amfani da shi wajen habaici da shagube ga masu irin wadannan halaye.

Yadda ake yin shirin cikin mutunci da tsari da barkwanci, ya kama zukatan yara da magidanta.

A 'yan shekarun nan babu wani shiri da ya tasirantu cikin jama'a wanda duk wajen da ka shiga maganarsa ake kamar Gidan Badamasi.

Na yaba kwarai ga marubucin da yadda yake tafiyar da zaren labarin cikin salon jan hankalin mai kallo da kwarewa.

Zaren labarin na tafiya sambal ba tare da gundura ko ginsa ba.

Matsalolin fina-finan Hausa

Zan yi amfani da wannan dama na sosa wajen da ke min kaikayi.

Daya daga cikin abinda ya fara ba fim na Hausa matsala shi ne rashin girmama rubutu daga marubutan fim.

Wannan ta sa aka dinga samun fina-finai da suka zama marasa kan gado.

Marubuci zai tsara labari cikin baiwa da kwarewar da Allah ya ba shi, amma sai mai shiryawa ko darakta ya cire abinda ya ga dama a duk lokacin da ya so da sunan wai ba shi kasuwar ke so ba.

Marubuta ya dace su juya akalar masu kallo ba da baiwarsu, ba wai kasuwa ko mai shirya fim ya juya marubuci daga baiwar da Allah ya yi masa ba. Shirye-shiryen da Arewa 24 ke yi na wasan Hausa ya shiga zukata kuma ya tasirantu a cikin al'umma saboda girmama fasahar marubuci da dama da ake ba marubuta su juya alkalumansu bisa baiwar da Allah ya yi masu.

Fatana ga Nazir Adam Salihi a cikin shirin Gidan Badamasi Allah ya ba shi ikon ci gaba da sakar zaren labarin cikin salon nishadantarwa da fadakarwa.

Auwal G. Danborno Kano, Marubuci ne kuma manazarcin Al'amuran yau da kullum.


Reactions
Close Menu