Ko kun san tarihin jaruma Roshni Patel ta fim ɗin Jamai Raja?

Hoton jaruma Nia Sharma, wato Roshni a fim ɗin Jamai Raja


Nia Sharma jarumar wasan kwaikwayo ce 'yar asalin kasar Indiya. Fannin da ta fi taka rawa shi ne bangaren fina-finan kafar talabijin da ake haskawa ta hanyar tauraron dan Adam. An haifi Nia Sharma ne a birnin Delhi ranar 17 ga watan Satumban alif dubu daya da dari tara da casa'in (1990), wato tana da shekaru 27 a halin yanzu.
Hakikanin sunanta shi ne Neha Sharma, ta sauya sunan zuwa Nia ne bisa dalilinta na cewa suna "Neha" ya zama gama gari tare da yawaita sosai a tsakanin mutane.
Nia ta fito a jerin fina-finai masu dogon zango da ake nunawa a kafar talabijin da suka hada da shirin Ek Hazaaron Mein Meri Behna Hai da shirin Jamai Raja wanda ake nunawa a tashar Hausa na Arewa24 inda ta fito a matsayin "Roshni" da kuma shirin Khatron Ke Khiladi a ahekarar 2017.

Nia tayi karatunta zuwa matakin digiri inda ta karanci aikin jarida kuma burinta ya kasance aiko a kafafen watsa labarai kafin daga bisani ta tsinci kanta a masana'antar fina-finai inda kuma ta samu karbuwa sosai. 
Ba a san wane ne mahaifin Nia ba amma sunan mahaifiyarta shi ne Usha Sharma.

A tsawon lokacin da ta shafe tana fitowa a fina-finai, Nia ta samu nasarori da kuma lambar yabo da dama kana kuma ta samu kambu daga kamfanonin jaridu da na mujallu da dama.

Nia ta zo a matsayi na uku cikin jerin mata 40 da mujallar Birtaniya ta wallafa inda ta kira su da "zafafan mata na lardin Asiya" saboda kwarewarta wajen iya shiga mai jan hankali.

Nau'ikan abincin da Nia tafi so sun hada da Hakka Noodles, Rajma Chawal da kuma Sitaphal Ice-cream. Yayin da kalar da ta fi so kuma ita ce jan launi. Infini mall dake garin Mumbai nan ne inda Nia tafi son zuwa don yin sayayya. Guraren da ta fi jin dadin zuwa kuma su ne kasar Brazil da kuma Miami.

Fassara daga jaridar Bollywoodhungama.


Reactions
Close Menu